*SHU'UMAR MASARAUTA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye.
SHAFI NA BIYAR
Cikin mugun yanayin ta kafe shi da ƙwalaƙwalan idanuwanta masu razana duk wanda ya yi tozali da ita, a hankali Sarki Abdul'aziz ya fara ja da baya jikinsa na karkarwa. Bai yi tsammani ba ya ji bayansa ya bugu da bangon ɗakin, cikin tsinkewar zuciya yake sauke ajiyar zuwa. Da wata irin sanɗa ta taso daga kan gadon tana durfafo wurin da yake tsaye, ganin tana gabda cin masa ya sa ya fice da sauri daga cikin ɗakin ya ƙarasa wurin dogaran da ke tsaron sashensa. Yanayinsa kaɗai ne ya tabbatar musu da tabbas Takawa yana cikin damuwa, tun bai ƙarasa wurinsu ba suka zube cikin girmamawa. "Allah ya taimake ka ya ƙara lafiya da nisan kwana, ɗawisu sarkin ado mai taƙama da ikon Allah..."
"Ya aka yi kuka bar waccan hallitar ta shiga har cikin turakata?" Mai martaba ya katse su fuska a tamke babu ɗigon fara'a.
"Tuba muke ranka shi daɗe, Allah ya huci zuciyar amale a gafarce mu wannan ne na farko na ƙarshe." A daidai lokacin Jakadiya ta ƙarasa ita da Baiwa Saro hannunsu ɗauke da kayan lambun da ake kai wa Sarki Abdul'aziz kamar wannan lokacin. Dogaran ta gani sun nufi turakar Takawa kafin su ƙarasa su ka ga wata baƙar mage ta fito daga cikin turakar idanuwanta jawur kamar gauta tana bin mutanen wurin da wani irin kallo. A zabure Jakadiya ta furta. "Ka gafarce ni uban gidana ka yi mini afuwa, amma ba ni da masaniya game da sakacin Dogaran ƙofa da har suka bar kyanwar nan ta shiga cikin turakarka." Jakadiya ta yi maganar jikinta na karkarwa don ta san a duniya babu abin da Takawa ya fi tsoro sama da mage, wannan ɓoyayyan sirri ne da ba kowa ne ya sani ba saboda gudun kada magauta su fahimci lagonsa. Ita ma Jakadiya abin da ya sa ta sani tun wani lokacin da ta taɓa shiga sashen Mai babban ɗaki (Mahaifiyar Takawa.) wata mage ta shiga har suma ya yi a wurin, kuma ko da ta ga haka sai da Mai babban ɗaki ta tsawatar mata a kan wannan sirrin.
"A kiyaye gaba, ba na buƙatar sake ganin kowacce hallita a sashena." Gabaɗaya suka amsa masa cikin girmamawa. Jakadiya da kanta ta shiga ta jera kayan lambun kamar kullin sannan suka fice bayan ta tambayi Takawa ko akwai wani abin da yake da buƙata, ya ba ta amsa fuska babu walwala. Har bayan wani lokaci Sarki Abdul'aziz bai saki jikinsa ba, ganin bai sake jin motsin komai ba ya sa ya ɗan saki jikinsa.
Cike da ƙwarin gwiwa Fulani Umaima ta ƙarasa cikin turakar Mai martaba, ganinsa zaune a gefen gado kusa da baiwa Maimuna ya sa ta zaro idanu cikin fargaba har sai da ya fahimci ruɗewar da take ciki.
"Lafiyarki Umaima?" Cikin kissa ta daidaita nutsuwarta ta ce, "Dama na yi mamaki ne ganinka shiru, kar dai ka jima kana jirana." Murmushi ya sakar mata haɗe da girgiza kai. Ta ƙarasa wurinsa asirtaccan ƙamshinta ya ratse hancinsa, ya lumshe ido cike da jin daɗin ƙamshinta.
"Ki tabbata kin sa shi ya shiga bayan gida kafin ki saka wa Maimuna turare a gabanta."
Kalaman Boka Bamaguje ya dawo mata raɗau a cikin kunnuwanta. Miƙe wa ta yi ta furta. "Sarkina bari na haɗa mana ruwa mu ɗan watsa ko?" Ba ta jira cewarsa ba ta nufi banɗaki ta haɗa komai da kanta sannan ta zuba turaren da Bamaguje ya bata, bayan dawowarta ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa sannan suka wuce banɗaki. Da kanta ta ɗebi ruwan ta watsa masa cikin sigar tsokana, sai kuma ta yi farat ta furta. "Na yi mantuwa."Kallon da ya yi mata ne ya alamta mata yana buƙatar ƙarin bayani daga gare ta.
"Ina zuwa." Kawai ta furta ta fice a gaggauce. Sai da ta tabbatar da ta rufe ƙofar ta baya sannan ta koma turakarsa cikin sauri ta ɗaga doguwar rigar Maimuna ta kwara mata turaren a ƙasanta sannan ta shafa mata a fuskarta, ita ma ta murtsuke jikinta da shi ta rage kayan jikinta ta sake komawa cikin banɗakin. Tana shiga ƙamshinta ya daki hancinsa, take ya ji wani irin yanayi ya tsarga masa. Buƙatar ya kusance ta ta yunƙuro masa, ganin saƙwannin da yake aika mata ya tabbatar mata da haƙonta zai cim ma ruwa, don haka ta fara neman shawarar da za ta yanke wa kanta. A hankali ta yakice shi tana faɗin, "Sarkina a banɗaki muke mu ƙarasa turaka." Bai musa mata ba, ta ƙarasa sheƙa musu ragowar ruwan sannan suka fito hannunta na riƙe da shi, idanuwansa a rufe suka ƙarasa don haka ko da ta zaunar da shi a gefen gado ta ga ya rarumo Baiwa Maimuna da ke zaune kamar gawa. Fulani Umaima ta koma gefe ta zuba masa ido zuciyarta ƙal, tana nan tsaye Takawa ya gama mu'amalarsa da Maimuna ya koma gefe ɗaya sai gani ta yi numfashinsa ya ɗauke. Da sauri ta ƙarasa ta ɗebi najasar jikinsu ta isa bakin rijiyar da tun da take shiga cikin turakar ba ta taɓa taka wurin ba, wata irin kuɗa ta fara ji a cikin kunnuwanta ga wata 'yar juwa-juwa da take ji sama-sama. A haka ta samu ta zuba najasar a kan rijiyar take murfinta ya buɗe, wata baƙar ƙura ta turnuƙe ta. Sai daga baya komai ya washe, ganin haka ya sa Fulani Umaima ta koma ta janyo hannun Baiwa Maimuna sai da suka je bakin rijiyar Fulani Umaima ta furta.
YOU ARE READING
SHU'UMAR MASARAUTAR 1
Historical Fiction"Na sadaukar maka da kishiyata a wannan daren, shi ne tukwicin da zan iya yi maka." Ba ta jira cewarsa ba ta ɗora rigar a jikinta. Bamaguje ya gyaɗa mata sannan ya furta. "Za ku iya tafiya." Umaima ta yi masa jinjina da hannu sannan ta sake ɗiban ru...