TALLA 💃

239 1 0
                                    

SHIN KINA MURADIN LABARIN ZALLAR BARKWANCI? MAZA KI HANZARTA NEMAN LITTAFIN UWANI YAR ƘARSHIN GWIWA. SALON LABARIN WOLLAH DABAN YAKE 💃💃

    GA ƊANDANONSA KADA KI BARI A YI BABU KE. 😎

*UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*

            ©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

 
  SHAFI NA ƊAYA

   Cikin karayar zuciya da ɗacin rai wasu tagwayen hawaye  suka fara 'yar tsere a saman dakalin fuskar Baba Isuhu, ya kai kallonsa wurin mai sunan malam da ke wutsul-wutsul a hannun Lami ya ce. "Mai sunan malam ba zan iya rabuwa da kai ba, don Allah Lami kada ki azabtar da ruhina da rashinku." Kuka ya sake ƙwace wa baba Isuhu da ya sauke idanunsa a kan ƙullin kayan Lami da ke ɗaure a ɗankwali.

  Sai da ya sharce majina da gefen rigarsa sannan ya sake kwantar da murya yana faɗin.
"Lami kin san irin so da ƙaunar da nake yi miki? Ko so kike ki mayar da ni marayan ƙarfi da yaji? Matuƙar za ki tafi gidanku sai dai ki tafi da ni Lami, domin ni na fi maye maita indai a kanki ne." Baba Isuhu ya janyo hannun Lami ya haɗa da na mai sunan malam ya rungume a ƙirji sai ya sake ɓarkewa da kuka.

"Don Allah ki haƙura da yajin nan da za ki yi Lami. Matuƙar naman ƙauri ne zai datse igiyoyin so da ƙaunar da ke tsakaninmu ko sayar da kaina zan yi, amma na yi miki alƙawari duk inda zan shiga zan yi koma me ye na nemo miki abin ƙaurin nan Lami."

Lami ta taɓe ba ki sannan ta ce.

"Wallahi Isuhu ba abin da zai hana ni tafiya a daren nan, don in gaya maka na ce wa Goggo Sala ko awa guda ba za mu ƙara a gidan nan ba. Saboda Allah kamar a kaina tsiya ta ƙare, haihuwar fari a ce yau kwana biyu cir babu kajin ƙauri ballantana na saka rai da ɗan akuya ko tinkiya. Kai tir da halinka Isuhu, wallahi da Isa mai tsire na aure na san nama har sai na ci na ture..." Cikin sauri Baba Isuhu ya katse ta.

"Me aka yi aka yi Isa ne Lami? Wai ko kin manta Isuhun Lamisuwa mai hadarin naira?" Lami ta sake taɓe baki ta furta. "Ai a banza man kare, tun da a haihuwar ɗanka na fari guda a ce abin ƙauri ya gagara, kenan haka zan zauna har hakikar sunan ita ma ta gagare ni. Wallahi ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa."

  Jin haka ya sake tsuma Baba Isuhu ya zabure haɗe da ɗaga hannu sama ya ce. "Sai ni isuhullen Lamisuwa mai hadarin nairori, sai ni Isuhun da ya sha gaban zaratan mazaje ya samu Lamisuwa." Lami ta ɗan saki murmushi sannan ya kalle ta ya ce.

"Wai ina Lami take?" Da sauri Lami ta amsa. "Ga ni mana."

  "A yau ba sai gobe ba zan kayar miki da tinkiya." Sai da ya kalli hagu da dama ya yi ƙasa da murya sannan ya matsa saitin kunnenta ya ce. "Kin san Allah yau uwar garke zan girke miki." Da sauri Lami ta washe baki cikin zumuɗi ta furta. "Uwar garke fa..."

"Ki yi ƙasa da murya mana haba Lami, ko so kike asirina ya tonu?" Baba Isuhu ya katse ta da sauri.

"Ɗan Isuhullena ai sai yanzu na fahimce ka, Allah Ya ba ka sa'a kada hatsabibiyar yarinyar nan ta ganka lokacin da za ka ɗauke mata uwar garken nan." Lami ta yi maganar murya can ƙasa zuciyarta fes.

"Ai maso abin ka ya fi ka dabara Lamisuwata, dare zan bi na san yadda zan yi da ita. Ke dai kawai ki zuba wannan ki sha kallo." Baba Isuhu da Lami suka kwashe da dariya.

"Lami! Ke Lami ki fito mu wuce kin shanya ni ke 'yar daɗi miji, kin san dai idan ana jego ko kyakkyawan zama a wurin miji ba a yi ballantama wannan mijin na ki..." Lami ta yi saurin katse Goggo Sala, "Goggo zo mu je ciki ai tuni mun riga da mun gyaro ta ni da shi." Baki sake Goggo Sala ta bi ta da kallo sannan ta ce. "Hmmm namiji kenan! Ke yanzu daɗin bakin namiji har zai sa ki zauna..." Lami ta yi saurin yi wa Goggo Sala raɗa a kunne, da sauri Goggo Sala ta washe ba ki ta furta.

SHU'UMAR MASARAUTAR 1Where stories live. Discover now