*SHU'UMAR MASARAUTA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye.
*Masu ƙorafe-ƙorafe ta pc da groups zan rage 100 daga yau zuwa ranar da zan gama free pages. Free pages za su ƙare a page a 10 daga yanzu zuwa ranar duk mai son karanta littafin za ta turo 400*
SHAFI NA TARA
Ayarin dakarun masarautar da ke tafe da su Baffajo tafe suke cikin gajiya sakamakon doguwar tafiyar da suka yi, a farfajiyar wata bishiya suka yada zango suna hutawa sai bayan sun huta sannan suka ci gaba da tafiya, cikin zuciyarsu kowa da abin da yake ayyanawa. Ganin magriba ta fara dosowa ya sa suka yanke shawarar kwana a cikin dajin washegari da asuba sai su ɗora daga inda suke tsaya.
Ƙauyen Gangare
Ganin yanayin da Umaru ya koma gida da shi ya sa Mai gado shan jinin jikinta.
"Mai gida ya kuka yi da Mai gari na ganka duk a sanyaye." Ƙasa ya yi da murya ya furta. "Ina yarinyar nan take? Zan kai ta gidan Mai gari" Kallon rashin yarda ta bi shi da shi ta sake gyara goyon Jawahir da ke bayanta. "Me za ta yi a gidan."
Kamar zai yi kuka Umaru ya ce, "Malam Malmo Mai gado ban san ya za mu yi ba, sun buƙaci na mallaka wa Mai gari ita." Rass! Ta ji gabanta ya faɗi, sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta yi ƙasa da murya. "Ba zan iya rabuwa da Jawahir ba Mai gida, na san Malam Malmo sarai ba zai wuce tsubace-tsubbace zai yi da ita ba." Umaru ya waiga kamar wanda ake kallo duk a tsorace ya ce. "Ya zamu yi yanzu? Mene ne mafita?"
Masarautar Huddam
Wuni guda haka Fulani Umaima ta yi shi cikin rashin ƙwarin jiki, ba ta san dalili ba amma haka kawai za ta ji gabanta na faɗuwa. Har ta so dannewa ta ji zuciyarta na azalzala ba za ta iya jure rashin zuwa wurin Bamaguje ba.
Tsufansa ya sake fitowa sosai don jiki da hannuwansa har karkarwa suke yi.
"Ta zo duniya da ƙarfin iko, shi kuma yana gab da dawowa gidansu na gado."
Bamaguje ya furta bayan ya gama sauraron ƙorafin Fulani Umaima. Ta ɗago a hargitse bakinta na rawa, ƙirjinta na dakan lugude. "Su waye? Kuma daga ina suke."
"Garaje ga dami, daɗina da ke gaggawa Umaima. Na ɗauka za ki tambayi alaƙar shi da masarauta da ita kanta yarinyar." Ajiyar zuciya ta sauke. "Tamkar tagwaye haka suka kasance tsakaninta da Hidaya, sai dai waccan ruwan sanyi ce salam a kan wannan. Ban san a wanne muhalli zan tirke ta ba, abu ɗaya na sani ita ta kasance daga cikin wata irin zuri'a masu matuƙar hatsarin gaske. Na ga takobi a cikin jininta sannan wuta na gewaye sashenta, takaicina ɗaya Mahaifiyarta ta riga da ta binne duk wani al'amari da sirrin da ke ƙunshe a cikin rayuwarta. Daga ni har sauran matsafan duniya duk wani bincike da za mu yi ba za mu tantance takamaiman ainihin tushenta ba. Sai dai kuskure guda mahaifiyarta ta tafka wanda da shi kaɗai za mu iya cin galaba a kan wannan yarinyar."Cike da zumuɗi Fulani Umaima ta furta. "Mene ne shi? Duk wuya duk tsaninsa zan nemo shi..."
"Bincike ya bayyana mini tana da matuƙar tasiri a rayuwarsa. Ina nufin jaririn da kika sa Maimuna ta fitar da shi shekara goma sha ɗaya baya, shi yake gab da shigowa gidan sarautarku. Sai dai kuma ita da shi za su kasance tamkar wuta da ruwa a fannin gaba, kowannensu ba zai ƙaunaci ɗan'uwansa ba. Shigarsa tamkar dasa nakiyar da ke tashin zamani da alƙaryarki ne, ba tun yau ba; na gaya miki shi ba kamar ɗan uwansa ba ne. Ruhinsa ɗauke yake da zaratan dakarun da ke sarrafa zuciya da tunaninsa, tun ranar haihuwarsa na fahimci zanen ƙaddararsa ya wanzu dalilin da ya sa na baki shawarar matse kunamar nan a cikin bakinsa, ashe tagwaye ne halwar tsafina ya gagara nuna mini. Tun yana jariri ya sauka a fadar Sarkin fararen aljanun doron ƙasa, da ke tsakiyar dajin Wuruju a daidai wurin da Baiwa Maimuna ta dire shi. Sun naɗa masa kambun da babu mai iya sauke shi sai mutum ɗaya wato wannan yarinyar." Bamaguje ya ƙarasa maganar yana haska wa Fulani Umaima inuwar wata yarinyar. Ta tsinci muryarsa ya ci gaba da faɗin.
YOU ARE READING
SHU'UMAR MASARAUTAR 1
Historical Fiction"Na sadaukar maka da kishiyata a wannan daren, shi ne tukwicin da zan iya yi maka." Ba ta jira cewarsa ba ta ɗora rigar a jikinta. Bamaguje ya gyaɗa mata sannan ya furta. "Za ku iya tafiya." Umaima ta yi masa jinjina da hannu sannan ta sake ɗiban ru...