*HUNAYDAH*
*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's friend)*_
_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_
_____________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com*BIMISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*
*Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah subhanahu wa ta'ala wanda ya bani ikon fara rubuta wannan littafin, ina rokon Allah yasa na kammala lafiya, ya kuma bani ikon rubuta abinda zamu amfana dashi baki ɗaya (Ameen.)*
*Page 1*
Motoci ne keta shawagi a gaban makarantar Delight Academy sakamakon tashi yara da aka yi, yayin da yara da mallamai suke fitowa daga cikin makarantar.
Tafe suke suna hira da sauran mallamai 'yan uwanta a daidai lokacin da yara suka rage ɗaiɗaiku a haraban makarantar domin ka'idar ce ta makarantar idan har kana malamin aji sai ka jira yaran ajinka sun gama tafiya kafin ka bar ajin, fitowarsu gate ɗin makarantar keda wuya ta hango wata ɗalibanta zaune a baki kwalbatin dake gaban makarantan, sallama tayi da sauran mallamai ta nufota
"Fadwah me kike a nan, why are you outside?""I'm waiting for my mom"
"C'mon maza taso daga wurin, baki ga drainage bane a wuri ba, kuma ai nace ki riƙa jiranta a cikin school" ta ce tana miƙa mata hannu.
Tashi Fadwah ta yi ta dawo gefen Auntynta. Lambar mahaifiyar Fadwah auntyn ta fara kira amma ta kira kusan sau uku amma ba'a ɗaga ba, gashi kuma bazata iya barin Fadwah a makarantar ita ɗaya ba, can dai ta kira mai daidaita-sahun ta yazo ya ɗaukesu, da yake yarinyar akwai yawo ita ta riƙa nuna masu hanyar har aka iso anguwarsu wanda estate ne, daidai kofar gidansu cab man ɗin ya sauke su sai dai gidan a rufe yake, hakan yasa ta ce yayi tafiyarsa kar ta ɓata masa lokaci.
"Ya Allah! Yanzu ya zan yi" Auntyn Fadwah ta faɗa cikin ranta. Nan dai suka tsaya a gaban gidan tana tunanin mafita, daidai nan wani mai mota yazo wucewa ya tsaya ganin Fadwah tsaye.
"Hi Fadwah"
"Hey Uncle Nas"
"Kuna jiran wani ne?" ya ce yana kallon wacce suke tare.
"Emm! Dama daga makaranta ne, Ni malamar ajinsu ce, an tashi ne daga makaranta kuma babu wanda yazo ɗaukar ta kuma na kira Mum ɗinta bata ɗaga ba, shine na ce bari na kawo ta gida sai dai gashi mun iso kuma gidan a rufe."
"Oh! So sorry, bari nayi parking sai na buɗe nawa gidan in yaso sai ta jira mamanta a nan" bai jira amsarta ba yaja motarsa zuwa parking lot ɗin shi yayi parking sannan ya fito daga motar "muje ko" rufa masa baya suka yi ya buɗe gidan, tsaye tayi taƙi tafiya ganin gidan babu kowa kuma bawai ta san shi bane balle har ta barshi da 'yar mutane, ganin ta tsaya tana tunani ya ce " da wani matsala ne?"
Murmushi ta yi sannan ta ce " Idan babu damuwa na ce ko zan iya tsayawa da ita?"
"Oh! Why not?. Bismillah ku shigo daga ciki" ya ce yana gaba suna biye dashi, "ga wuri ku zauna, make yourself comfortable and feel at home. Bari na ɗauko maku ruwa."
"No, Ka barshi I'm ok, and u Fadwah, did u need anything?"
Girgirza Kai tayi alamar a'a.
"Ok, Ina zuwa" ya ce sannan ya fita daga gidan, bayan 10mins sai gashi ya dawo, sannu da zama yayi masu bayan ya zauna nan yake sanar dasu wai ashe mahaifiyar Fadwah ta kai kanwanta asibiti babu lafiya. Addu'ar samun sauƙi tai mata daga haka ta cigaba da kallon da take a TV. Wasa-wasa awa kusan uku kenan mumyn Fadwah bata dawo ba gashi har an fara kiraye-kirayen magriba, Fadwah kuwa tuni ta jima da barci, miƙewa Nas dake ɗan taya Auntyn hira yayi, ya ce "bari inje inyi sallah, maybe kafin nan ta dawo. Ga bayi nan idan zaki yi alwala" ɗaki ya shiga ya ɗauko mata sallaya sannan ya tafi zuwa masallaci. Miƙawa ta yi ta ɗoro alwala zuwa wannan lokacin hankalinta duk ya koma gida kuma babu yanda zata bar yarinyar ƙarama tare da wannan baligin mutumi wanda ba muharraminta ba, gashi sai kiranta Ammi ke yi ta dawo gida kafin Abbansu ya shigo gidan ya tadda babu ita, haka dai tazo ta gabatar da Sallah tana mai addu'ar Allah yasa Maman Fadwah ba tsaresu aka yi a asibitin ba. Nas bai shigo gidan ba sai da yayi Isha ya biya wani restaurant ya siyo masu abinci, da sallama ya shigo gidan inda ya sameta zauna bisa sallayar tana addu'a, zama yayi a gefen Fadwah da tashinta barci kenan ya miƙa mata ledar, ba musu ta amsa don yunwa take ji, "Thank you Uncle Nas. Uncle mum bata dawo ba?" Fadwah ta ce tana buɗe ledar abincin.
YOU ARE READING
HUNAYDAH
RandomLabarin ne wanda ya soyayya, cin amana, ƙaddara da tsantsan tausayi ku dai ku biyo ni kuji yadda zata kaya.