*HUNAYDAH*
*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's friend)*_
_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_
_____________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
*Page 5*
*WANENE NAS*
Nasir Sadeeq shine cikakken sunansa. Mahaifinsa Mall. Sadeeq Bello Abubakar manomi ne wanda ya shahara gun noman shinkafa wanda ya gada gun mahaifinsa. Haifaffen garin Patigi ne dake jihar Kwara. Kamar yadda mafi akasarin jama'a garin suka kasance nufawa, shima mall. Sadeeq ya kasance banufe duk dai yakasance ruwa biyu saboda mahaifiyarsa Halima bafulatana ce, wannan ne ya jawo Sadeeq ya tashi cikin tsangwama kasancewar sa ɗan bare a cewarsu. A lokacin Mall. Bello mahaifin Sadeeq nada matar aure uku Fatima da Amina, sai kuma Halima wanda suke da 'ya'ya goma sha ɗaya. Fatima wacce ta kasance uwargida nada shida amma uku ne kawai a raye Haruna, A'isha sai kuma Umar, Suleiman, Maryam da Ruqayyah su kuma Allah yayi masu rasuwa. Yayin da ita kuma Amina wacce ita ce ta biyu tana da 'ya'ya huɗu Zainab, Khadijah, Yusuf sai kuma Hauwa. Sai kuma amarya Halima wacce ke da ɗaya wato Sadeeq wanda keda sunan kakansa. Mall. Bello tsaye yake akan gidansa amma duk iya ƙoƙarin sa na ganin matansa sun haɗa kai abin yaci tura don ware Halima suke yi duk da idan yana gida sukan nuna masa suna zaune lafiya da ita amma yana barin gidan suke fara zuba mata rashin mutunci son ransu. Wannan dalilin yasa Sadeeq ya tashi babu wani shakuwa tsakaninsa da 'yan uwansa, da ya fara girma kuma kullum yana tare da mahaifinsa a gona, idan kuma basu tare toh yana makarantar allon. Sadeeq nada shekara goma sha uku Halima ta bar duniya. Wannan ranan Sadeeq kwana yayi yana kuka don mutuwar ta girgiza shi matuƙa. Kusan haka ne ya kasance a gurin mahaifinsa shima don duk acikin matarsa babu mai girmama shi kamar ta. Suma iyalansa mutuwar Halima ta sosa masu rai don duk wannan cin kashi da suke mata da wuya tayi musayar yawu dasu kuma bata taɓa sanar da mai gidansu ba. Haka yasa Sadeeq ya ɗan samu sassauci daga wurin abokan zaman mahaifiyarsa da kuma 'yan uwan shi. Sosai ya maida hankali gun noma kuma Alhamdulillah don Allah yasa masu albarka sosai a cikinta.
Sadeeq ya taso da kyau, irin na asali fulani don idan ka gansa idan ba faɗa maka aka yi ba zaka taɓa kiransa banufe ba, wannan yasa 'yan matan ƙauyen suka mutu masa. Ko wacce burinta ta samu miji kamar shi ga kuɗi ga kuma kyau, don yanzu shi da mahaifinsa suna da ma'aikata da suke tayasu aiki. Sadeeq nada shekara ashirin da biyar ya auri matarsa Bilkisu wacce ɗiya ce ga abokin mahaifinsa Mall. Nasiru Zubairu wanda a lokacin bata wuce shekara sha shida ba. Babu laifi Bilkisu nada kyau daidai gwargwado. Sadeeq da Bilkisu sun kwashe shekaru kusan shida basu da haihuwa. A cikin wannan shekarun kuwa sau uku tana haihuwa daga wanda basu zuwa da rai sai wanda tana haihuwarsa ya mutu. Sadeeq da Bilkisu suna da shekara goma cif da aure ta haifo ɗan ta santalele, kyakkyawa mai kama sak da mahaifinsa sai dai shi ya ɗauko hasken fatar mahaifiyarsa. Ranar suna yaro yaci sunan Nasir, sunan mahaifin Bilkisu wanda bai jima da rasuwa ba aka haifesa. Nasir wanda suke kira da Abba ya tashi cikin tsantsan gata gun iyayensa har ma da kakanni, daga kasansa kuma haihuwa ya tsayawa Bilkisu. Babu yadda ba'a yi da Sadeeq ya ƙara aure amma yaƙi don tuna irin zaman da mahaifiyarsa tayi tare da abokan zaman ta.
Tunda Nasir ya taso mahaifinsa yake tsaye akan karatunsa don ya kudurta a ransa tunda har shi bai yi ilimin zamani ba, iya kacinsa na addini amma ɗansa kam bazai yi ƙasa a gwiwa ba sai ɗan sa ya samu duka biyun har sai inda ƙarfinsa ta kai.
YOU ARE READING
HUNAYDAH
RandomLabarin ne wanda ya soyayya, cin amana, ƙaddara da tsantsan tausayi ku dai ku biyo ni kuji yadda zata kaya.