1

551 28 11
                                    


A kicin ya sameta tana wanke-wanke, motsin shigowarsa yasa ta juyo. Ta kare masa kallo tana murmushi, shima kallonta yake yana murmushi. Yace

‘Daina motsa baki ki fadi abinda yake ranki.’

Ta kyalkyale da dariya ta cigaba da dauraye kwanon da ta wanke tana fadin

‘A’a! Gani nayi an ce Bichi za a je a gaida Baffa amma kuma naga an dau wanka kamar za aje wajen bazawara.’

‘Au ashe fa ban gaya miki ba akwai wata budurwa ce ma da zan dan abinnan....'

Kafin ya karasa ta katseshi tana dariya

‘Babu abinda zakayi, daga ni sai kai nawan ni kadai.’

‘Idan na dawo nace ki kwashe kayanki daga daki daya ai zaki gane.’

Ta kyalkyale da dariya.
Suna ta zolayar juna suka yi sallama tayi masa a dawo lafiya ya kama hanyar Bichi; inda zai je ya gaida kakanninsa na wajen uba.

Haka suke rayuwarsu cikin walwala da kaunar juna tare da yaransu biyu Abdallah da Farha masu shekaru hudu da kuma biyu.
…….

Wunin na yau baiyi mata dadi ba, gashi su Abdallah da zasu debe mata kewa suna gidan yayan babansu Baba Sani. Babu abinda yake damunta amma dai bata jin walwala, tunda sukayi sallama ya tafi Bichi take fargabar da bata san dalilinta ba. Haka har akayi sallar la’asar.

Tana zaune a falo ta kunna TV tana kallo; duk da hankalinta baya wajen; taji ana buga gate. Ta saka hijabinta ta nufi gate din, tana zuwa ta leka ta gefen gate din ta hango Baba Sani a tsaye rike da mukullin mota. Ta karasa da sauri ta bude gate din ta matsa don ya wuce

‘Sannu da zuwa Yaya, Bismillah.’

Ta fada tana kama hanyar cikin gidan da nufin ya biyota su karasa ciki. Ya ja ya tsaya a bakin gate, ganin haka itama ta juyo ta tsaya tana dubansa. Kafin tace wani abu yace

‘Ai ba ma sai na shiga ba,  Umma ce dama tace na taho dake can gida yanzu.’

Gabanta ya fadi, dama tayi mamaki da ta ga Yaya shi kadai; musamman da yake su Abdallah suna gidansa.

Ta kalleshi ta dafe kirji ta fara Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun a ranta. Fata take Allah ya sa ba wani abu ne ya sami su Abdallah ba don watakila shi yasa gabanta yake faduwa tun safe. Ta kasa magana kallonsa kawai takeyi tana kokarin fassara damuwar dake kan fuskarsa, muryarsa ce ta katseta

‘Rufo gidan kawai ki zo muje, mu ake jira.’

Ya juya ya koma waje don ya jirata.

Da kyar ta ja kafa ta koma cikin gidan zuciyarta na faman bugawa da karfi kuma da gaggawa, dole ta sa hannunta ta dafe kirjinta.

‘Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.’

Ta fada a fili.

Mukullin gidan kawai ta dauko sai wayarta ta jefe a jaka ta fito ta shiga bayan motar Yaya Sani ya ja suka kama hanya ba tare da sunyi magana ba. Fata take Allah ya sa ba yarantane wani abu ya samesu ba don wannan shine karo na farko da suka taba zuwa gidan Baba Sani ba tare da ita ba kuma har aka barsu su kwana.

Suna shanyo kwanar gidan Umma ta hango mutane a tsaye cirko-cirko, ta dafe kirji cikin matsananciyar fargaba; tabbas ta san Abdallah ne ko Farha wani ya mutu; Allah ya sa ma ba su duka ne suka mutu ba.

Tuni hawaye ya wanke mata fuska yayinda ta balle murfin kofar motar ta fito ta nufi cikin gidan da sauri tana ketare mutane.

Babu wanda ya tare ta har ta kai tsakar gidan,  kafin ta karasa kofar falon ta hango Umma a zaune a kan baranda ko shimfida babu. Mata ne a kewaye da Umman, duk da bata da natsuwar da zata tantancesu amma ta san duk kuka sukeyi. Da sauri ta karasa har tana cin tuntube, tan zuwa matan suka dan buda mata ta wuce har gaban Umman. Tana zuwa gaban Umma ta zube, Umma ta goge hawayen dake fuskarta ta kama hannunwanta duka biyun ta matse tana fadin

‘Hakuri zamuyi Aisha, haka Allah yake ikonsa.’

Tuni hawayen Aisha ya kara tsananta, ta kalli Bushra wadda take zaune a gefen Umma tana share hawaye suna hada ido Bushra ta kara rushewa da kuka tana fadin

‘Yaya ya tafi Anti Aisha! Yaya Mustafa ya tafi mutuwa tayi mana yankan kauna.’

Take Aisha ta daskare, hawayenta ya bushe ta bude baki tana zare ido; idan ta kalli Umma sai ta kalli Bushra. Ta bude bakinta cikin in-ina tace

‘Mustafa! Shi ai yana Bichi ko? Na zata Abdallah ne ko Farha, Abbansu ai yana gidan Baffa ko?’

Babu wanda ya amsata sai kukansu da ya kara tsananta. Cikin rawar jiki ta fara kokarin bude jakarta tana fadin

‘Bari na kirashi ai Bichi ya  tafi dazu fa.’

Anti Rakiya kanwar Umman ita ta dafe hannun Aisha wanda take kokawar bude jaka da shi ta kalleta suka hada ido tace

‘Aisha hakuri zakiyi, Allah ya karbi rayuwar Abban Abdallah. Yana daf da shiga garin Bichi yayi hatsari a motar sai gawarsa aka kaiwa su Baffa.’

Ta fasa bude jakar ta bude baki tabi Rakiya da kallo yayinda bugun zuciyarta ya sake karuwa. Cikin rawar murya tace

‘Abban Abdallah ya rasu?’

Ta dafe kirjinta da hannuwanta yayinda numfashi ya fara yi mata nauyi. Bushra ta matso ta dafeta ta dubi Anti Rakiya tace

‘Anti Rakiya duba jakarta ki dauko inhaler dinta, kada asthma dinta ya tashi.’

Nan da nan Rakiya ta zazzage jakar sai dai babu inhaler a ciki, daga waya sai mukullin gida.

‘Babu fa inhaler a nan, babu ma komai a jakar daga waya sai key.’

Bushra ta mike ta dubi ta kusa da ita tace

‘Ku dafeta bari na fita don dole a samo inhaler.’

Tayi waje da sauri tana share hawaye, kafin ta kai farfajiyar gidan wajen rumfar motoci tuni numfashin Aisha ya fara sama. Tana dab da kaiwa gate Abba wanda shine dan autan gidan ya taso ya sha gabanta

‘Ya Bushra ina kuma za kije?’

‘Asthman Anti Aisha ne ya tashi gashi bata taho da magani ba ko inhaler.’

‘Subhanallah!’

Ya fada yana share kwalla, ya dubeta yace

‘Koma yanzu zan kawo in sha Allah. Ventolin ko?’

‘Eh, inhaler ko tabs duk wanda ka samo.’

Ya fice ya barta inda sauran ‘yan uwansu maza dake wajen har sun taso sun kewayeta tana musu bayani.

Ko minti goma Abban baiyi da fita ba ya dawo, ya samesu a tsakar gidan nan a kan baranda Aishan ta jingina da bango tana hawaye tana numfashi da kyar. Kafin ya karasa Anti Rakiya ta mike ta karbi ledar hannunsa, nan da nan ta balle kwalin inhaler din ta mikawa Bushra wadda ke kusa da Aishan. Haka aka dinga fesa mata inhaler din har numfashinta ya dawo dai-dai.

Can wajen karfe shida saura Baffa Tijjani wanda kanin mahaifinsu Mustafa ne ya shigo tsakar gidan ya sanar da su Umma zasu iya zuwa suga gawar Mustafa don an kawota daga Bichi har sunyi masa Sallah da yake a can din an riga an wanke shi anyi masa sutura.

Umma ta mike a hankali, itama Aisha ta mike yayinda su Bushra suka rufa musu baya. Falon baki wanda yake da kofa a bakin gate nan aka shimfeda gawar Mustafa, tsaf an yi masa sutura kuma da yake ba wani ciwo yaji ba fuskarsa tayi fes kamar ka kirawo sunansa ya amsa.

Umma ce ta fara isa kan gawar ta tsuguna, ta bishi da kallo tana fitar da hawaye yayinda Aisha ta zagaya ta daya bangaren ta tsuguna itama tana kallon fuskarsa wadda tayi kama da ta me bacci kuma yana murmushi a lokaci guda.

Umma ta daga hannu sama tayi masa addu’a na tsawon lokaci sannan ta mike cikin sauri ta fita daga falon tana share hawaye.

Aisha ta mika hannu ta shafa fuskarsa, ta bude baki a hankali tace

‘Mustafa.’

Babu amsa. Ta dan kara matsawa kusa tana shafa fuskarsa, kawai sai ta fada jikinsa ta rungumeshi tana rusa kuka. Duk mutanen da suke wajen saida sukayi mata kuka; tabbas mutuwa tayi musu gaggawa.

UWAR SADDIKU Where stories live. Discover now