6

240 22 0
                                    

*TSAKA MAI WUYA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V
+201123302418

Slm ina maiso taga tayi kiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakiyar mace ❤️ina maza da basacin abinci ina maza masuso suyi kiba ina yara da basuda kiba ina mai farin cikin sanar daku *ZUMAR K'IBA*, zumace wadda take saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA*  zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam,hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza..,Ina masu fama da  Ciwan sanyi  duk nacin sanyin ki hajiya kikai amfanin da maganin Mmn khairat saikin warke duk ko iya da d'ewarshi ajikinki..Domin k'arin bayani👉 WhatsApp no 07044450136, 08167453086

*06*

*Zaria*
Samaru_Tsamiya.
8:11am.

A cikin anguwan samaru Layin Tsamiya, Ire iren gidajen su na b'arayin wajen zaku ga akwai d'akuna a waje saboda anguwa ce ta yan makaranta, Makaranta kuma Babba a Africa wato ABU ZARIA.
Ko bayan makaranta akwai y'an kasuwa da masu huldar arziki da neman na kansu, iren iren gidajen wajen duk akwai dakunan a waje domin ba da Haya na maza matasan yan makaranta.
A irin hakane na hango wani gida mai Damdamali a kofar gidan har da Rumfa sai Dakunan waje jere a layi Guda biyar, Daga gefe har da makewayin su na lalura.
Gidan na marasa karfi ne ammh kuma bai lalace sosai ba, yanzu haka kila ma megidan ya rasu dakunan magada ne.
Dakunan duka suna Rufe ne,Sai guda d'aya na farko ne a bud'e har da Labule, Kai tsaye sai ga wani Dogon Saurayi ya fito Sanye da kayan yan Bautar kasa completed, a jikinsa Farar Riga da Green din wando,sai Falmaran din su Green sai Facin cap itama kalan green mai haske.
Kafarsa sanye da Booth din takalminsu mai ruwan goro. Bayansa goye da wata Bakar Jaka karama ta baya.
Dukawa ya yi yana kara tamke igiyan takalminsa duk da yana Duke ne ammh Dole za'a kirasa ingarman Namiji Tunda ya had'a tsawo da Fad'i na Budewar cikakkun maza.
Ya nan nan a duke Wani farin Saurayi ya sake Fitowa daga Dakin shima da irin shigar sak, Daga gani ni masu yi ma kasa Hidima ne ma'ana Corpers.
Kofar Dakin ya Rufe ya saka makullin yana kullewa lokaci d'aya yana fadi'n"Hala yau tafiyar kasa zaka yi?
Ya fad'a daidai Lokacin da ya gama kulle Dakin, Shima yana da jakar baya kalan kayansa wato green. Sai ya kara gyara zamanta a saman kafad'ansa na Hannun Dama Key din kuma sai ya zura a aljihun wandonsa.
Wanda ke duke kuma bai tankasa ba,Illah cigaba da tamke igiyoyin takalminsa da ya yi, na tsayen ya kara kallonsa lokaci d'aya ya duba Bakin agogon Fatan da ke hannunsa cikin Kosawa yace"Mallam mun fa makara. Ka tsaya sai faman tamke igiyoyin takalmi ka ke yi."
Sai a lokacin ya mike yana kara Dage wandonsa sama har ana ganin sawowin kafarsa mai cike da gargasa ga su nan duk sun kwanta. kai tsaye ya kai duban shi kan agogon Silban da ke hannunsa 8:20am na safe kuma ya kamata By now ya isa inda zashi.
Yana shirin mgana wayarsa da ke aljihun wandonsa ta Dauki Vibration alamun ana kiran shi,Hannu ya saka ya ciro wayar yana duba mai kiran duk da yasan Daga gida ne, Tunda itace wayarsa da kowa ya san layin. Babbar waya ta makaranta ce da aiki ba kowa ya san shi da ita ba.
Sunan UMMA da ya gani ne yasa ya yi kasake shi bai dauki wayar ba, shi kuma bai maidata aljihu ba.
Saurayin da ke bayansa ya yi Dage tunda ya fishi tsawo ya leka yana Fad'in"Waye ke kira?
Ko SULTANA ce?
Da sauri ya kauce bayan ya jimke a wayar a hannunsa yana sauke numfashi, Dariya na gefensa ya saka kafin yace"Yarinyar nan na bala'in ji da kai, tana kulawa dakai kai kuma ga shi ban ga kana kula da ita ba"

"Tahir..."

Muryansa cikin Kaushi da asset din Zamfaranci acikinta ta katse Tahir da ke masa Tsiya. Rai ya bata kafin yace'Tahir me? Ba gaskiya na Fad'a ba. Ina fa lura da kai tun satin nan ta ke kiran ka da wayar Umma ba ka Dauka"
Mirmishi ya saki kafin ya juyo suna kallon juna. Fuskarsa Ma'abociyar Haiba da zati ta bayyana, Baki ne mai ruwan kalan haske doguwar Fuska garesa Dauke da Dogon Hanci da idanuwansa matsaikata. Yana da Zagayyen Saje da gemunsa baki Suluf Cikin Yanayin Mganarsa ta cikakkun maza yace"Au ashe? wa ya saka ka aiki a kaina?
Tahir yace"Sai an sakani? Kasan dai tare muke kwana nasan komai da ya Danganceka"
Kai ya jinjina masa kafin yace"Ka sani mana Tunda ka na sakamin Ido"
Ya fad'a yana hararansa Dariya ya yi lokaci d'aya ya Dafa kafad'ansa yana Fad'in"Na gaida Magajin gida"
Wani mugun kallo ya yi masa. Da yasa da Sauri ya Daga Hannunsa sama yana Fadin"Afuwan. SADIQ.. "
Kokarin maida hannunsa ya ke saman kafad'arsa ya yi saurin tureshi ya wuce gaba. Da gudu ya bi bayan shi yana Dariya. Duk da ya so kada Tahir ya yi masa shakiyancin Dafe nan sai da ya Dafa shi suna tafe suna Rangaji kamar wasu yara.
Suna tafe zuwa bakin Titi Tahir ya kallesu ganin Sadiq s ya fisa tsawo shi kansa wajen kafad'arsa ya ke. Yasa ya ce"Tabdijam. Gaskiya ka na da Tsawo kamar wani Samudu"
Kai tsaye Sadiq yace"Shi ne.."
Tahir ya yi shegiyar Dariyan sa da Sadiq ya tsana kafin yace"Kai ma ka sani kenan?
Kallon juna suka yi kafin Sadiq ya jinjina kai yana Fad'in"Ina maka Fatan samun lafiya Tahir yusuf Daura"
Tahir na Danne Dariyansa yace"Ba ni lafiya ne?  Sadiq ya gyada masa kai kafin yace"Eh mana. ai ciwon ka ba shi da mgani saboda Dariya soso min Hauka ne"
Tahir ya dauke Dariyan sa ya na kallon Sadiq shi ko ya sha Mur ko kara kallon su bai yi ba,Tahir ya daga kafa ya bisa ganin ya yi gaba ya barshi sai da ya bari sun jera sannan yace"Nasan mganin ka. Innani zan gayamawa abunda kace a kaina. wato ina Hauka ko Sadiq?
Mirmishi ya saki mai tsada ammh bai yi mgana ba. Tahir ne ya cigaba da zuba mganarsa yana jinsa ammh ba kowacce mgana ya ke bashi amsa ba. Duk da shi ba miskili ba ne ammh mganarsa Ra'ayi ce akwai Lokacin da Ra'ayin hakan baya zuwa masa.
Suna tafe in sun ga gungun matasa Sadiq zai daga musu hannu ya yi musu sallama, in Dattijai ne kuma ya gaishe su da kwana bayan ya yi musu sallama. Tahir ma dolensa ya ke yi Tunda yasan Halin Sadiq suna yin gaba zai fara masa wa'azin yad'a sallama a tsakanin Mutane na tsaye ya gaida na zaune har ya Haddace wannan Mganar.

TSAKA MAI WUYA.!Where stories live. Discover now