*TSAKA MAI WUYA..!*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk
Ku zo ku yi sayayyarku tare da Yar Gidan Imam, inda za ku sami komai cikin sauki, tun daga kan kayan kicin, kayan yara,atamfofi da lesissika uwa uba da kayan gyaran jiki irin na manyan matan da suka San kan su,har counselling mu na yi yadda duk damuwar da ki ke ciki a game da aurenki da gyaran jikinki zaki samu solution. Ku dai ku shigo cikin wannan gidan na karamci kai tsaye domin more tagomashin da ke ciki.
*14*
Tahir ke kiransa ya na Dagawa yaji Muryan Tahir cikin Firgici yana fad'in"Sadiq ka na ina ne? Har daya saura na dare baka dawo ba?
Wlh na zata ka dawo gida barci ne ya kwasheni sai farkawa na yi naga baka dawo ba."
Sadiq ya shafa kansa da Hannunsa guda d'aya kafin yace"Eh ban dawo ba."
Cikin Tashin Hankali a muryan Tahir yace"Sadiq ba ka dawo ba? To ka na ina ne?
Kamar bazai yi mgana ba sai kuma dai yace"Ina asibiti ne."
A firgice Tahir yace"Asibiti? Innalillahi me ya faru da kai?
Tahir ya fad'a gabansa na fad'i saboda Matukar Razana ya razana da rashin Dawowar Sadiq abunda bai taba Faruwa ba ne.
firgicinsa kada wani abu ne ya samu Sadiq din ya shiga Uku.
Sadiq yace"Eh ina asibiti ne nan cikin Samaru."
Tahir yace"Baka da lafiya ne? Sai da ya juya ya kalleta ta na zaune ta had'e kai da gwiwa daga ganinta ta na son mahaifiyar nan nata shiyasa ta ke cikin Damuwa da kuka.
Kafin ya yi ajiyar rai ya ce ma Tahir"ba ni ne ba ni da lafiya ba Tahir."
Tahir cikin kosawa yace"Ka na so ka kasheni da Zullumi ne Sadiq? Waye ba shi da lafiya.?
Sadiq yace"Taimako na yi Tahir. Wata baiwar Allah ce."
Tahir ya jinjina kai kafin yace"Zaka dawo ne?
Shuru Sadiq ya yi Kara kallonta ya yi ita kad'ai ne bai kamata kuma ya tafi ya barta ita kadai ba. Ga ta karamar yarinya ba bu mataimaki a kusa da ita.
Kai Tsaye ya ce"An ya? Ban tunanin haka."
Tahir ya sauke ajiyar zuciya kafin yace"Wani asibiti ne? Sai na zo na same ka."
Sadiq yace"Ka yi zaman ka Tahir lafiyata kalau fa."
Tsaki Tahir ya ja kafin yace"Dilla ka Turomin sunan asibitin gani nan zuwa.."
Daga haka ya kashe wayarsa.
Sadiq ya Sauke wayar daga kunnensa shi kanshi bazai iya fad'an sunan asibitin ba. Sai da ya fita daga Haraban Asibitin ya ga sunan asibitin sannan ya Rubutama Tahir ya tura masa.Dawowa ya yi cikin asibitin ya isketa har ta yi barci ta d'ago kanta saman masagin kujerun da ke wajen domin zaman masu jinya.
Daga gani a wahale take numfashin ma nata a wahale ya ke fita, kauda kansa ya yi ya na kallon gefe. Bayan ya zura duka hannuwansa a aljihun wandonsa yana nazarin wasu abubuwan.
Kudad'en hannunsa gabadaya sun kare, Allah yasa ma ya na yawo da Atm dinsa da baisan yadda zai yi ba kudin bankinsa sun yi kasa akwai bukatar ya kira Abba ya sake Turo masa kudad'e.
Jiya ba su yi mgana ba Shekaranjiya ne ya kirasa da kansa saboda Matsalan Innani tsohuwar nan matsala ce mai zaman kanta a gidan Abba.
Wai sultana babanta ke son taje shinkafi ta yi hutu tunda ta gama Jss3 zasu shiga Ss1 ita da Siyama. Umma ta shirya mata Tafiya Abba kuma daman bai da matsala, Ammh Innani naji ta fara Tsine ma Mahaifin Sultana ta na kawo Labaran da bata san Tushen su ba ballatana makamar su ba.
Akan Sultana bazata je wajen Mahaifinta ba, ban da Innani da Shegen kafiya da Rikicin Tsufa ta ina zaki raba y'a da mahaifinta? Duk da Sultana yarinya ce tasan Mahaifinta kuma ta na son shi tare da Sauran yan'uwanta.
Umma ta kirasa ta fad'a mai Abba ya ce Sultana ta zauna Tunda Innani ba ta so taje. Shi kuma sai ya kira wayar Innani ba ta shiga sai ya ce ma Umma ta kai ma Innani wayar zai mata mgana Umma tace ya Rufa mata asiri kada Innani ta ce ita ta kai kararta wajen Magajin gida.
Dalilin haka yasa ya kira Abba ya ce in ya shiga wajen Innani ya kirasa zai yi mgana da ita. Innani dole ta yi shuru da bakinta Tunda ya ce mata Sultana zata tafi Shinkafi taga Babanta da yan'uwanta Dole Innani ta amsa, ammh kuma jiya sun yi mgana da Umma tana fad'a masa Innani ma ta shirya kayanta tace kafarta kafar Sultana kada shitu ya cuta mata ya ganta marainiya.
Shi ko kara bi ta kanta bai yi ba innani case ne mai zaman kanta a wannan gidan in ka toshe nan ne sai kaji ta kara balle wata kofar, yasan zuwa zatayi ta yi ta rashin Mutumci sannan ta hana yarinya sakewa a gidan Ubanta tare da sauran yan'uwanta.