*TSAKA MAI WUYA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk
Ku zo ku yi sayayyarku tare da Yar Gidan Imam, inda za ku sami komai cikin sauki, tun daga kan kayan kicin, kayan yara,atamfofi da lesissika uwa uba da kayan gyaran jiki irin na manyan matan da suka San kan su,har counselling mu na yi yadda duk damuwar da ki ke ciki a game da aurenki da gyaran jikinki zaki samu solution. Ku dai ku shigo cikin wannan gidan na karamci kai tsaye domin more tagomashin da ke ciki.
*19*
Koda su ka dawo babu Innani ba wanda ya damu sanin halinta. daman tunda aka ganta da wannan uwar jakar an san sai ta hantse zata dawo.
Kuma daman ta na son garin su Umma tunda Mallam zakari da iyalansa suna biye mata shiyasa ta ke matukar son zuwa garin Gummi fiye da zuwa Shinkafi.
Sadiq ya na so ya koma cikin Satin nan mai shiga daga kamfanin da ya ke Hidimar kasa sun kirashi.
Shiyasa ya shirya tafiya shinkafi ya jima sosai bai je ba tun wani rashin Lafiya da mahaifin Sultana ya yi ya matsa ma Abba suka je tare kuma za'ayi shekaru biyu da faruwar abun.
Wannan karon ma yace Abba ya shirya su tafi ba shi ta cewa illah Toh.
Yaje Gummi da kwana uku su ka tafi Shinkafi shi da Abba.
Tafiyar ta su da Sassafe ne saboda a ranar zasu dawo ba za su kwana ba.
Gidan Baba Sammani suka fara sauka aka rika ina za'a saka da su. Da kansa ya aika ma su Hussau sai ga su kowacce ta zo gaishe da Abba.
In kunga yadda su ke girmama Sadiq ko Abba albarka.
Ga shi matashi ne ammh yadda su ke kallonsa ya wuce tunanin shi.
Dalilin Sadiq yasa Abba ya yi ziyara sosai a garin Shinkafi. Sannan ya kuma Fitar da kudade.
Tunda aka ji yazo garin mutane sai zuwa su ke da bukatun su.
Su Baba Sammani kuwa an ba su na su zakkar har da karin kudad'en da Sadiq ya ware musu.
Kowa ya zo sai yace yaushe ne bikin Magajin gida da Sultana?
Abba ke rattafa bayanin sai lokacin da Sadiq ya gama karatunsa ya baro Zariya gabad'aya.
Gabadaya labaran daga bakin Innani suka fita Sadiq acikin ransa sai fad'i ya ke yi Tsohuwar nan bazata daina karya ba, ta tsufa ammh ba ta san Darajan Tsufan ta ba.
Su ne har gidan su Sultana kowa ya san Sadiq Surukin gidan ne shiyasa karramawan da aka yi musu suma din dai duk mganar Innanin ne na bikin Sadiq da Sultana.
Nan ma Abba ne ya yi musu bayanin ba yanzu ba in Lokaci ya yi zasu sanar da su.Sun jima nan suka yi Sallar la'asar su ka kuma ci abinci sannan suka yi shirin Tafiya. Sun kamo Hanya Booth dinsa cike da abubuwa irin ta mutanen kauye. irin su gyad'a aya da su kuka da kubewa,goriba da sauran su, suka baro Mutanen Shinkafi suna ta zamabad'a musu godiya tare da addu'an Fatan alheri ga Alhaji Sulaiman da Magajin gida.
Ranar da suka dawo har washegari barci Sadiq ya yi ta sha ya na Hutawa duk da wayoyin yan'uwansa sun cika masa waya da kira suna rokon sa don Allah yazo gidajen su.
Kowacce Burinta yaje gidanta kuma bai cika zuwa ba sai dai su suzo su same shi a gida. Gwara ma gidan Surayya tunda itace Big Sis kuma ta su tafi zuwa daya da Sadiq daga ita sai Sa'ima sai kuma Shahida da ke aure a katsina ita in suka shiga katsina za su je Daura sun sha biyawa shi da Tahir.
Sajida sakonsa ne domin Umma tace kwata kwata shekaru biyu ne a Tsakanin su.
Bayan fad'a tsakanin Sako da Sako jininsu kuma bai had'u ba. Saboda Sajida na da Surutu da son jin gulma sannan ta na diban mgana sai ayi mgana da ita ta sirri sai aji ta a bakin wata a cikin su, Mace ce mai kishi da son komai ya zama ita kad'ai ta mallaka shi kuma Sadiq baya son halinta na Surutu shiyasa ba su cika Shiri ba, zai iya kirga saunawa ya taba zuwa gidanta duk da ta na kusa ba ta da nisa da gidan tsakaninsu bai wuce Naira Dari ba.Yafi yarda da Surayya fiye da kowa a dakin su da gidan su. Saboda ta na da kirki da kamewa sannan cikin Nasiha da Lallashi zata yi maka mgana har ka Fahimta. Ya na zuwa gidanta sosai barin ma in yazo garin Hutu ya jima.
Shiyasa wannan karon ma ita kad'ai yace mawa zai zo mata kafin ya tafi.
Ranar da ya cika sati biyu a garin Gusai ya shirya ya je gidanta.
Umma kad'ai ta san ga inda zai je Abba ya fita da wuri Mama kuma bai shiga shashenta kafin ya wuce ba, innani kuma ta na chan bata dawo ba daga ita har su Sultanan.
Umma ce ma da ta kira Mallam zakari tace a ba ma Innani su yi mgana.
Bayan an bata sun gaisa ta tambayeta yaushe za su dawo?
Innani tace uban wa ta ijiye a gidan Sulaimanun da za'a dameta sai ta dawo? Ita ba d'a ba ita kuma ba jika ba kada a dameta sai taga dama zata Dawo tunda Umma taji haka ta kama bakinta Sanin Halin Innani yanzu sai cibi ya zama kari in ma batace ta na so ta yi mata gorin gari tunda taga gidansu ne.
Da ta fad'ama Sadiq karamin Tsaki yaja a fili ya Furta"ku kyaleta Umma ranar da ta gaji kuna zaune zaku ganta. Yaran nan dai su dawo saboda ana komawa Hutu zasu fara zuwa makaranta."
Umma tace"Wa ya isa ya ce su Sultana su dawo Innani ta tsine masa."
Sadiq kai tsaye yace"Ni na isa. Kuma zan kira mallam d'in da kaina nace a bata wayar na fad'a mata."
Umma na Dariya tace"Sai dai kai d'in."
Haka ya ke maida ma Surayya yadda suka yi da Umma da ta tambayesa Innani ta dawo? Shine ya ke gayamata yadda suka yi da Umma.
Surayya ta yi dariya kafin tace"Innani Rigima. Ai in kaine bazata yi fad'a ba tunda Shalele ne."
Bai yi mgana ba sannan bai ko yi mirmishi ba. Suna zaune ne a falon Surayya ta cika gabansa da kayan makulashe yaranta duka basa nan suna gidan kakaninsu na bangaran uba sun je Hutu.