*TSAKA MAI WUYA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj
*17*
Shi ko Sadiq gidan su Hasiya ya je. Daman ya saba in dai yaje a waje ya kan tsaya ya aika yara sai Hasiya ko Habiba su fito su shiga da shi ciki.
Saboda akwai mata a gidan sannan a tsarin addini shi balaggage ne babu tsari ya rika shiga gidan matan aure kai tsaye batare da izini ba.
Duk da matan gidan na su Hasiya kallo garesu ba wani abu ba ne, kamar ba matan aure ba. Shi dai har ya shiga ya fito kansa na kasa ba shi da dogon kallo a rayuwarsa koda da wanda ya sani ne, ko da akwai sabo a tsakaninsu.Yau ma d'in Habiba ce ta fito ta shiga da shi ciki har dakin Amma ya na shigowa da Hasiya ya ci karo ta na ganinsa ta sakar masa mirmishinta shima sai ya maida mata martani cikin zolayar da ya fara mata kwanaki nan yace"Hasiya mai Danwake."
Baki ta tura kafin na juya ina kallon Amma lokaci d'aya ina fad'in"Amma kin gan shi ko? Wai Hasiya mai Danwake ya ke kirana."
Amma na zaune ta na mirmishi na ganin Abubakar d'in, Allah ya sani haka kurum ta ji Allah ya Do'ra mata kaunar wannan bawan Allah, har cikin ranta komai na shi ya yi mata.
Cikin Annurin da kan bayyana saman Fuskarta in har ta ga Abubakar tace"Ke ma ba sai ki rama ba. Da ya kira ki Hasiya mai Danwake sai ke ma ki ce masa Habu mai siyan Danwake."
Gabadayan su suka fashe da Dariya Habiba na rufe bakinta tace"Amma Hamman ne Habu mai siyan Danwake.?
Da ya ke Hamma ta ke kiransa. da Ladabin Fulani yaya kenan.
Abubakar ya yi dariya har sai da Fararan Hakoransa suka bayyana awaje Hasiya ce tace,"Shikenan ko Amma ta kawo shawara."
Sai da ya zauna gaban Amma sannan yace"Hasiya mai danwake ya fi dad'in fad'a ko a baki Amma"
Amma ta yi dariya ba ta ce komai ba gaisawa su ka yi a mutunce kamar yadda suka saba.
Habiba ta kawo masa ruwa a jug. Hasiya kuma ta kallesa ta na fad'in" a kawo abinci..?
Kai ya girgiza Lokaci d'aya ya na Fad'in" na sha fura a wajen aiki. Cikina ya cika Sosai."
Amma tace"ko aikin ne ya hana ka zuwa kwana biyu Abubakar?
Ya na sosa kansa yace"A'a Amma kauye na je. kuma tafiyar ta gaggawace shiyasa ban Sanar da ku ba."
Amma tace"Ayya. Ka same su lafiya ko?
Ya ce"Eh duk sun ce suna gaishe ku Amma"
Amma ta amsa cikin sakewa. Kafin su cigaba da Hira kan rayuwa da sauran su.Rabin Hiran duk na Amma ne shi na shi eh a'a ne sai ko in ta yi masa wata Tambayar.
Habiba islamiya ta shirya ta tafi ni kuma sai na fita waje na Hura gawayi na Dorama Amma ruwan wanka tunda ba ta yi ba.
Daman ban cika zama adakin ba in ya na nan saboda gudun zargin mutane.
Yan gidanmu sun ta bin kwakwafin ko saurayina ne to ganin ya na shiga har Daki kuma su jima su na mgana da Amma sai suka aminta da cewa da gasken dai kila d'aan uwan mu ne.
Kila kuma cikin Dangin Babanmu da suka watsar da mu ne.
A cikin raina na ke jin Abubakar a chan kasan raina na saka shi cikin Layin masu kaunar mu. Ina shiga Damuwa in bai zo ba, Saboda shi ma ina Fargaban kada watarana a rabamu da shi ina jin Tsoron faruwan hakan shiyasa in bai zo ba na rika shiga Damuwa kenan ina faman ce ma Amma" yau fa bai zo ba"
Amma kan tausheni da cewa"Zai zo Hasiya. A jikina na ke jin yaron nan ba irin sauran ba ne. Zai zo in sha Allahu."Yau ma sun jima suna Hira da Ammah sai da yammah ta yi ana gabda kiran mangariba sannan ya yi ma Amma sallama ya tafi. Bayan ya ba ta dubu uku Amma ta ki karb'a ta na Fad'in"Kai da ka ke d'an makaranta Abubakar kuma ka ke Hidima damu? Ai sai abun ya yi maka yawa."
Haka ta ke fad'i duk sanda ya yi mata wani karamin kyauta.
Shi kuma kai tsaye ya ke cewa"Amma kin manta na fad'a miki ina Hidimar kasa ne? Suna biyan mu duk wata kuma Dubu uku ai ba Hidima bace."
Amma ta amsa lokaci d'aya ta na Fad'in"Allah ya yi albarka. Allah ya jikan iyayen ka, Allah ya haskaka makwancin su Allah yasa suna cikin Dausayin Aljannah. Nagode sosai Allah ya tsare ka duniya da Lahira."
Shi dai na shi amsawa da Ameen ne cikin jin dadi.
Ko da ya fito da niyyar tafiya samuna ya yi ina ta fama da fifitan gawayi ya ki kamawa saboda nayi rashin sa'a ya na da Sanyi a jikinsa.