Page 9

64 9 0
                                    

Karamar hukumar rogo dake a cikin jihar kano gari ne madaidaici, tana da yanki 802 kilometres^2 da yawan jamaa 227,742(kidayar 2006) Garin rogo tana iyaka da kananan hukumomin karaye da kiru daga gabas, karamar hukumar makarfi a jihar kaduna daga kudu, kananan hukumomin danja da kafur a jihar katsina daga Arewa. Garin na rogo gari ne na noma da kiwo tun shekara da shekaru, mutanen cikinsa na zaune lafiya cikin amince, kwanciyar hankali, rufin asiri da yalwar arzikin noma.
   
Unguwar jajaye, rogo 5:20pm

Tsakar gidan kato ne sosai shafe da siminti Ko ina da Ko ina, a share yake tas tas dan Ko abincinka ne ya fadi kana iya dauka Ka karkade kaci abunka Ba tare da fargabar komai ba. Dakuna ne a jere Ko wanne da ciki da falo daga cikinsa,  sai wasu blocks din dakunan dake can gefe, general dakin girki ne katoto sannan bandakuna guda 2, daga can gefe kuma kusa da kofar shigowa rumfa ce ta hatsi da kuma Kewayyen waje da ake kiwon shanu, awaki da kuma raguna, kiwon kaji ne kawai baayi a gidan Wanda ina tunanin shi ya kara contributing to tsaftar gidan har ma kuma da karancin mutane dake rayuwa acikin sa a yanzun. baba gazali da baba Abubakar ne agidan tare da iyalansu, baba gazali matar shi daya da yayensu 6 sun aurar da biyu,sai baba Abu mai mata 2 dakuma yaya 5 uwargidan tanada 4,amaryar kuma tana 1.       Goggo amarya agidan take rayuwa dasu tunda ainihi nan ne gidan aurenta kuma general family house, tanada nata dakin falle ciki da parlor. Rayuwar gidan rayuwa ce kadaran kadahan facalolin a tsakanin su kowa ta ciki na ciki sabanin su mazan da suke zaune lafiya lau, Goggo bata yarda wata tazo ta wargasa zumuncin yayanta dakuma jikokin ta ba, Hakan ne yasa duk suka shiga taitayinsu.
        Ina zaune kan karamar kujera Ana min kitso, kitson ya dauke mu tsawon lokaci Dan tun bayan laasar muka fara shi, gashi na nada cika, tsayi da kuma santsin da ba kowa ne yake iya kitse shi ba sai qalilan din masu kitso, ciki kuwa har da Habiba yar uwata kuma sa'a ta acikin cousins dina dake rayuwa anan rogo.
Ban cika yin kitso ba amma duk lokacin dana tashi yi to kananu, siriri ake min Wanda shine kawai zaiyi kwanaki bai warware yayi rashin kyan gani ba, habi ita take min kitso tun ada kafin tayi aure tabar gidan shekaru 4 da suka wuce, har yanzun indai na shigo garin Ko kuma in wani shaanin ya kawo su kano. Tana ta mita tana kitson kamar kullum nide ina jin ta kawai ina murmushi, Goggo Amarya dake zaune kan tabarma tana ta gyaran shinkafar tuwo tace
   "Oh ni Amarya na shige su, wai habi idan kin gaji da kitson nan mana ki sakar mata kanta kowa ya huta, ke ma Ummi da naci kike, Ana miki wulaqanci akan kitson da kowa ya iya, jiyan nan Salame ta shigo ta miki tayin kitso amma kika ce baza kiyi ba kinfi son na habi, habin kuma gata tazo amma sai wulaqanta ki take ke kuma kin nace"
    Goggo ta karasa fade cikin fada Dan ta gaji da mitar habi, habin ta kyalkyace da dariya sannan tace cikin tsokanar goggon
     "Goggonmu kenan, ina fa zata iya hakura da kitso na ai tasan duk cikin kano ba Wanda ya ke iya mata mai kyan nawa, ni sauri nake in tafi gida na bar dana a wajen yaran can na gidanmu(tana nufin yaran kishiyarta) sannan kuma ni zanyi tuwon dare, Kinsan ni inada miji ba kamar su wae ba"
ta fada tare da mintsinin ummin a kafada.
Abun ma ni dariya yake bani kullum idan naji habi da sauran cousins dina wadanda sukayi aure suna mun gorin miji da aure, inda sabo na saba dashi amma Abu ne da baka iya sabo dashi, bashida dadi ko kadan duk lokacin da akayi maka shi sai kaji shi sabo sannan kaji zuciyar Ka ta tabu. Ban ce mata komai ba Haka ma Goggo da Ko dagowa batayi ba daga aikin ta, har Allah yasa ta karasa kitson ta tashi ta karkade jikinta tare da zuwa can wajen famfo ta wanko hannayenta, sallama tayi wa Goggo sannan ta shiga dakin mahaifiyarta Dan yi mata sallama itama, nima na shiga uwar dakar Goggo na dauko hijabi na Dan na raka ta zuwa kofar gidan, muka fito har wajen soron gidan sannan habi ta Dan tsaya tare da riko gefen hijabina tace
    "nikam Ummi yaushe wannan balaraben saurayin naki zai fito ne ayi auren nan? wallahi Ummi kullum kara girma kike bana jin dadin ganin ki Haka ba aure, ji bi fa nida haulatu saaninki ne amma shekarar mu hudu da aure har mun Haihu, Nide ina mai baki shawara ki maida hankali kisa ya fito ayi abunnan in kuma bayayi ne ki ba manemanki dama su fito, da kyan ki da komai kin wani mannewa mutum guda, Ko da yake ku yan binni ne sai masu kudi da kyau Ko?
    Ta fada cikin gatse.
Ire ire wannan maganganun na saba jin su Indai akace na zo rogo, ni har ga Allah suna bani dariya sabida yanda suke dagewa kamar da gaske abun na damunsu, iyayena da sauran yan uwanmu da sukayi ilimi mai zurfi kuma suke rayuwa a cikin birni wannan tunanin baya zuwa kansu,for goodness sake I'm just 21 years old..... karatu muke yi amma Hakan baya nufin idan Allah ya fito miki da miji zasu hanaki aure but no one will pressure you, pressure sai kazo rogo wajen su habi, Wanda Allah na tuba babu wani abun burgewa a nasu auren, duk dattijai masu mata bibbiyu suka aura aka kaisu gidan gandu cikin kishiyoyi kuma. Haka suke rayuwa cikin rashin nutsuwa da  kishi kamar abunda ya kawo su Duniya kenan. Na dafa kafadar habi nace
    "habibalo kenan, nagode da shawararki sosai sannan kuma kar ki wani damu habi, aure lokaci ne kamar yadda lokacin ku yazo har kukai ku Ka Haihu, nima inada niyya kuma zanyi inshaa Allahu.  Saurayin nan nawa kuma waye yace muku balarabe ne wai? Bahaushe ne kamar ni yama fi ni iya hausa, zaizo har nan rogo ya gaishe ku ai sai kiji hausar a bakinshi" 
    Na fada mata cikin raha, yaqe kawai tayi sannan mukayi sallama tayi tafiyar ta. Na koma cikin gida na tadda Goggo amarya har ta gama aikin ta, ta tattare wajen da muka yi kitson, banji dadi ba sai naga kamar na sa ta aiki, Allah sarki Goggonmu bata da daukar komai a ranta Ko jin kanta a matsayinta na uwar masu gida, she's the most humble woman one will ever meet. Na zauna a gefenta kan tabarma ina mata sannu da aiki muna Dan tadin mu har sauran yaran gidan suka dawo daga islamiyya aka hau hirar dasu.
      yau kwana na hudu a rogo, gaba dayanmu mukazo ganin gida har da yaya zainab a motar baba amma su kwana daya sukayi suka koma kano washe gari, ni dama da niyyar yin wasu yan kwanaki nazo.  Na je gidajen yan uwa sosai nayi zumunci, wasu kuma da sukaji nazo sunzo da kansu mun gaisa, abun Ka da mutanen kauye masu kara da alheri kullum tunda mukazo sai an kawo min abincin rana wasu kuma su aiko dana dare, abinci da kayan kwalama na gargajiya har sai da na ture. Haka zamu fita da dare nida kanwata hafsatu yar gidan baba Abu mu zagaya unguwar cikin hasken farin wata, so peaceful and therapeutic.
       Sosai muke video call da fu'ad ina nuna mishi wajaje da gonaki yayi ta shaawar su, har cewa yake shima zai taho coz he have been missing me so badly.  Fu'ad ya tabbatar min da cewa yayi maganar aurenmu da mahaifiyar shi sannan babu wata matsala kuma tayi farin ciki da alamarin, anytime soon idan babansu yayi fixing date na zuwa neman auren zai fada min na sanar agida. Describing how happy I am is just an understatement, hankali na ya kwanta sosai ba kamar da danake ta fargabar Ko mamanshi bazata amince da ni ba. I feel like I'm dancing in the sky now, every thing is becoming more colorful and beautiful to me, anya akwai abun da yafi shirin mallakar masoyinka dadi a rayuwar Dan Adam??
     

Muhibbi♥️Where stories live. Discover now