Ruwan zafi nake zubawa acikin flask amma hankalina baya wajen kwata kwata, cikar da flask din yayi har ya Dan zubo a tafin kafata ne ya dawo da ni hayyacina... "ouchhh" mace sannan na debo Dan gishiri kadan na barbada a kafar daidai wajen da ruwan ya zuba Dan hana shi kumburi. Nayi zurfi a tunanin abunda yake damun masoyina, tun safe nake Abu daya amma bai bani wani kwakkwarar amsa ba har yanzun da dare yayi. Duk da ina iya kokarinta wajen yakice tunanin ganin yau Abbanmu ya dawo daga umarar daya tafi bayan dawowarmu daga rogo kwanakin baya, muna ta shirye shiryen tarbar shi tun safe har Goggo Amarya tazo daga rogo a yau din. Ruwan tea daya zame mishi wajibi kullum shi na dafa zan kai mishi parlor amma bani da wani karfin jiki sosai, shawara nakeyi Ko nakira munah ta miqa musu ruwan tean tunda dama tun dazu mun gaisa da Abban nayi mishi sannu da zuwa. So nake naje na kira Fu'ad Dan a yau sai na sashi dole ya fada mim abunda ke damunshi, bazan kuma kwana da wannan dutsen a kirjina ba, ganinshi cikin damuwa shine Abu na karshe da zanso ya faru.
Shiga falon Namu nayi na tarar da muna da aysha anyi kaca kaca anata wasa da sabbin toys din da Abban ya taho musu dashi,
"zo nan munah, karbi flask dinnan ki kai falon Abba, idan ance ina nake kice na kwanta bacci,"
Munah ta karba ranta bai so ba sabida an katse mata wasan ta, ta fyalla a guje Kuwa Dan tayi sauri ta dawo su Dora.
Ina kwance rigingine nayi dialing number shi kenan sai ga munah ta yi knocking tare da shigowa,
" ya Ummi kizo in ji Abba"
Ta fada ba tare da tsayawa jin me zaa ce ba ta fita aguje zuwa wajen wasanta.
Gabana ne yadan fadi sabida ba kasafai muka saba irin wannan da Abban ba, babu wannan shaquwar da zai kirani muyi wata hira saidai ya kiraka yayi maka tambayoyi game da school, islamiya Ko ya kiraka ya saka wani aikin Ko ya bada wani umarnin, har gara muhsin, aysha da munah Abban yafi jansu sosai a jiki fiye da ni da zee. Dadin dadawa kuma yau goggon tasu da mami duk suna falon a wajen shi, janyo hijab dina nayi na saka tare da kama hanyar falon Abban.
Na samu waje a gefen kujera 2 seater na zauna bayan nayi sallama tare da yi musu barka da dare. Abban yana zaune a gefen Goggo a kujera 3 seater, mami kuma tana zaune akan carpet daura dasu.
Abban yayi gyaran murya sannan yace
"mamana, ya makarantar? Kunata shirye shiryen gamawa Ko?
" eh Abba, sauranmu 3weeks a fara final papers, "
" toh Allah ya baku nasara, na kiraki ne gani ga mahaifiyar ki ga kuma goggonki, me kuke ciki game da maganar yaron nan dayake zuwa wajen ki?
Gabana ya fadi amma sai nace
" lafiya lau Abba, yana zuwa har yanzu, muna tare"
"Ai nasan yana zuwa din, amma ba wannan nake son ji ba, yaushe zai turo manyan shi na gansu? Dan babu wani amfani yayi ta zuwa wajenki shekaru kusan biyu kenan ba wani progress, me Hakan yake nufi kenan?
Abban ya fada muryar shi tana Dan hasalowa sama. Ummi ta kalli mahaifiyar ta dake gefe tana fatan ta saka baki amma Ko alamun magana bata dashi, dan idonta nakan TV da aka rage volume can karshe. Hankalin Ummi ya tashi Dan dama wannen fagen take tsoron azo kuma da alama anzo din.
"uhmm Abba yayi maganar turowan, yayiwa mahaifiyar shi magana tace zaa turo kwanannan...."
Ummi ta fada muryar ta can Kasan, bata sani ba idan fadin Hakan yanada amfani tadai fada ne kawai.
"mahaifiyar shi kuma? Mahaifiyar shi ce ke tsara yanda zaa turo neman aure? Ke Ummi sa idon ki a nawa, tuntuni dama na zuba miki ido ne sabida naga alamun kuna san junanku sosai sannan yaron kirki ne, amma duk Namiji indai da gaske yake bazaa dauki wannan lokacin bai turo manya gidanku ba. Da hankalinki da ilimin ki karki yarda irin wannan yaran manyan suzo suyi wasa da tunanin ki, muma din ba mutanen banza bane da darajar mu"
Goggo amarya tafada da tun dazu batayi niyyar yin wata magana ba amma taga abun kamar Ummi ake shirin rainawa wayo a lamarin, abunda bazasu laminta ba kenan.
Abba ya kara da cewa
"nasani yaron da izinina ya fara zuwa wajenki amma Hakan ba yana nufin izinine na har abada ba, kin kusa gama jamia Allah yasani banida burin na cigaba da ganinki agabana bayan Haka, even though I'm not pressuring you, Inaso ki cigaba da addua sosai kuma ki nutsu ki gane mai qaunarki, nan da wasu yan watanni bazan cigaba dayi wa yaron uzuri ba dole ne ki fito da wani cikin manemanki ki yi aurenki. Ina miki fatan nasara a final exams dinki, tashi ki shiga ciki"Monday, 11Am.
"mansur, ina zan sami number David? I need it urgently"
Mansur dake danna laptop akan table ya dago ya kalli Fu'ad din da mamaki, mamaki mana tunda baya mantawa fu'ad da kanshi ya miqa David hannun police shekarun baya sabida kamashi da sukayi yana gab da scamming dinsu makudan kudade akan zaiyi musu visar mutum 8 Dan wani taron kasuwanci zuwa Qatar.
"gaskia banida contact dinshi yanzun, amma ai Kasan office dinsu dake Abuja, why not check it yourself? Amma Meyasa kake neman shi? Fu'ad? Don't tell me you gonna lea... What? "
Mansur ya fada tare da ture system din baya yana zaro idon shi cikin mamaki."shiyasa nake son ka, akwai Ka da iya saukakawa mutum bayani, tafiya zamuyi mansur, we gonna leave everything behind and go, I mean every damn thing! Meyasa zan zauna a kasheni da rai na, meyasa zan zauna mama tana shaping mun rayuwa duk yanda taso? Daddy yana bayan ta shima..... Nah, not again wallahi"
Fu'ad ya fada hankalinshi kwance kamar normal hira sukeyi. Ya fahimci duk wani daga hankali bazai amfana mishi da komai ba, he needs to be smart and act accordingly shiyasa bai yiwa kowa maganar yanda sukayi da maman ba, bai fada wa kowa ba sai Aminin nashi mansur, Ko Ummi da abun ya shafa 100% bai fada mata sabida he doesn't want her to panic har a fahimta agidansu plans dinsa su wargatse. He's trying all his possible best to be calm even though he is dying inside.
He lost another big hope jiya dayaje ya samu daddy a parlor shi, bai ji dadin samun maman a wajen ba coz ya so suyi magana shi kadai da daddy, he waited for a few minutes Ko zata tashi amma bata da niyya. Yana cikin shawarar yayi maganar agabanta or not sai muryar Daddyn yaji
"Ango Ango, ya shirye shiryen ne? Naga baka shawarar komai dani ai hala sai Abdulsamad shine yaro Ko?
Daddy ya fada cikin raha sabida ya saba da yaranshi sosai suke wasa a tsakaninsu.
" Daddy maganar nazo muyi dama, Daddy mama told you about johara ni kuma ba ita nace ba, mardhiyya nakeso aje wajen iyayenta please, ita nakeso daddy" fu'ad ya fada cikin dakakkiyar murya Wanda babu tsoro Ko damuwa acikinta
"bamu gama maganar nan bane fu'ad? How dare you!!!
Na Riga na yanke Johara zaka aura Ko kana yi ko bakayi, kada Ka sake min zancen wata yarinya ina wajen, wallahil azeem zan saba maka!
Hajja insaf ta fada ranta yana tafasa sosai a wannan karon, ji takeyi tsanar yarinyar yana taso mata duk da ada bata tsaneta ba kawai dai aurenta ne batayi naam dashi ba, babu wani dalili kuma ba wata hujja sai na kasancewarta ba jininta ba."mama taya zan auri johara for goodness sake, johara is just a cousin to me banida wata alaqa da ita, nafi shekaru ban sa ta a ido na ba ma, I don't have any connections with the girl, mama you don't have that right Allah..
" Fu'ad! Are you alright? Kana cikin hayyacinka kuwa? Mahaifiyar Ka kake fadawa Haka a gabana kuma? Yaushe Ka zama Haka?
Daddy ya fada cikin bacin rai sounding so confused sabida bai gane ma tushen maganar ba, wace mardhiyya? Bai gane fu'ad baya son johara ba, daman ba fu'ad bane yake son ta, hadin insaf ne?
Ya juya kallon shi ga insaf din with fire razing from his eyes, bacin rai gami da haushinta yakeji sosai for the 1st time in forever. Amma shi ba namijin da yake yiwa mace tsawa bane, ba Namijin da zai bawa uwa laifi agaban danta bane, Hakan yasa ya kuma duban fu'ad din yace
"she has every right on you kaji Ko? Even more than I do, Mahaifiyar Ka ta zaba maka macen aure sannan Kana ja in ja da ita? Abdulsamad kake so Ka zama? Baka da wata hujja da zaka ki auren johara, kuma ba zaka maida ni karamin mutum ba sabida naje har wajen mahaifinta kuma ya baka aurenta nan da wata 3 masu zuwa. Fita Ka bani waje you are dismissed!"
Prof bello ya fada da dukkan wani bacin rai da yayi shekaru baiji irin shi ba.
A karo na biyu fu'ad ya kuma barin zuciyar dake dokawa mahaifinshi a wajen ya fita daga falon baya Ko ganin gaban shi, bashida sauran wani hope yanzu kuma sai a wajen Allah dakuma mardhiyya. Hakan ne yasa ya fara laluben mafita agaresu, har ya samo abunda yake ganin shi kadai zai zama mafita..... They need to leave.
YOU ARE READING
Muhibbi♥️
RomanceA forbidden love! Rayuwa bata cika tafiya kan turbar da bawa yake muradi ba.... Ku biyoni Dan karanta labarin Fu'ad da mardhiyya, ku biyoni dan karanta irin tasu qaddarar. COMPLETED!