Page 16

46 4 0
                                    

Knocking  kofar parlon Daddy da akayi ne ya sa Daddy tashi daga kwanciyar dayayi a cinyar Insaf din, sannan itama ta gyara mayafin rigar ta tare da cewa
    "shigo Sadiya"
Sadiyan ta Bude kofar a hankali riqe da wani Black tray dauke da tea pot mai kyau na glass kuma transparent sai kananun cups dinshi irin na kasar turkey, sai wani container karami cike da brown sugar dakuma teaspoons, Ta dora akan center table dake parlon sannan ta fice tare da janyo kofar.  Hajja Insaf ta tashi ta zuba musu cinnamon and lemon infused tea,Daddy ya karbi nashi yana sha a hankali yana danna katuwar tablet din dake gabanshi.
      Jefi Jefi suna hira da Insaf din da itama take ta danna wayar tata, magana sukeyi da wata mata da ake cewa Hajiya ramatu. Hajiya Ramatu shahararriyar yar kasuwa ce da duk wasu mata masu ji da kansu kuma suka San harkar sutura toh a wajenta suke sayan kaya musamman atamfofi.  Kamar yanzu da ta turowa hajjan tarin atamfofi da laces na yan ubansu dukkan su sun ba dubu 50 baya, hajjan tana ta zaba ba tare da ko tunanin aljihun ta ba ko kuma ace aljihun daddy, tuni ta jima da fara hada lefen Fuad din Dan yanzu tasan zasu iya cika akwati 10 da kaya kuma ko rabi baayi ba, Dan akwatina, laffayas, English wears, underwears, jewelries da cosmetics baa Nigeria take da niyyar siyansu ba.
       Fuad ne ya shigo parlon Daddyn bayan yayi sallama, duk sai yaji wani iri Dan ya kwana biyu Rabon daya shigo falon tunda ba fuska a wajensu, yau ne yasa aniyar zuwa wajen daddy da maman domin ayita ta kare. Samun waje yayi ya zauna bayan ya gaishe su duka, hajja Insaf ta dubi Dan nata da kewar shi takeji Kamar ta halaka ta, tayi kewar shi sosai amma tana sane da duk abunda takeyi, she needs to do this sabida fuad ya gane cewa they ain't joking here, ba zata biyewa zuciyarta dake ta rokon ta akan ta bar fuad din yayi abunda yakeso ba sabida tana ganin Sam zabin da fuad yayi bai dace da shi ba.
Abunda fuad bai sani ba shine yawanci kullum da tsakar dare sai ta shiga har dakin baccin shi, ta shafa kanshi tayi mishi addua sannan ta fita.
       Daddy yayi mishi tayin tea din amma fuad bai sha ba duk da ga kamshin cinnamon ya karade wajen, a halin dayake ciki yanzu ko yawu baya jin zai wuce ta wuyanshi har sai ya fadi abunda ke ranshi sannan ya kuma ji amsar da zasu bayar.
   
  "Daddy, neman Alfarma nazoyi a wajenku, ina fatan zaku fahimceni sannan ku taimakamin sabida Allah....
     Fuad ya fada da dukkan wani fata na rayuwarshi, sannan ya cigaba da magana Dan ganin yanda duk suka bar abunda sukeyi suka zuba mishi ido.
     " Daddy na bi Allah sannan na biku, na karbi auren johara da kuka min umarni dashi da zuciya daya, Amma Dan Allah Daddy kayi min izini na hada da mardhiyya itama, Ka amince min na aure su duka biyun. Bazan iya rayuwa babu Mard....."
       
       Bai karasa maganar ba sakamakon tsawar da hajja Insaf ta daka mishi Kamar an watsa mai ruwan zafi haka ya ji saukar muryar tata, ko daddy sai da ya waiwayo ya dubeta da mamaki.
     " kai da Allah rufe min Baki! baka isa ba Fuad! wallahi baka isa ba, ni zaka mayar ban San abunda nakeyi ba? Mu zaka mayar kananun mutane? Har kazo gabanmu kana cewa zaka auri mata biyu, a ina ake haka? toh bazaka aure ta ba wallahi, sai naga uban da zaisa Ka....
      
      " Insaf!!
Muryar Daddy ta ratso cikin tata muryar shima da nashi karajin, da sauri Insaf ita da fuad suka waiwayo suka dubi Daddyn cikin mamaki. Insaf ba zata ce ga ranar karshe da daddy ya Kira ainihin sunan nata ba balle tsawa, tsawa ma ai ko alamun tashinta bataji agidan balle ayita. The only place where daddy yake ambaton full name din ta shine a text message, a love letter ko a gift card from him. Anan ne kawai take ganin sunanta a rubuce bawai a zance ba, Amma yau, yau Daddyn ya daka mata tsawa??
      "Ni ubanshi ni zan amince mishi ya auri mata har hudu idan yana muradi ko da duk abunda na mallaka zai kare, kuma ke Insaf baki isa ki hana ba.  Da farko na baki gaskia na kuma goyi bayanki akan wannan auren da tuntuni Fuad has already confessed baya so, Dan me zaki hana shi Samun farin ciki a rayuwarshi? Sabida na sake miki da yawa? "
      " Fuad Ka sanar wa da iyayen yarinyar cewa zamu zo neman aurenta wannan lahadin mai zuwa Amma da sharadi fuad, da sharadin zan shaida musu cewa ita din zata zo a matarka ta biyu"
   
    Daddy ya fada tare da daukar wayar shi ya bi corridor da zai  kai shi bedroom dinshi, Hajja Insaf da har yanzu ta kasa fahimtar abunda fuad din da daddy sukayi, tana Zauna ne kawai akan sofa kwalla ta taru a idonta. Babban abunda ya fi bata mata rai shine tsawar da Daddy ya mata kuma agaban danta, Dama wannan ranar zatazo? Sannan kuma da bakin cikin fuad yana fadin zai mutu akan  wata yarinya, abun ya taru yayi mata yawa.
      Fuad da duk ya rasa farin ciki zai yi ma ko bakin ciki sabida shima bai tsammaci tsawar nan daga wajen daddy ba, bai kuma ji dadi ba ace yau Daddy yayiwa mamintashi tsawa akan sa, why all these? Meyasa abubuwa basa tafiya daidai ne?
      Karasowa yayi kujerar da maman ke zaune ya kamo hannunta tare da kwantar da kanshi akan cinyar ta,  a hankali yaji hannunta yana shigewa cikin sassalkan gashinsa mai tsantsi.
      " tashi Ka fita Fuad, I need to be alone"
       Hajja Insaf ta fada a hankali Kamar mai rada, ya dago ya kalli yadda fuskar ta tayi jaa, hancin nan yayi jaa abunka da farar fata. Bai taba ganin ran maman a bace haka ba, he wants her to yell at him, so yake tayi mishi fada zaifi jin sauki akan wannan shirun nata... Amma sai ya tashi kawai ya fice tare da Jan kofar falon. 
      Zuqar numfashi tayi tare da fesarwa a lokaci daya, wani hawaye mai dumi yana biyowa ta kan kumatun nata. Share hawayenta tayi ta fita daga falon bayan ta kashe mishi fitilun parlon Dana dining area, dakinta ta koma ta kwanta akan makeken gadonta still zuciyar ta tana zafi.
       zata kyale daddy ya sauko, zata kyaleshi yayi tunani and as well yayi missing dinta. Akan wata yarinya can bazata yarda ta sami matsala da Daddyn ba balle a yanzu da shirye shiryen tafiya yayi nisa dan ta karasa siyayyar kayan auren johara. Da wannan tunanin bacci ya dauketa Wanda sam bazaa kirashi mai dadi ba.
         Da gari ya waye bayan ta idar da sallar asuba, da kanta ta sauka kasan ta shirya wa daddy favourite food dinshi, Funkaso da farfesun cow leg dakuma kunun shinkafa, duk da bashi ne a menu ba yau haka ta sa aka fara shirye shiryen yinshi.
      Tura kofar dakin tayi bakinta dauke da sallama, ta yi kyau cikin wani Swiss cotton lace red color, tana ta zuba kamshi kamar amarya,  tasan Daddy yana kaunar red color a jikinta shiyasa yau ta kudurci niyyar mantar dashi komai daya faru last night. Amsa sallamar tata yayi yana shirin warware babbar rigar shi, Ya gama shirya wa tsaf Dan tafiya wani taron seminar da Jamiar bayero ta gayyaceshi,  ba karamin kyau matar tashi tayi ba Amma ya dake bai nuna ba sabida incidents din jiya ba karamin bata ransa sukayi ba.
       Ba tare da nuna alaman komai ba hajja Insaf ta gaishe da mijin nata, ta karbi babbar rigar tare da taimaka mishi yasa, wannan ne yasa shi kanshi Daddyn jikin sa yayi sanyi ya dena fadin rai dayake tayi da farko, bai kara jin mamaki ba sai da yaga Abincin data shirya mishi, a ranshi ya na jinjinawa Insaf din Dan tabbas Samun mace irin ta sai ansha wuya,bata fushi kuma bata fasa kula dashi komai zai faru a tsakaninsu Kuwa.
     Hakan yasa qaunarta gamida ganin girmanta ya karu a zuciyarshi sosai  yana jin cewa bashida tamkarta kuma zai iya yin komai Dan farin cikin ta.
       Insaf tana sane da yanda ta shigo da farko ta sameshi yana ta faman cika da batsewa, she intentionally ignored that ta cigaba da yin duk wasu abubuwan da ta saba mishi har ma da kari. Tabbas ta laqanci mijin nata sannan kuma ta laqanci zaman aure, shiyasa har gobe har abada bata yarda da wani Abu wai shi boka ko maganin mallaka, they do not have it in their dictionary. Bata yarda wani kato ya tsara mata yanda zatabi da mijin ta ba, bata yarda ace wani ne zai gaya mata yanda mijin ta zai so ta ba. Insaf Bata da aboki ko abokiyar shawara akan duk abunda ya danganci iyalinta, bata yarda da kawaye ba Sam shiyasa babu wata kawarta da ta San sirrinta ko daya. Tun daga lokacin da Daddy ya fara lomar Funkaso da kunun gyada ya manta da duk wani fushin daya kwana yanayi da Insaf, ya manta da komai a duniyar, baya gane komai sai kyakkyawar matarshi dake gabanshi, his every breath depends on her love.

Muhibbi♥️Where stories live. Discover now