Washe gari nayi bacci sosai Wanda na jima banyi irinshi ba, sai goma ta wuce na farka Dan ko shirin su iman na tafiya school banji ba. nayi wanka na shirya sannan na fita parlon Dana dade rabo na dashi, Dan ko abinci saidai sayyada mai aikin anty laila ta kawo min daki.
Falon shiru ba kowa amma ga food flasks din abinci akan dining, na zuba masa da miya naci, karar daka da nake jiyowa daga bayan gidan yasa nayi hanyar kitchen din na fita ta kofar kitchen inda bayan gidan yake, Tarar da Baba hansai nayi ita da sayyada suna ta dakan yajin hannu da alama yau wake da shinkafa zaayi ko danwake.
Baba hansai tana gani na ta fara farin ciki
"lale lale da uwar dakina, tafisu tafi sauran mata, ko kefa yar nan ki fito kisha hantsi kiga ranar Allah, amma ace bawa ya kunshe kai a daki kwana da kwanaki Iye? ki kwantar da hankalinki uwar masu gida, kinji?"
Da ace da ne da nake mardhiyya ta da tuni na biyewa baba hansan mun fara wasa da dariya, Dan baba hansai tamkar kaka take a wajenmu, asali a rogo take gidan su mamina da Anty laila, ita ta rainesu muma kuma ita take mana wanka sanda muna jarirai har ayanzun da take zaune agidan anty lailan tun bayan haihuwar iman shekaru 9 da suka wuce, tana zaune dasu ne kawai bawai a matsayin mai aiki ba, ta na zaune da su a matsayin ta na kakarsu mai kula da yaran har ma da Anty lailan.
baba hansai tana sanaar ta na saida yaji dakan hannu da garin kunu kala kala mai shegen dadi, Allah yayi mata wannan baiwar Dan har daga gari gari ake zuwa siyan yajin ta da garin kunu.
"baba kenan, ba zaki gane ba, yau Danwake zakuyi ne?
Na fada a gajarce Dan bana so zancen yayi tsawo. Kamar ta gane mai nake nufi itama bata kara zancen ba muka fara dan taba hira har Anty lailan ta fito nan inda muke, ganina da tayi yau a waje ba karamin faranta ranta yayi ba, taji dadi sosai Dan adduarsu a kullum itace Allah ya bawa Ummin dangana, ya sanyaya mata zuciyar ta sannan ya bata ikon wannan jarabawar.
Ban wani jima sosai a wajen ba na tattara na koma dakin da ya zame min komai, na koma na Shige cikin bargona ina jin yanzu nan ne my only safe place. Duk lokacin da na rufe hango wannan daren daya zamo dare mafi baqi a rayuwata nake yi, daren da har kasa ta rufe idanuna bazan manta dashi ba, daren da yasa na fara fuskantar inda qaddara ta ta dosa.....
Ranar lahadin da zaa kai kudin aurena rogo rana ce mafi dadi a rayuwata, inata kallon agogo ina ayyana nasan yanzu an gama sa ranar aurenmu nida Fuad, na Riga na zama tashi shima ya zama nawa abunda ya rage mana kawai daurin aure ne, na tuna yanda zuhra tazo gidanmu a ranar just to celebrate with me, tana tare dani har yamma tayi ta fara shirin tafiya, na rakata bakin titi tana ta min hira tana tsokanata wai na fara kyallin amarci, munata hirar mu muna kyalkyale dariya.... Ashe tazarar dake tsakanina da yin wani murmurshin tazara ce da ba wadda yasan nisanta sai Allah.
Abun da ya bani mamaki Shine yanda banga wani ko wata ta kira wayar mami Ana mata Allah sanya alkhairi ba sabanin yanda nasan anayi, ko Goggo Amarya bata kira waya ba, yaya zainab ma bata kira ni ba ko mami. Kowa dif naji shi tamkar ba wani muhimmin abune ya faru a ranar ba, Abban mu dama baya ma garin gaba daya but I was expecting him to call mami and say something. Tsakanina da mami akwai kunya sosai Dan haka ko giyar wake Nasha bazan iya tambayarta mai ya faru a rogo ba, amma ina sane da yanda ta chanja itama bata cikin walwala. Wayar da mukayi da Fuad washe garin ranar ita ta kara tabbatar min da cewa abubuwa basu tafi daidai a rogo ba, ya fada min cewa iyayena basu Riga sun tabbatar da amincewar su ba sun dai ce zasu kira waya da zarar sun gama yanke shawara, ya kara kwantar min da hankali da cewa ba wani Abu bane.
Abun yayi matukar daure min kai Dan ban San wata shawara kuma zaa yanke ba,na dai ture wannan tunanin daga rai na.
na daure na cigaba da harkokina har Allah ya dawo da Abbanmu bayan sati daya. Lokacin da ya dawo naga an Bude store room dinmu Ana ta shigo wa da kwalayen deep freezer da kuma Fridge, da wani kwali babba sosai dayayi kama da na TV, munah tana ta murna tana tsalle wai an siyowa yaya Ummi fridge da TV. Ganin hakan ne yasa na kara tabbatar da cewa maganar auren mu da fuad na nan daram tunda ga kaya nan Abba ya siya.
Komai ya Birkice ne lokacin da Abba ya kirani falon sa a wannan daren daya dawo, na shiga falon na tarar da mami itama a kusa da Abban tana kokarin hada mishi shayi, da farko komai ya fara tiryen tiryen Abba yana tambayata exams din da muka sha fama da ita, inata amsa tambayoyin da yake min game da lokacin da results dinmu zai fito.
Yayi gyaran murya tare da cewa na bashi dukkan nutsuwata na saurareshi da kunnen basira, Abunda Abba bai sani ba shine ban taba maida nutsuwata na Bude kunnena sosai ba kamar yadda nake a yanzu Dan ko tafiyar kiyashi ina iya ji sabida tsabagen nutsuwar da nayi, buri na kawai naji Abba yayi min bayanin cewa sun bawa Fuad aurena ga kuma ranar da suka tsayar na daurin auren, Amma me?
Bayanin muhimmancin yarda da ko wace iriyar qaddara da naji Abba ya fara yi shi ya sani na fara jin numfashi na yana barazanar ficewa daga kirjina, na cigaba da sauraren shi har zuwa gabar da ya ce
"Shin yaron ya miki bayanin cewa ku biyu zai aura daman? Kunyi wannan yarjejeniyar dashi?
Tamkar tsawar dake barazanar tarwatsa duniya haka naji wannan zance mara dadin ji, zance mafi muni a tarihin rayuwata, cikin kaduwa ban San lokacin da nace
"mu biyu kuma Abba? Ni kadai yake so fa Abba, ba mu taba wannan zancen ba Abba...."
Na fada idanuwa na suna ta yawo akan fuskar Abban yayin da wani malolon Abu ya tsaya min a wuya, yaki ya sauka bare na zuqi numfashi
"Toh wannan bayanin suka zo mana da shi, a wani launi Tamkar na yarjejeniya ma, Dan haka ni da sauran iyayenki muna baki umarnin ki janye kema daga wannan bigiren domin mu tuni muka sauka daga kai kuma mun aika musu su ma. Kiyi hakuri ki dauki hakan a matsayin jarabawa, Allah ya miki zabi mafi alkhairi..... "
Abban ya fada tare da sunkuyar da kan shi dan a tarihin rayuwar shi yayi hira kala kala da mutane, ya tsaya a gaban camera sau ba adadi ya gabatar da labarai kala kala amma babu wata sanarwa daya taba gabatarwa da ta kai wannan nauyi a kirjinsa dakuma bakinshi, bashida wani zabi, he doesn't have any choice than to do this in other to save his most precious being ever.. Yana kaunar Ummin fiye da komai a duniya Dan haka Abu na karshe da zaiyi shine aurar da ita a inda yake jin she isn't the priority.
Ya kuma runtse idonshi yana jin yanda take kunjin kuka ajikin mahaifiyar tata, yana jin yanda take ta cewa a bashi hakuri ya aura mata Fu'ad, yasan zaa rina wai an saci zanin mahaukaciya. Amma akwai sauran magana abakinshi ai, ya lura da yanda Kubra take kallon shi yayinda take rungume da Ummin, kallon shi take tana isar mishi da sako ta Ido, alamun Ka kara sa mata zancen, Ka juye komai a yanzu.
"mamana" naji Abban ya furta, na dago da sauri daga jikin mamin ina fatan Abba tausayi na yaji, na dauka tausaya min yayi yace ya amince da auran.
"Akwai aminina Alhaji Tukur kiyawa nasan kin sanshi, mamana tun kina yar secondary yake rokona Akan na amince mu hada auranku da Babban Dan sa Jaafar. Da farko ina da wannan raayin amma ganin yanda kuka shaqu da Fuad yasa na bashi hakuri kuma ya fahimta, but he always keep reminding me that har abada yana da burin ace Dan sa ya aure Ki, hakanne yasa na aika masa da sakon cewa yanzu na amince duk da amince wa ta ba tana nufin dole nake miki ba, Jaafar zai zo ku fahimci juna... Allah ya zaba maki mafi alkhairi mamana"
Wadannan maganganun Abban na karshe Tamkar kasar da ake diba ake toshe duk wata mashigar iska ko haske a kabari, yanda mutane makusantanka, mahaifi, wa, qani, miji, makoci da duk wani mai qaunarka zai Debi kasa yana danne duk wani waje da ake ganin cewa iska ko haske zasu shiga, a nasu tunanin hakan shine soyayyar da zasu nuna ma.
Na tuna yanda na miqe daka jikin mamin na share hawaye na, nafita daga falon na tafi dakinmu, Idona a bushe babu sauran digon hawaye.... A bushe nake jin zuciya ta Tamkar bata bugawa. I felt so dead, so unexisting.... Dama wannan itace qaddarar tawa da nake kwana ina tashi da tunanin yaya take? Ta ina zata bullo min? Wannan Itace qaddarar da nake ta jin araina cewa akwai wani gagarumin abunda zai faru?
YOU ARE READING
Muhibbi♥️
RomanceA forbidden love! Rayuwa bata cika tafiya kan turbar da bawa yake muradi ba.... Ku biyoni Dan karanta labarin Fu'ad da mardhiyya, ku biyoni dan karanta irin tasu qaddarar. COMPLETED!