*ALHAKI...*
Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabirPage 3.
Likita ya koma kan Batul sai yaga ita suma tayi wanda fargaba ne ya haifar mata da haka, sai ya saka nurses suka kamata suka fitar da ita zuwa falo suka kwantar a kan kujera, sai yasa aka kawo ruwa suka shafa mata a fuska, ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi ta cigaba da yin barci, haka dai suka gama bincekensu likita ya tabbatar da mutuwar Hibba, dan ba ƙaramin lokaci ya ɓata ba akan haka, inspector Bashir yace ya haɗa duk wasu bayanai zai zo ya amsa kuma zai ji alert sai yayi musu godiya kana suka yi sallama suka wuce. Yan sanda suka fito tsakar gida suka fara yiwa Mamam Zeena tambaya, cikin kuka take kore musu bayanin yadda tazo gidan ta same su, ta ɗaura da cewa.
Jiya ma a gidana Hibba ta kwana saboda Zeena tana fama da zazzaɓi tasha magani yasa ta barci da wuri, shine Hibba ta leƙo ta dubata dan har kusan tara da rabi bata ga Zeena ba, shine nace ai ba tada lafiya ta koma ta rufe gidan tazo ta kwana a nan tare damu. Wajen ƙarfe shida na safe tace zata je ta shirya ta wuce makaranta ƙarfe bakwai da rabi saboda tana da exam ƙarfe takwas da rabi na safe, nayi mata fatan alkhairi nace tazo ta ƙarya kafin ta wuce. Tace mini to sai ta wuce, ganin har ƙarfe takwas ta wuce bata zo ba sai nayi tunanin ta wuce ne ƙila bata so ta karya damu, to abinda ya bani mamaki wajen sha biyun rana ina aiki a tsakar gida sai naji ihu daga gidan mai ƙarfi shine na saki aikina na fito danna duba ko wani abun ya samu Hibba, shine na zo na tadda Batul a kwance ga Hibba itama kwance.
Ta ƙarashe maganar da kuka sosai, nan suka gama ɗaukar bayaninta sai suka yi sallama da Bashir akan duk abinda ake ciki na bincike zasu ɗaura zuwa in an gama jana'izar Hibba, a lokacin ne Habib ya shigo gidan, ganin mutane a tsakar gida ga wasu a ƙofar gida dan har mutane sun taru saboda ganin motar 'yan sanda dan su bawa idonsu abinci, ya tsaya yana tambayar Bashir meke faruwa, nan ya koro masa bayanin abunda ya faru harma da binciken likita dana 'yan sandan, dafe kansa yayi jikinsa yana wani irin kakkarwa ya durƙushe a wajen yana salati nan take ya soma kuka ba hawaye wanda tashin hankali ne tsintsa a ciki.
Taya Hibba zata rasu, mun shiga uku diyar amana ce, yanzu da wani ido zan kalli mahaifinsu, Innalillahi wa in a ilaihir raji'un Allahumma ajirnii fee musibati...
Sai ya miƙe zumbur ya ɗauko wayarsa domin ya kira mahaifiyarsa, Umma tana ɗaga kiran ya fashe mata da kuka.
Umma umma anyiwa Hibba fyade an kasheta.
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Me kake faɗa mini haka Habibu? garin ya haka ta faru.?
Umma yanzu nake dawowa daga tafiya ban san komai ba sai bayanin da maƙocina yayi mini yanzu.
Ina Batul?
Gata can a kwance a sume, itama dawowarta ta samu Hibba a wannan halin sai ta yanke jiki ta faɗi.
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, wannan wace irin ƙaddara ce ta faɗo mana, to kayi ƙoƙari ka sanar da mahaifinsu gani nan zuwa yanzu zan kira su Salamatu yanzu na faɗa musu Allah ya jiƙanta ya tona asirin wanda yayi wannan ɗanyen aika aikan.
Cewar umma tana matsar kwallar tashin hankali, Habib ya kashe kiran ssi ya kira Babansu Batul yana ɗauka sai ya daburce ya kasa yi masa magana, sai ya miƙawa Bashir wayar ya amsa, shine ya yiwa Baba bayanin komai a takaice, salati kawai baba ke jerawa yana ambaton sunan Allah, daga karshe yace.
Allah da ya fimu sonta ya amsa abinsa, iyakar abinda ta ɗibo kenan Allah ya jikanta ya gafarta mata, ka sanar da Habib a kawo gawarta nan gidana a sallaceta in yaso sai mu yi zaman makokin duka a nan family house ɗinmu dan a ragewa mutane wahalar zirga zirga.
Bashir ya amsa da to kana ya miƙawa Habib wayar yana yi masa bayanin da Baba yace, sai ya ɗaura da cewa.
Ina ganin ayi mata wanka da sutura anan in yaso sai a tafi da ita can ya zama sallah za a yi a kaita makwancinta dan a rage musu aiki.