*ALHAKI...*
Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabirPage 7.
Batul Bayan ta shiga shagon ta ɗaure gashinta kana ta kwance gyalenta data ɗaura a kugu ta yafa akai, tana shirin ɗaukar tiren murucci Habib ya tare da cewa.
Nawa ne gaba ɗaya muruccin daya rage?
Ta sanar da shi na ɗari takwas da hamsin ya rage, sai yace ya siya gabaɗaya ta rabawa yaran shagonsa, ba musu ta bisu ɗaya bayan ɗaya ta basu saura biyu da ya rage sai ya amsa kana ya biyata kuɗinta, sai a lokacin tayi masa godiya har ta ɗan saki fuskarta, ta fito ta wuce abinta a nutse kamar ba yanzu ta gama rikici ba. Habib kamar ya bita amma saboda yadda ya ganta ba cikakken tarbiyya zata iya yi masa rashin kunya, sai ya danne abinda yake ji a ransa yana ganin sam bata dace da irin matar aurensa ba, amma da yake shi so hana ganin laifi ne yakan shiga mutum ta inda bai kamata ba, duk yadda yaso ya yakice tunaninta ya kasa haka ya yini a ranar zuciyarta tana ƙara azalzala masa soyayyar Batul da ko sunanta bai sani, har alla alla yake washe gari yayi ko zata ƙara zuwa talle wajen shagonsa, duk da yana fargaban da wuya tazo tunda bata kwashe da mutanen wancen shagon lafiya ba.
***
Bayan mako guda
Batul bata kuma shiga tudun wada yin talla ba, Habib yana ta zuba ido amma bata ba labarinta, tabbas yasan ya gama kamuwa da soyayyarta yana jin in har bai sameta ba zai iya samun tangarɗa a rayuwarsa, hakan yasa shi Addu'ar Allah ya ƙara haɗasu. Batul a ranar ta shiga kasuwar bacci yin siyayyar kayan gwanjo, irin riguna da wando na mata da kayan pakistan saboda tana so ta ƙara yawan kayanta da kuma samun kayan da zata cigaba da birge samarinta, Habib shi kuma ya shiga kasuwar siyayyan kayan ɗinki har hakan ya fito da shi bakin hanya yana niman wani landin, kamar ance ya kalli can gefen titi wajen 'yan gwanjo sai ya hangota tana ɗaga wata riga, da sauri ya bar shagon daya tsaya ya tsallaka titin ya isa inda take tsaye, ya tsaya a bayanta tare da yi mata sallama a hankali wanda ita kaɗai taji, da sauri ta juyo tana kallonsa suna haɗa ido ya sakar mata murmushi, itama ta sakar masa domin ta gane shi, sai yace mata.
Kin daina tallar muruccin ne tun wancen ranar ko kuma kin daina kawowa ta arean shagona ne?
Tun ranar ban sake zuwa tudun wada ba sai yau dana zo siyan kaya, can unguwarmu nake talla zuwa cikin gari.
Kin yi fushi damu kenan?
Gaskiya abinda TJ ya mini ya bata min rai shiyasa ban sake zuwa ba.
To ayi haƙuri, yanzu yau ba tallar kenan tunda na ganki a nan.
Haba me za a fasa, ai sai da na siyar da kayana kafin na zo nan na siym abinda nake so na wuce gida, ga tiren can na bada ajiya.
Habib ya gyada kai yana jin ba zai taɓa bari wannan damar ta wuceshi ba dole ne yayi ƙoƙarin kafa gomnatinsa, dan haka ya nisa yace.
To ki jirani yanzu na kai kaya shago na ɗauke mashin ɗina na kai ki gida, amma Allah yasa banyi laifi ba dana buƙaci haka.
Batul ta washe baki ganin ta samu banza yau ba kashe kuɗin moto, tace.
Ba laifin da kayi ni da zaka taimaka, aiko zan jiraka, je ka dawo ina nan.
To yace mata yana mata murmushi sai ya tari napep ya shiga dan yana buƙatar yayi sauri ya dawo baya so ya ɓata lokaci, Batul ta gama siyan kayanta da zaba ta biya kuɗin aka zuba mata a leda ta koma gefe ta ɗau tirenta data bayar ajiya ta tsaya jiran Habib. Bai daɗe sosai ba sai gashi ya dawo a mashin ɗinsa tana ganin ya tsaya ta zo ta hau bayansa suka wuce. Ba wani hira suka yi ba har suka isa rigasa da kwatancen da take yi masa, ya sauketa a ƙofar gida yana cewa.