*ALHAKI...*
Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabirPage 8.
Ko da Habib ya isa asibitin an sallamesu, biyan kuɗi ya rage musu dan haka yayi sauri ya biya kuɗin kana ya dawo ɗakin ya ce su fito su wuce, napep ya tare musu har zuwa ƙofar gidansu Batul, shi kuma ya hau mashin ɗinsa, bai samu damar yin magana da Batul ba saboda mutane ba wajen keɓewa, sai dai ya samu bayani a bakin su Aliya kan abinda ke damunta shiyasa ma bai damu sosai ba, sallama yayi da ita akan sai ya dawo washe gari addu'ar Uku, kana ya wuce gidan umma da tun ɗazu suka wuce.
Yana shiga gidan ya same su zaune a tsakar gida suna shan rake ƙannensa duk basu tafi gidansu ba, ya samu ƙaramar kujera ta mata ya zauna yana gaida Umma suma ƙannen suka gaisheshi tare da sake yi masa gaisuwa, ya amsa yana duban umma yace.
Umma kan batun auren Saratu na amince, domin nayi zurfin tunani naga gata kike son yi mini dan haka ina so ayi auren nan a cikin kwanakin nan kan Batul ta dawo gida, saboda nasan in ta tadda an ɗaura dole zata yi haƙuri ta karɓi ƙaddara.
Kai Alhamdulillahi naji daɗin wannan bayani, yadda ka faranta mini Allah ya faranta maka kaima ya baka yaran da zasu yi maka biyayya. Amma baka gani anyi gaggawa a ɗaura a yanzu ina ganin gwara mu bari maganar rasuwar Hibba ta kwaranye sai a yi.
Cewar Umma, Salamatu ta katseta da cewa.
Haba umma ai da zafi zafi ake dukan ƙarfe kuma a bari ya huce shike kawo rabon wani, wannan damar da muka samu ya amince gwara ayi auren kafin yazo ya sauya shawara.
Nima dai Umma na yarda a ɗaura in ta Batul ne ba zamu samu wata matsala ba saboda akwai fahimta a tsakaninmu.
Cewar Habib, Aliya ta kaɗe baki tace.
To ma wani gardama zata yi matar daka tsamo daga cikin ƙangin talauci ka rayata ta zama mutum, a da ban da Talla ai ba abinda ta sani, ina ce yanzu duk kayan ɗakinta kaine ka sake yi mata su, wani gata ne baka bawa Batul ba, sannan shekara huɗu ba haihuwa ai kayi mata halacci in kuma tace zata yi bore kanta za ta yiwa mugunta.
Ke Aliya bana son rashin mutunci duk lalacewar Batul ina sonta, kuma ba wai zan ƙara aure dan bana sonta bane, zan yi ne domin na yiwa Umma biyayya kar na sake jin kin aibata matata tom.
Cewar Habib cikin ɗaure fuska, Umma ma nan take ta tsawarar musu daga bisani suka ɗaura da hirar yadda za a yi bikin tunda abu yazo cikin sauri. Lawisa tace cikin damuwa.
Umma gaugawa aikin shaiɗan ne, dan Allah abar batun auren nan zuwa nan da wani lokaci, gani nake in aka yi yanzu kamar an ci amanar Batul.
Dalla uwar kanzagi ki mana shuru dama ke ba a abun arziki da ke, to sai ki hana ayi auren, ni bana son munafurci ina ce dake muke zancen rashin haihuwar Batul ɗin.
Cewar Aliya, umma ta ce.
Bana son haka Aliya, wai ke ba a taɓa zama waje ɗaya dake ba ayi rikici ba girma kike yi amma kamar kina cin ƙasa, ki daina yin magana cikin kausasa harshe in ba haka ba wlh watarana bakinki shi ne zai yanka miki wuya.
Aliya ta zumɓuro baki domin tasan ita duk abinda tayi laifine, sai ta miƙe tana cewa.
Ummm to ni bari na wuce gida kawai tunsa naga ni komai nayi laifi ne. Yaya dan Allah rage mini hanya ka kai ni gida, kuɗin motar dake hannuna ba zai kai ni ba.
Sai dai na baki ɗari biyar ki wuce, kuma ki rage wannan baƙar zuciyar ba dama ayi miki faɗa sai ki fara fushi kamar kububuwa.
Cewar Habib yana miƙa mata ɗari biyar daya ciro a aljuhunta, ta amsa tana godiya kana tayi sallama da su ta wuce, ba jimawa Salamatu da Lawisa suka tafi kuma Habib sai da ya basu suma dari biyar biyar, sai wajen magrib ya bar gidan ya wuce shagonsa. A lokacin ne Umma ta samu damar kiran Hajiya Uwa ta shaida mata amincewar da Habib yayi, ba ƙaramin farin ciki tayi ba tace sai ayi bikin nan da sati biyu ko uku, tunda aure ne na zumunci kuma bazawara ce ba sai an ɗauki lokaci ana shiri ba, umma ta amince da bayaninta kana suka yi sallama.