*ALHAKI...*
Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabirPage 10.
Gidan Namir.
da sassafe Amira ta tashi ta haɗa musu abun breakfast, ta soya musu doya da kwai ta zuba a food dish kana tayi souce ɗin albasa ta saka soyayyen manan ragon jiya a ciki ta juye a mazubi ta kai dinning ta jerasu kana ta dafa ruwan lipton da kayan ƙamshi ta saka a flakes, sai ta ɗumama sauran shinkafar jiya dan da shi take so ta karya ta shirya komai a dinning sai ta koma ɗaki ta watsa ruwa ta sanya doguwar jallabiya baƙa ta ɗaura dan kwalin, sai ta tashi Haneefa daga barci tace ta shiga bayi tayi wanka ta haɗa mata ruwa, in ta gama ta fito su karya sai ta fita zuwa ɗakin da su Anas suka kwana, ta kwankwasa Anas ya buɗe ta ganshi shima yayi wanka ya sauya kaya ta gaishe shi kana tace su fito su karya, to yace mata kana ta juya ta nufi falo ta zauna a cushing tana jiransu, ta kunna tv tana kallo sai taji takun takalmin Safeena tana saukowa daga step ta waiga tana kallonta, Atamfa ce ta sanya riga da siket ɗinkin sun matseta dan straight siket ne kuma anyi masa tsagu har zuwa ƙaurinta, sai rigar aka yi shi fited sama ya kama boob ɗinta sun fito ƙasan rigar kuma ta buɗe anyi mata hannun donot, dan kwalin ta ɗaura shi irin ɗaurin nan da ake kalmashe shi a fito da goshi tsakayar kai kuma a buɗe, sai jaka da takalmi iri ɗaya tana riƙe da key a hannunta ƙamshinta nan da nan ya cika falon, Amira sai da taga ta sauko ta nufota tayi saurin kawar da kai tana jin wani faɗuwar gaba dan abinda ta yiwa Namir jiya ya saka mata tsoronta sosai, dan ta kula sam ba tada mutunci. Safeena tana ƙarasowa ta tsaya a tsakiyar falon Amira cikin sauri tace.
Anty ina kwana.
Lafiya. Ni zan fita zan barku da yayanku sai gobe In Sha Allah zan dawo.
To Adawo lafiya.
Sai dai bana san rawar kai ki gayawa 'yan uwanki ban da ɓarna bana so na dawo na tadda gidana ba yadda yake ba.
In Sha Allah zamu kiyaye.
Cewar Amira, a lokacin ne Namir ya sauke yana binsu da kallo Safeena tana ganinsa ta kaɗa kai ta nufi fita daga falon, sai ya bi bayanta da sauri suka fita tare, sai da suka isa wajen motarta ta tsaya tana buɗewa Namir ya ce cikin damuwa.
Safeena yanzu kin gwammace kibar gidan nan akan dalilin da bai taka kara ya karya ba, bama wannan ba kina nufin a haka zaki fita ko gyale baki ɗauka ba.
Yau na saba fita da shiga irin wannam? Namir ya kake niman sauyawa ne lokaci guda, to haka nayi niyyar fita. Kuma maganar abinda ya faru jiya ai na gama magana akansa bana son mayar da hannun agogo baya.
Hmmm to Allah ya baki haƙuri na kula haushina kike ji har yanzu, to yanzu gidan zaki wuce kenan?
Eh amma sai na biya super market na yiwa Abdul siyayya.
Ok amma da kin jira na shirya sai mufita tare na sauke ki a gidan na duba Abdul ɗin, in yaso in zaki dawo sai ki kirani nazo na ɗauke ki.
Ba zan iya jira ba kuma ko yaushe zaka iya zuwa ba lallai sai yau ba, ni zan wuce bana son na ɓata lokaci.
Ok ki gaida su momy sai na shigo.
To ta ce masa kana ta buɗe motar ta shiga ta zauna, akan idonsa ta kunna motar ta cillata ta bar gidan dama mai gadi tuni ya buɗe mata gate dan kar yayi laifi, sauke ajiyar zuciya Namir yayi ya koma ciki, ya same su gabaɗaya sun fito suka gaisheshi kana suka nufi dinning har da shi suka karya hankali kwance, sai dai Namir zuciyarsa baya cikin sukuni na fargaban zafin kishin Safeena, damuwarsa in tasan maganar aurensa komai ma zai iya faruwa, amma har cikin ransa yaji daɗin tafiya gidansu da tayi saboda zai samu damar sakewa da Amira suyi maganar aurensu ba tare da fargaban komai ba.