⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Arewabooks @18saikaska
_________________________________
*Proud of my first novel*★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★
*Wannan babin naki ne Habeebty*
*BABI NA GOMA SHA SHIDA(16)*
UCHENNA POV.
Yau kwanan sa uku da fara aiki a HANAM FASHION HOUSE, kuma aiki a wajen na masa daɗi, shi da Hanam suke zana ɗinkin da za'ayi, amma kullum tana faɗin nasa yafi kyau, kuma a kullum zeyi ɗinki cikin yabawa take.
Amma kuma ya lura da wasu sabbabin ɗabi'u da take da su, bata sakarwa kowa fuska, duk da dama can haka take, amma kuma na yanxu yafi na da ɗin, kuma a yanda ya lura bata da aure, hakan yasa ya tambayi wani Aminu a wurin, wanda yake kawo masa kayan aiki idan ya buƙata.
Kuma Aminu ya faɗa masa cewa, suma haka suka ganta da ɗan, daga tafiya USA na shekara biyu sai gata ta dawo da wa, kuma har yau iƙirari take kan cewar itace uban ɗan, abun yaso ya ɗaure masa kai, dan haka yayi niyyar tambayar Abba.
Yana zaune a office ɗin da aka bashi domin ɗinki, bayan ya gama dinka wata riga sai ya ɗauki break yana shan coffee, kawai sai yace bari ya kira Abba ya tambayeshi, tunda basa samu su hadu.
“Abbana”
Cewar Uche bayan Abba ya ɗaga kiran kuma sun gaisa.
“Na'am ɗana”
“Tambayarka na ke sanyi”
Ya faɗi yana kallon windown daya buɗe, hannunsa na dama rike da mug.
“Faɗi ɗan Abbansa, ina jinka”
“Abba.....”
Sai kuma yayi shiru, shi sam bai iya ƙunbiya-ƙunbiya ba, idan yana so ya faɗi abu kansa tsaye ya ke faɗarsa, amma yanzu sai ya ji nauyin Abban, sai ya tattaro ƙarfinsa ya furta abinda zai zama sanadiyyar sauyawar ƙaddararsa.
“Abba ni Hanam ta tab'a aure ne ?”
Abba beyi mamakin tambayar ba, dan tun a ranar da Uche ya fara zuwa HANAM FASHION HOUSE ɗin ya faɗa masa cewa ai ya sana Hanam sun tab'a yin aji ɗaya a secondary.
“A'a haris, bata tab'a aure ba”
Uche yayi wata b'oyayyar ajiyar zuciya, amma duk da haka saida Abba ya ji, Abba yayi murmushi
“Haris”
“Na'am Abba”
“Next week zanje hakuɗau, kuma tare nake so muje”
Hakuɗau shine mahaifar Alhaji Muhammad.
“Zuwa lokacin na gama aiki a nan, ba matsala zamu iya zuwa”
“Eh nasan zuwa lokacin ka gamawa Hanam aikinta, kawai na faɗa maka ne dan ka shirya”
“To Abbana, Allah ya kaimu”
“Ameen ɗan albarka na”
Kuma daga haka wayar ta ƙare, Uche ya aje mug ɗin hannunsa akan wani table, sannan ya dawo ya ɗauki measuring tape, ya shiga auna wani yadi, zuciyarsa fal tunane-tunane iri-iri.
Kuka yaji, kuma yasan cewa babu me kukan bayan Arya, dan ɗakin da ake renonsa kusa da office ɗin sa ne, Allah ya sani tun daga ranar da yaron ya riƙe ƙafarsa ya shiga ransa, dan haka da sauri ya aje yadin da measuring tape ɗin duka ya fice da sauri ya faɗa ɗakin.
Ya iske Naani ɗin nasa ta na rarrashinsa shi kuma sai kuka yake, gaba ɗaya ya rikita Naani ɗin nasa.
“Kinga kawo shi”
Ya faɗi yana miƙa mata hannu, miƙa masa shi tayi, shi kuma ya karb'eshi ya fice daga ɗakin.
Office ɗin nasa ya koma da shi, ya shiga rarrashinsa, amma yaƙi shiru, sai kawai Uche ya ɗauki wani zanin atamfa daya yanka ya goyeshi, yana jijjiga shi.
Tunda Aryaan yazo duniya ba'a tab'a masa goyo irin wannan ba, dan Hanam bata goyonsa saide ta sakashi a baby carrier, nan da nan yayi bacci.
Hanam taji kukan Arya hakan yasa itama ta fito domin taga abinda yake faruwa, sai Naani ɗin ta faɗa mata cewar ai wannan na ɗayan office ɗin yazo ya karb'eshi, dan haka Hanam ta fita, ta shiga office ɗin Uche.
Samunsa tayi yana kai kawo da Aryaan ɗin a bayansa, kuma gashi ya goye shi, wani abu ya motsa a kirjinta, wanda rabonsa da ya motsa tun shekaru biyu baya, sai ta kawar da tunanin, dan a ganinta abun ba meyiwuwa bane, ita sai abun ma yaso ya bata dariya, namiji da goyo, kuma ya iya goyon ko dan igbo ne oho.
“Yanzu Uche da atamfar dubbunan kuɗin ka goyi yaro ?”
Ta faɗi tana shigowa ciki, shi sam ma bai kalleta ba.
“Me zai hana idan de boy ze yi shiru, idan yana kuka bazan iya aiki cikin kwanciyar hankali ba”
Hanam taji wanna abun yaci gaba da motsawa, kuma wannan irin wanda tavjine lokacin da ta haifi Arya ɗin.
“Naga ya yi bacci kawo shi, kar ya hanaka aiki”
“Ba dole yayi bacci ba, yaji goyo, nasan yanzu haka ba goyonsa kike ba”
Ya faɗi yana ƙoƙarin since zanin goyon.
“Na miye zan wani zo ina goyonsa, ai baby carrier ɗin shine dai-dai shi”
Ta faɗi a lokacin da ya miƙa mata shi, daga haka kuma ta fice daga wajen, Uchenna yabisu da kallo su duka, yana murmushi ya dawo yaci gaba da aikinsa.
YOU ARE READING
YADDA KADDARA TA SO
RomanceA wasu lokutan kaddara na faruwa ne a yadda ta so, a wasu lokutan kuma takan faru ne a yadda dan adam yaso, kamar kullum Allah na nasa dan adam ma na nasa, amma na Allah shine gaskiya.