*_KWANKWASON JIMINA!!_*
_(MAI WUYAR SHAFAWA)_
🦩🦯🦾_NA_
_NANA HAFSATU_
_MX_*_ZAFAFA BIYAR 2024_*
*_arewabooks:mssxoxo_*
*_Free page :02_*
__
"Ba kiji ciwo ba ai ko?... Ki dai na tsalle tsalle Amna.." Ta karasa fada tana mai tambayar ta da hannu alamar menene?
Amna ta bude dan karamin bakin ta tana furta sunan yafendo a hankali. Ai kuwa bata karasa rufe bakin nata ba yafendo ta karasa dakin tana dogara yar sandar ta.
"Ah yafendo..." Cewar Nawra tana mai danne gefen katitar data zura littafin ta zauna akai.
"Amna tace baki da lafiya ko?"
Nawra ta kakaro murmushi tana kada kanta.
"Da sauki amma.."
"Tun dazu nake cewa kina ina ne duk su Layla suna nan.. Bake kwata kwata. Kwanakin nan na rasa gane kan ki. Na tambayi mahaifiyar ta ki tace zata miki magana. Sai Amna ce danasa Adam ya kirawo ki tace ai baki da lafiya "
Nawra dai kanta a kasa tana lankwasa yatsunta. Tace,
"Uhum... Amman da sauki ai. Nagode sosai"
"Sannu kinji?. Allah ya baki lafiya Nawrah. Kwanta ki huta"
"Tohm yafendo.. "
Nawra ta haye Kan katitar sosai ta kwanta tana mitsitsika idanu..Yafendo ta mike dakyar tana dafe bango ta fice daga dakin
Nawra ta sauke katuwar bahaguwar zuciya ganin yafendo ta fita. Tadaga gefen katitar da saurin gaske ta zaro littafin, ta bankada kasan akwatin ta ta saka.
Amna na gefe tana kallon ta. Nawra ta riko hannun kanwar tata tace,
"Nagode sosai Amna tah.. Yau da yafendo taga Ina rubutun nan ai sai an kusa yankani. " Ta karasa fada tana kada Kai.
Amnah tayi murmushi kawai. Tana Wasa da zaren jikin rigar ta.
"Ungo biyar dinnan na baki jeki sayi wani abun"
"Nagode" Amna ta karba cike da farin ciki ta fice da sauri.
Nawra ta kwanta akan katifar ta ta lumshe idanun ta.... Fuskar ta ta gauraye da murmushi. A zuciya take karantowa. idanuwan ta na hasaso mata rubutun haruffan da zanen su. Ya yinda labbanta ke matsowa ahankali tana karanta su...
"Nawra.... Nawra .... Nawra" Layla ta kwada mata kira. Ta shiga dakin nasu.
Nawra ta mike da sauri tana duban ta tace,
"Kai Kib katse ni wallahi"
"Dalla aiken mu akayi..."
"Ina aka aike mu ?"
"Gidan bappah Auwalu."
"Tam. Bari nasaka hijabi"
"Dalla muje a haka kaman wasu manya zamu saka hijabi?" Cewar Layla ta fada tana yiwa Nawra nuni da kanta.
Nawra ta girgiza kai tache,
"Zan saka.. Ammi tace da hakan ake dorewa har girma. "
"Shikenan sai ki saka ai"
Nawra ta girgiza kai. Ta bude wardrobe din kayan su ta dakko hijabin ta ta zura... tana duban kanta a wani madubin su karami dake jikin dressing mirror dinsu..
Tsaf da ita kamar wata babbar budurwa ta dubi Layla dake nannade kasan zaren hannun rigar ta tace,
"Muje"
YOU ARE READING
KWANKWASON JIMINA!! (MAI WUYAR SHAFAWA) ..PAID NOVEL..
General FictionLabari Mai tsuma zuciya...🦋🤍 #Destined lovers #Life partners #Rich vs poor #The battle of................... KWANKWASON JIMINA (MAI WUYAR SHAFAWA) BOOK 1 & 2