FREE PAGE 4

109 1 0
                                    

*_KWANKWASON JIMINA!!_*
   _(MAI WUYAR SHAFAWA)_
          🦩🦯🦾

_NA_

_NANA HAFSATU_
    _MX_

*_ZAFAFA BIYAR 2024_*

*_arewabooks:mssxoxo_*

    *_Free page :04_*

____
  *HAMIDNIYYA LEBANON*

   Hamidniyya Lebanon wata zuri'ah ce mai karfi dake shiyar sansanin yankin bunza. Yankin bunza na dauke da yarika kala kala. Mafi yawa acikin su Fulani ne, Fulani dai kabila ce da tarihi ke turke asalinta tun karni na 15 daga wasu manyan yankuna biyu da ke kasashen Senegal da kuma Guinea Conakry, wato Futa Toro da kuma Futa Jalloh... Sai mafi karfin ciki wato wadanda sukafi tarin dukiya zuri'ar hamidniyya ne wadanda usulin usulin su larabawa ne yan kasar Lebanon..

Daga su sai barebari, Yarabawa, Idoma, Igbira da sauran su. Kusan dukkanin wasu yarirrika dake kunshe cikin kasar akwai su a yankin garin na bunza..

**ASALIN SU**

   Tarihi yazo da cewa usulin zuriyar hamidniyya yan kasar Lebanon ne, Lebanon kuma kasa ce a Western Asia..

Tarihi ya nuna cewa Marigayi Hamidniyyah Mohannad Lebanon Wanda sunan sa ne zuriyar ta samu asali. Ance sunzo kasar ne yin wani bincike. Jiragen da suka zo da su suna da dan yawa. Dan haka sansanin inda ake ajiyar jirgin sai a ka samu ibtila'in gobara jiragen duk suka kone... Sai jirgin su Marigayi Hamidniyyah Mohannad wanda shi Marigayi da cikin daga cikin manyan kasa alokacin sun fita yawon bude idanu a gajimare da jirgin daga nan suka biya wata kasar..

Labarin gobarar jiragen ya koma kunnuwan can kasar inda sukayi koke koken su. Ance dukkanin jiragen sun kone da Mutanen su dake ciki. Baa banbance gawa da karfen jirgin aka tarkata aka wanke aka sallace su a haka aka birne...

Ko da ragowar jirgi daya ya dawo wato nasu Marigayi Hamidniyyah Mohannad. Sai suka samu mummunan labarin abunda ya faru..Gashi babban lefi ne ya koma kasar su shi da sauran wadanda basu rasun ba. Su ce dalilin daya faru sun bar kasar hakan ta faru to akan me zasu tafi yawon bude idanu su bar sauran mutanen su da aiyukan da aka turo su suyi? Wannan dalilin ne yasa suka yanke zama anan kawai. Domin idan suka koma kasar su ma hukuncin kisa ne za'ayi musu.

Anan suka kafa sansanin su suka auri junan su.. su da fulanin wajen suka zama mutane daya...Suna daya daga cikin manyan kabilun da suka taimaka wajen sama wa kasar 'yanci daga turawan mulkin mallaka.

Baya ga zaratan sojoji na Fulani da suka yi gwagwarmaya, akwai kuma fitattu da suka taimaka wajen sama wa kasar 'yanci.

Daga nan ne suka ci gaba da bazuwa cikin kasashen duniya musamman yammaci da kuma tsakiyar nahiyar Afirka domin nema wa dabbobinsu abinci da kuma ingantacciyar rayuwa.

Ko da yake babu tsayayyen adadi na yawan Fulani a duniya, amma kiyasi na nuna yawansu ya kai akalla miliyan 45, kuma sun fi yawa ne a kasashen yammacin nahiyar..

Kamar yadda Fulanin ke da masarautu da dama haka ma kuma suke da karin harshe kala-kala wanda masana tarihi suka kasa kashi shida.
Wannan ne ma ya sa ba lallai ne wasu Fulanin Najeriya su fahimci fulatancin wasu 'yan uwansu da ke kasashe kamar Senegal da Gambiya ko kuma Burkina Faso ba. Ko da a Najeriya, akwai wani karin harshe da wasu Fulanin ba su fahimtarsa.

Akwai aminta sosai tsakanin fulanin yankin bunza da zuriyar Hamidniyya Lebanon.. Tun shekarun baya ya zuwa yanzu. Kuma Allah ya sanya musu wata albarka ta tarin dukiya. Basu da wani yawa. Dan sun rarrasu da yawan su. Sai 'ya'yan 'ya'yayan su da sukayi aure sika hayayyafa suma suka tada tasu zuri'ar amman duk da haka basu da wani tarin yawa sai tarin dukiya .

KWANKWASON JIMINA!! (MAI WUYAR SHAFAWA) ..PAID NOVEL..Where stories live. Discover now