CHAPTER 12

150 10 0
                                    

Kun ji ni shiru kwana biyu sakamakon rashin da muka yi. Amman Alhamdulillahi ala kulli halin.

______________________

Ta dade shiru bata ce komai ba kamar bata jikin wayar har sai da ya dauke wayar daga kunnesa ya duba ya sake mayarwa.

"Safaeena ina tunanin saboda kina da magana da ni ne kika kira ni"

Cikin muryar kuka ta soma magana.

"Ka canja min Kareem, daga lokacin da ka hadu da mahaukaciyar yarinyar nan gaba daya hankalinka ya tashi daga gareni ya koma gareta, yau har ta kai ta daga wayarka ka fada min magana son ranta, Wallahi da ban yi kokarin rike kaina ba da Allah kadao ya san abun da zan aikata a yau din nan kuma Allah ya san halin da zan shiga"

Ya sauko daga matakalal dake gurin yana rike da wayar a kunnensa.

"Ina kokarin shata liyi ne a tsakaninmu, akwai abubuwan da idan suka yi yawa, rashin tunani yana shiga ciki ya zauna, kamar yadda yake kike tunanin son haihuwa da ni yayinda kike da aure da wani, abun da kika yi niyar aikatawa ya tsorata ni, kuma ya bani mamaki, sannan ya farkar da ni daga dogon bachin da nake"

"Baka ji tsoro ba? Lokacin da na ce maka cikina ya zube saboda kishinka? Baka yi tunanin zan iya shiga damuwa idan ka guje min ba, Kareem a can baya ma da muka yi soyayya kawai da na rasa ka sai da na rasa mijin aure saboda na kusa haukacewa, aka rasa namijin da zai aureni sai Abdull, balle kuma yanzu da na riga na san ka farin sani ka tsara jikina ta yadda bana jindadin mu'alama da miji sai da kai, ka san duk yadda zaka yi ka kawar min da kishina ka faranta zuciyata, Kareem saboda ina sonka ne ya saka nake son na haihu da kai, saboda ina da mafarkin da nake son ya tabbata a nan gaba, Wallahi ina sonka Kareem na sabu da kai, idan ka sake guje min a karo na biyu ba zan hakura ba..."

Wani dogon numfashi ya sauke ya juya ya kalli kofar da ya fito sannan ya ce.

"Safeena na san kina so na, ni ma ina sonki amman Allah be kaddara mu zama ma'aurata ba, be kamata mu yi ma yaran mu haka ba, be kamata ke ma ci amanar mijinki ba, ya kamata mu karbi kaddarar mana ko dan karin imaninmu da yafiya daga zunubanmu"

Yana jin lokacin da taja majina tukuna ta amsa.

"Mun karba, shiyasa kake auren wata macen ni kuma nake auren wani namijin da ba kai ba Kareem"

"Idan har zamu cigaba da aikata abun da muke aikatawa kazantar ta yi yawa abun yayi muni, kuma hakan yana nufin ba mu karbi kaddarar ba Safeena"

Ta yi dariya da zai iya ji.

"Ba akan mu farau ba Kareem, kuma shi Allah mai yafiya ne a koda yaushe, ba haka za mu dauwama ba, wasu ma suna matsayin budurwa da saurayi suke yi balle mu da muke da aure, wannan abun duk kauna ce ta kawo, karka bari yarinyar nan ta canja min kai"

"Babu ruwan Noor a alakata da ke, ni ba soyayya nake da ita ba, kawai dai an yi sara ne akan gaba ne, amman ba aurenta zan yi ba"

Fashe masa ta yi da kuka.

"Kana cewa mu rabu kamar abu ne mai sauki Kareem, kana kokarin juya min baya bayan kuma na saba da komai na ka, taya kake son na jidadin rayuwa babu kai a kusa da ni? Wallahi saboda kai bana sha'awar Mijinta yayi sati daya a garin nan, saboda kai bana jindadin duk wata mu'alama da mijina, kullum mafarkina da burina akanka ne Kareem, ka juya min baya a lokacin da na fi bukatarka, yanzu kuma mun sabu da juna kake kokarin guje min a karo na biyu? Ko ka manta wacece Safeena a gurinka Kareem....?"

Tif... Ya kashe wayar ya sauke ajiyar zuciya, jin kamar kalamta na kokarin saukar masa da tausayinta kuma suna kokarin kusanto da rauninsa.

"Me na jefa kaina a ciki? Me yasa na bari zuciyata ta yi nesa? Ba zan sake aikatawa ba, ba zan sake ba, ba zan sake cutar da wani ba, ba zan sake bari zuciyata da yaudari da jindadin da ba zai tabbata ba a gareni"

TA ƘI ZAMAN AURE...Where stories live. Discover now