Chapter 14

253 19 1
                                    

“Kasan halinta ai da shirme da ma dai baka bata wayar ba”

Mama ta fada sai ya juya ya kalleta.

“Na dauka magana zata yi masa ta hankali amman meye na fada masa magana haka gatsai, babban mutum ne fa Mama kawai yana da saukin kai ne shiyasa Noor ta same a ruwan sanyi”

“Yanzu aikin gama ai ya gama, sai a tari gaba, ka je ka bashi hakuri kace baka sani ba ta dauki wayarka ta kira shi”

“Haka zan yi”

Ya juya ya fita Mama ta bi bayansa ni kuma na zauna ina ta aikin kuka. Yadda na kwana banci ba haka na wuni haka wani daren ya sake tararda ni na kasa cin komai sai ruwa kawai nake iya sha...
A daren ma sai na kasa bachi saboda tunanin Zafeer ko ya dawo ko kuma yana can, a wane hali yake a can? Wace kalar azaba suke gana masa? Me zai saka ma su kama shi? Na ji yayi abun da be dace ba amman ai taba shi aka yi domin be taba zuwa haka nan kawai ya ci mutuncin Kareem ko ya masa wani abun ba sai yanzu.

Mama ce ta shigo har cikin damunmu a lokacin da Hana take shirin makarantar Islamiya kasancewar yau assabar ba kamar sauran ranakun da take zuwa makarantar boko ba. Ta zauna kusa da ni ta aje min kunun.

“Noor daure ki sha idan kika ce zaki saka damuwa a ranki zata wahalar da ke, kuma ita kaddara ba a kauce mata komai wayon mutum, idan Allah ya kaddara Zafeer mijinki ne zai aureki babu wadda ya isaya hana, idan kuma Allah yayi shi ne mijin ba ko an taru an hadu za a daura muku aure ba zai dauru ba, kalli yadda kika rame cikin kwana daya da rabi, kin koma kamar ba ke ba, ki yi hakuri kinji ƴata”

Ta kwanto da ni jikinta sai na ji sanyi a raina na lallabar da ta yi min da kuma kokarin kwantar min da hankali. Na bude bakin a hankali ta fara ba ni kunun ina sha har na sha rabin kofin sannan na ji na koshi.

“Na koshi Mama”

Hana ta kalli kunun ta kalleni.

“Lallai na yarda kina son Zafeer kalli yadda kika natsu kika koma kamar ba ke ba, kuma yadda kike fushi ko kuka baki rabuwa da abinci amman yau dubi yadda kika ki cin abinci”

Na kalleta kawai na dauke kai domin ni kadai na san yadda nake ji a raina ni kadai na san halin rayuwar da bake ciki

“Ni ma dai na yi mamakin yadda noor ta natsu kamar ba ita ba”

Mama ta fada kamin ta yunkura ta tashi tsaye ta dauke kunun ta fice daga dakin. Hana kuma ta gama shirinta ta kama hanyar makaranta, aka bar ni a dakin ni kadai ina jin jikina babu karfi tunani ne ko kuma dai yunwar da bana ji ce take karya garkuwar jikina. Ina daga kwance na ji sallamar kawata Zainab, na tabbatar a lokacin Mama bachi take domin ban ji ta amsa mata ba, wata kila kuma tana bandakin ne ko kuma ta fita ba tare da na sani ba. Cikin dakinmu ta shigo ganinta ya saka na tashi zaune domin na san ba zan rasa labarin Zafeer a bakinta ba.

“Noor amman dai baki da lafiya ko?”

Na daga mata kai.

“Me yake damunki?”

“Ni ma ban sani ba”

Ta yi shiru tana kallona kamin ta kawar da kai ta ce.

“Wata magana na ji ana ta yi Noor, ko da yake dai ba zan boye miki komai ba gaskiya Zafeer ma ya fada min kuma ya aiko ni gurinki na kawo miki wannan takardar, amman ina son na san me ya hada ku Noor?”

“Ba abin da ya hada mu, me kika ji?”

“Baki ji an kama Zafeer ba? Jiya misalin sha daya na dare ya dawo gida, kuma kamin a kama shi ina ta jin magana sama sama cewar ke da mahaifinki kun bi kudi wai ana son a aura miki wani ba Zafeer ba, ance har da gida ya siyawa Babanki kuma yana kawo muku kayan dadi a gida”

TA ƘI ZAMAN AURE...Where stories live. Discover now