🌠Zuciyar Tauraro🌠(Adams story).
By Bilkisu Muh'd
40: Family
" Family means no one gets left behind or forgotten"
Sama sama suka gaisa, Fariha ta dan sake daga farko saida ta lura Kiara batayi tunanin ganinta ta kame a gaban seat ba lokacin neh yanayinta ya kara canzawa ta daure fuska dan dama ba fara'a a fuskarta koda ta hango su suna karasowa.
Can ba tsammani Kiara ta jefo mata tambaya "How far along are you Fariha?"
Fariha ta danyi ammmm kafin tace 7th months
uhmm Kiara tayi tana jin jina kai.
Ta mirror Adams ya saci kallon Kiara dan yaga yanayin fuskarta, dama ita ba meh iya boye feelings dinta bace.
"where do you intend to stay?" ya kalleta ta mirror bayan ya yi tambayar.
"Kaman ya? where else?" Fariha ta daga gira sama, murmushi na bayyana a fuskarta. A kaikaice ta kalli fuskarsa taga yana cizon leben shi na kasa.
Suna isa kofar gda ta fito daga motar, shi ya fara fitowa kafin Kiara wacce ta jira saida ya bude mata kofa. "zan bi ta baya"
ya hade fuska "saboda meh?"
"Inyi abinda na so yi kafin ka jani na fita" be gamsu da amsar ta ba amma ya kyaleta ta tafi.
"duk sun san zan zo?" ta tambayeshi, eh ya amsa mata dashi yana jagora.
"sun sani, suna jiranki ma, sai dai ba kowa neh yake gda ba, my brother karami kin tuna shi" ta jin jina kai
yace "shi kadai yake gda sai babanmu"
ta jin jina kai "ba yau zan fara haduwa dasu ba, amma duk sai nake ji kaman ban san su bah, but no matter, zan maida hankali in ga na fahimci kowa"
yace good yana bude mata double doors din da ze sada su da cikin gdan.
Matan dake gda, suna falo zaune, harda Momma suna hira, sama suka tashi kowacce da fara'a suna mata sannu da zuwa, murmushi ta saki itama tana binsu daya baya daya suna gaisawa.
ya hanya
mutanen gda fah
ya kwana biyu
sune irin tambayoyin da suka dinga jera mata, tana amsa wani ana jefo mata wani saidai anxiety din su ya ragu sannan kowa ya koma ya zauna, koda aka ce ta je ta ci abinci ta amsa da toh. Jakarta ya dauka ya hau sama, a bayan shi yaji tana cema su yunwa take ji sosai dan bata iya cin abincin cikin jirgin ba. nan Inaya ke cewa tana son airline food, duk da it's not top notch.
Abu na karshe da ya ji shine Kiara ta amsa da "oh"
"Her room is 2 doors down" ya juya ya kalli meh Magana, "Nasan in da dakin ta yake"
Inaya tayi murmushi "tana cin abinci, in ta gama i'll take her there" nagode yace mata sannan ya bata jakar data mika hannu zata karba.
"Da gaske you were busy" ta amsa da uhmm, sannan ta tattare kayan babyn da take separating. Basu taba magana akan kayan baby ba haka beh taba attempting siya ba, koh tunanin abinda zasu bukata ma baby din beh taba ba. "Riha tnk u for preparing the room"
ta amsa da bakomai, kayan ta hada ta kai cikin walk-in closet dinsu sannan tayi shiru har saida taji rufe kofa sannan ta sulale kasa ta zauna. Fuskar shi take hangowa yadda ta murtuke da yaga kayan baby din tana hadawa, koda ya gano tana da ciki batayi kokarin siyan abubuwan nan ba saboda tasan baya so, wannan ma ba ita ta siya ba, saidai taga boxes din, wasu daga wurin farha ne sauran kuma Maman su.

YOU ARE READING
Zuciyar Tauraro
RomanceKudi. Shahara. Kyau. Duk babu wanda Allah beh bashi bah. The one thing da ya fi so ya kuma kasa samu shine So na asali da babu wani ulterior motive a ciki. Rashin samun abinda yakeso yasa yake kaffa kaffa da zuciyar shi,yake protecting zuciyar...