09:Get You Wet

783 82 3
                                    

🌠Zuciyar Tauraro🌠(Adams story).
By Bilkisu Muh'd.

09: Get You Wet

Ita dama haka take da saurin dabircewa, saidai na yanxu yana so ma ya fi na da, kuma tana alakanta hakan da sirrinta da Adams ya sani, shi yasa take firgicewa in yana kusa.

Tana tunani ta fito daga gda bayan ta gyara inda ta bata. Ƴa'ƴunta da suka bar brkfst din wai ta sa abincin ya fita ransu yasa ita ma ta kasa cin abincin. Yunwar cikinta mah beh dameta bah, abinda ya dauke hankalin ta shine chanjin fuskar data samu daga wurin Sa'ad. A da in tayi wani abu shine meh tsaya mata koda kuwa fadan ze dawo kanshi. Har cewa yake nature dinta yasa yake santa. Shi yasa cikin sauki ta fada kogon sanshi itama, gashi yanxu a fili yake hantararta, banda wannan kaunar Farha da yake nuna mata, abinda yafi kasheta shine kishinta da Farha batayi, instead ta biye mai suke kuntata mata.

Kukan zuci ta cigaba tana tafiya ta gefen footpath kusa da filin ball da kanta duke kasa, bata ankara bah taji ruwa na jikata ta ko wani gefe. Rudewa tayi ta hau gudu tana kare fuskarta dan zumbuleliyar hijab tasa har kasa. Saida ta bar gefen football field sannan ruwan ya daina jikata.
Bata kawo a ranta sprinkler system bane bah shi yasa kawai tayi gudu ta karasa cikin gdan su Yarima.

Tana shigowa gdan ya bar bakin window in da yake lekenta ta fallon baki ya wuce na can cikin gda, daya zauna kusa da mamanshi sai ya ja newspaper ya hau budewa kaman tun dama nan yake zaune.

Sharkaf ta shigo falon tana fiki fiki da idanu kaman kazar da aka tsamo daga cikin ruwan zafi, beh san sadda ya fashe da dariya bah yana kare fuskar shi da newspaper, bakaman da Momma ta tambaya in ruwan sama akeyi, cikin ranshi yace ' wannan ita kadai akayi wa ruwa' . Yana cikin dariya yaji an dan dukeshi, daya dago Inaya ke cewa "Haba Adams"
Daure fuska yayi sannan yace "Yanxu dariya mah laifi neh? Meh yasa ake sa jokes sections a jarida in nishadi laifi neh?"
Ya juya yana cigaba da magana, sai yayi kaman lokacin ya ganta "Ah ya akayi wannan ta jike?" Yayi tambayar fuskar shi na nuna mamaki,

Yarima yace "Fariha ya akayi?"
Juyawa tayi ta kalli bayanta dan itama ta danyi confusing,saida taji gari shiru da alamu ba ruwan sama ake bah sannan tace "Ina tafiya kusa da field naji saukan ruwa"
Yarima yace"Ayyah kinyi irin na Adams kenan, shima haka ya shigo ranar yace sprinklers ya jikashi"
Momma tace "Koh system din ya samu matsala neh"
Yarima ya amsa da i dont know,amma zansa a duba, Inaya kije da ita ta canza kaya pls.

Suna barin falon yace yayi maki kyau cikin ranshi.
Tana dawowa Yarima yace su haura sama office din shi, tare suka tafi dan ya zama dan guardian shima.
Bayan ta zauna ta fadi rana da tym  da Dr din yace ta dinga samun shi.
Yarima yace"Kaji Adams, so kayi including komai a schedule dinka dan kar ka manta" ya amsa da okay.

Yarima yace"Shikenan Fariha?"
Girgixa kai tayi amma bata ce komai bah, saida Yarima ya fara magana cikin sanyin murya yana tambayar yadda akayi sannan tace "Yace wai in dinga abinda nakeso, ni kuma ina so in koma aiki nah"
Yarima ya jinjina kai yana cewa "okay, dama Ali da Sa'ad neh ke da matsalan koh?"
   Tace "Eh"
Ya amsa "Okay,  kije ki fada musu kina so ki koma wurin aikin, kice ni na baki dama, kuma zan same su da kai na in fada musu"
   Sunkuyar da kanta tayi bata ce komai bah dan tasan Baffa Ali ze ci mutuncinta yace kara ta kaishi dan beh so tana aiki a gdan TV, shima Sa'ad ra'ayin shi daya da Baffa Ali, dan tun da aka fara  maganar hada su aure ya nuna beh son tayi aiki, da yake son shi ya makantar da ita sai ta aje aikin, kuma tasan yanxu ba karamin aikin shi bane bah ya sa ta tsani kanta dan taje da batun zata koma aiki.
   Kaman Yarima ya karanci abinda ke ranta yace  "Shikenan bari zanyi masu magana"

Tace nagode sannan ta tashi, zata fita hatishawa ya tsayar da ita saida ta jera guda uku sannan ta tsaya.
Yarima yace"Ikon Allah gashi har mura na son kama ki" ya kara da "Anya Adams sprinkler system dinnan beh baci ba kuwa"
Cikin ranshi yace 'ba wani baci, yayi aiki neh yadda ake so' a fili kuma cikin kulawa yace "Toh Dad koh a taimaka mata da umbrella neh, kar taje ta kara jikewa"
Da sauri tace "Aa bazan sake bi ta wurin ba mah".
Ya gimtse dariyar shi yana cewa ' ƴal kare, zaki sani neh next time I'll do worse than get you wet'.
Wata hatishawa tayi sai Yarima yace"Adams je ka sa a hada mata tea tasha kafin ta tafi"
Tana cewa Aa a barshi, Yarima ya cigaba da fadamai abubuwan da za a hada yana ignoring dinta.
  Yace "Toh Dad daga nan mah zan duba system din".

Zuciyar TauraroWhere stories live. Discover now