Page Twenty

148 7 2
                                    


🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Twenty

First abunda yazo mishi arai shine ya zaiyi yasamu wannan kudin? dankuwa ko karen hauka ne yacijeshi baya tunanin zaije yayi submitting kanshi dakanshi yace shine yashigo gidan ranar da dare because inyayi hakan toh tabbas bazai samu dubu goman ba Kuma Babu tantanma zai kirbu a hannun dogarayen Masarautar bakidaya,inkuma baiyi sa'a bama ace za'a sakashi a gidan yari. So dole wani alternative zainema, alternative dinda yakeda tabbacin it'll not stop him from going to Bauchi gobe dasafe but rather help him get the money he's been yearning for tun daren jiya.

Dabara ɗaya ne yazo masa arai kuma yasan if he's very careful wurin aiwatar da wannan dabarar it will surely help him achieve his goal. Anma fa tabbas kafin yayi going through with his plan dole seya nemi taimakon wani danhaka take yayi deciding yaje yasamu Hafiz su tattauna danyasan he's the only person that can help him dukda kuwa shiɗin ma yana kokwanton kozaiyi masa abunda yakeso ɗin ko bazaiyiba. Hanyar gidansu Hafiz yanufa dukda kuwa har lokacin safiyane sosai,jama'a basu fara fitowa daga gidajensu ba tukunnan se ɗan tsirarrun mutane dake wulgawa da ba'a rasa ba.

Daman gidansu Hafiz ɗin babu katanga se Ƴar karamar kofar dazai sadaka da cikin gidan danhaka Lamiɗo na'isa gidan yazagaya tabayan windown Hafiz ɗin sanin cewa inyace zai bubbuga kofar tasu toh tabbas zetada mutanen gidan ne baki ɗaya. leƙa ɗakin Hafiz ɗin yashigayi ta window inda ya hangoshi baje kan katifa yana sharara bacci shida kaninshi Musa. sunan Hafiz ɗin yashiga kira ahankali ko Allah zaisa yajishi yafarka amma segashi yayi masa kira yafi goma ko gezau beyi ba. Tsaki Lamiɗo yasaki sannan yashiga knocking jikin windown yana kiran sunan Hafiz ɗin. Musa dake kwance gefen Hafiz ne yaji kamar ana kwankwasa musu windown ɗaki. Buɗe idanunsa yayi dan tabbatar da zarginsa and then he saw the glimps of Lamiɗo,tashi yayi yazauna daga kwancen dayake yana mutsutsuke idanun sa dan son tabbatar da abunda idanunsa suka gane masa seyaji Lamiɗon yasake knocking windown. Kallon window yakumayi ayayinda Lamiɗo yashiga yimasa alama da hannu kan yazoshi,tashi yayi daga kan gadon yakarasa jikin windown yana kurama Lamiɗon idanu sannan cikeda mamaki yace "Hamma Lamiɗo?" Lamiɗon alama da hannu yashigayi mashi akan he should talk softly kada yatada sauran yan gidan sannan yace "buɗe windown Musa" sa hannu Musa yayi yabuɗe windown yana mamakin meyakawo Lamiɗo gidansu da sassafennan sannan yace "Ina kwana?" Lamiɗo yace "lafiya Lau. dan Allah tayarmin da kasan can. wannan ai se azo asaceshi ma baisani ba" dariya Musa yayi yana faɗin "kumafa baijima da komawa bacciba" ayayinda yakarasa jikin gadon yashiga tashin Hafiz ɗin yana kiran sunansa.

Buɗe idanu Hafiz yayi rai bace Jin irin bugun da Musan keyi masa dukwai da sunan tashinshi daga bacci fuska a murtuke yace "Wai miyene kake tashina?" Musa yace "Hamma Lamiɗo ne yace in tashe ka" tsaki Hafiz yayi Sannan yace "Lamiɗo kuma da sassafennan? Hankalin ka ɗaya kuwa?" Musa yace "wallahi dagaske nikeyi Yaya Hafiz. inbaka yarda ba ka kalli windown ɗakin mu gashican yana kallon ka" kallon direction ɗin windown Hafiz yayi rai bace and then he saw Lamiɗo waving at him,yana cemasa yataso yazo suyi magana.

Dole yatashi yazauna dukda kuwa baccin idanunsa basu ishesa ba,amma ya ya'iya? yasan koyace zaikoma baccinma Lamiɗo ba barinsa zaiyiba harsai ya sauraresa dan haka ya tashi yakarasa jikin windown yana mutsutsuke idanu sannan yadubi Lamiɗo yace "Wai meyafaru irin wannan sammako haka Lamiɗo?" Lamiɗo yace "lafiya lau kaidai shirya kafito waje muyi magana zaifi" Jin Lamiɗo yace Lafiya Lau yasa Hafiz cewa "toh jirani ba'in wanke fuskana se infito" Lamiɗo yace "alright be fast. Inajiranka"

Cikin mintuna biyar Hafiz yashirya yasamu Lamiɗo awaje yace "good news kakawomin kokuma bad news?" dariya Lamiɗo yayi sannan yace "toh dai za'a ce good news ɗinne tunda it's a way to success" Hafiz yayi murmushi yace "ansamu hanyar samun kuɗin kenan?" danko tantama babu yasan maganar kuɗin tafiya Bauchi ne yakawo Lamiɗon da safiyar Allahn nan tunda dabakin shi yace masa komai lafiya Lau agida.
Excitedly Lamiɗo yace "Exactly Hafiz" Hafiz yace "Ta wace hanyace za'a samun kuɗin?dako zaka yini kanayi a kasuwa? Kokuma Bara zakaje kayi?" Hafiz yakarashe maganar playfully,dundu Lamiɗo yakaimai yana dariya tareda faɗin "bana son iskanci fah Hafiz" Hafiz dabaibar dariya ba har lokacin yace "I'm sorry kaima kasan wasa nakeyi maka" Lamiɗo yace "whatever. nidai yanzu I need your help" Hafiz dahar lokacin fuskarsa na ɗaukeda annurin ƴar zolayar Lamiɗon dayagamayi yanzu yace "wace irin taimako zanyi maka? kafaɗa muji kozan iya" Kai tsaye Lamiɗo yace "zuwa zakayi Fada kace kasan barawon daya shiga masarauta ranar da daddare" ware idanu Hafiz yayi sannan yace "bangane ba? nasan barawon neni? Kuma how does that have to do with samun kuɗin ka?" cikeda kaguwa Lamiɗo yace "mekakeji na baka na zuba? kayi hakuri mana,zanyi maka bayanin komai ai" ajiyar zuciya Hafiz yasauke sannan yace "toh inajinka" Lamiɗo yace "Yauwa. katuna anyi guje guje a masarautar kan barawo yashiga a daren dazamu gama exams ɗinmu?" cikeda gamsuwa Hafiz yace "Natuna" Lamiɗo yace "toh ai ba'asamu ankama barawon aranar ba kuma haryau ba'a kamashi ba sabida anrasa wanene shidin,anyi bincike anyi bincike haryau ba'a gane wanene ba shine Sarki yace zaibada kyautan dubu goma a duk wanda yazo yace yasan waye barawon yakuma zo yanuna shi" wani kallo Hafiz yama Lamiɗo sannan yace "toh se mekakeson inyi yanzu?" Lamiɗo yace "zuwa zakayi kace kasan barawon" wannan karan harara Hafiz ya watsama Lamiɗo sannan yace "kafaɗi hakan ai yanzu. Sonake inji wakekeso inyi pointing as barawon don kasamu dubu goman?" sosa kai Lamiɗo yashigayi mischievously yana murmushi sannan yace "Ni zakayi pointing" Hafiz sarai yasan abunda Lamiɗon ze faɗa kenan shiyasa tun ɗazu yakeyi mashi wani kallo yanajiran yaji tabakinshi kafin ya san irin amsar dazai basa dan haka yace "You're totally out of your mind" sannan yajuya daniyar komawa cikin gidansu dan dagaske gani yakeyi Lamiɗon yasamu tabin kwakwalwa.

QADRWhere stories live. Discover now