Page Five - Young Geologist

482 44 1
                                    

🌹 _*QADR*_ 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

*Page Five - Young Geologist*

Inazaune kan benci wuraren takwas da ƴan mintuna haka sega su Lamiɗo sun bullo dukansu cikin shirinsu kamar kullum,hanyar gidansu Hari sukayi don karbar fura da nonon dasuka ce a ajiyemusu zasu saya dasafen nan sutafi dashi field wanda abakin Hari naji labarin jiya da dare takumace dayanma ma sunkarbi wanda sukace a ajiyemasu suka sha anan kofar masallaci sukayi sallah kafin suka wuce bakin hanya. dagudu natashi nashige gida ina kwala kiran Gogode,a rumfar kofar ɗakin ta nasameta zaune sanye da sabon kaya da alama wanka tayi tashirya zataje wani guu anma excitement ɗin tafiya neman gwal bebarni natambayi inda zata ba cikin yaren fillanci nace "Gogode mai yotti mindo dilla jonta ma (Gogode sun iso zamu tafi)" Gogode duban Baffa Idiii tayi sannan tace "sekaje kabada amanar tata kamar yanda kace zakayi ai" gyadakai yayi ahankali tareda kama hannuna yana faɗin "muje Ru'eyya" bye bye nama Gogode kafin muka fice agidan.

Akofar gidansu Hari muka samesu sunata miƙa gorunan daza'a dura musu nono da furar tasu bayan andama banda Lamiɗo. wanda naji sunƙira da Auwal ranan ne yafara ganina sakan baki yayi yana nuna musuni yace "wancan ba Ƴar birnin Lamiɗo baceba?" take dukansu sukajuyo suna kallona Lamiɗo dake zaune kan wani gungumen itace yana kallon yanda suke miƙa gorunan ana zuba musu fura da nonon yayi saurin tashi tsaye donshi yama manta deal ɗin mu najiya inba yanzu daya ganni ba.

Sakin hannun Baffa Idiii nayi naruga inda yake tsaye da gudu ina murmushi nace "Ina kwana" yace "Lafiya Lau young geologist" tura baki gaba nayi ina mashi kallon bangane meyake nufi ba nace "Young geologist?" Jan kumatuna yayi ahankali yace "eh mana,sunan da ake kiran duk masu karanta wahalalliyar course ɗin kenan and you're young shiyasa nakiraki da "Young geologist" murmushi nayi cikeda Jin daɗi sannan nace "har kayansu ma gashi nasaka" Lamiɗo yace "Kuma sunyi miki kyau ba,duksekika fimu fasalima anya gwalagwalannan bake zasu gani sufara fitowa dakansu ba Ƴar Birni?" dariya su Uztaz sukayi Auwal ya karaso inda muke tsaye nida Lamiɗo yace "Ƴar birni ce takoma Young Geologist yaukuma?" Lamiɗo na dariya yace "eyi wai taji ance ƴan Geology ketono gold shine tace zata bimu ta nemoma Gogode da Gwaggo Suwaiba gwal tanason suyi kwalliya irin yanda taga matan film nayi. tanason suzama yan gayu sumaaaaa" yakarashe maganar yana rawa funnily,dariya suka dingayi wa yarintata da abunda Lamido yayi nikuwa se washare hakwara nake nace "aitare zamu nemo bakaima zaka samona Aunty jiddah ba?" Yace "eyi anma ai inbansamu ba kikasamu zakibata koh? Tunda kince kinason tazama yayarki" Cikin sauri nace "eh zanbata se inraba musu su uku" shafa kaina yayi ahankali yana dariyar yarintata haka Baffa idi dake gefema harsuka gama amsan fura da nonon suka shirya tafiya.

Baffa idi yaƙira su duka yace musu nadage sena bisu suyi hakuri sutafi dani kuma yabasu amana na,suɗaukeni kamar kanwarsu duk inda zasuje su tabbatar Ina taredasu. Lamiɗo yace "indai wannan ne bakada matsala Baffa. insha Allahu zamu kula da Ƴar birni" godiya yamasu yakama hannuna yasaka cikin na Faith yace "kece mace Ƴar uwarta nasan kuma zatafi sakewa dake,dan Allah ga abokiya namiki kikula da'ita" murmushi Faith tayi tanasake riƙe hannuna tightly sannan cikin ragwababbiyar hausarta tace "toh Baffa kerka damu. She'll be safe with us" daganan yasake musu godiya sannan yabar gurin Uztaz da tunda ake maganar bece komaiba sabida Jin nauyin Baffa daya keyi harsaida yatafi sannan yadubi Lamido yace "yanzu fisabilillahi alkawarin daka daukar ma yarinyarnan ka kyauta kenan? ta'ina zata iya tafiyar wahalar dazamuyi? she'll just be a burden and nothing else"

Hafiz yakalli kafata yace "ga canvas ɗin tama babu grid ko dutsi bazaiyuyu tahauba kasani" Kabir dake gefe yace "Babu reflective jacket kuma ba and it's the most important sabida danger" duk senaji jikina yayi sanyi idanuna sunciko da kwalla Jin korafin dasukeyi,nafara tunanin kozasuce baza su tafi dani ba bayan nariga nagama kwallafa raina akan abun.

QADRWhere stories live. Discover now