Page Six - Young Geologist 2

417 43 1
                                    

🌹 _*QADR*_ 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

*Page Six - Young Geologist 2*

Lamiɗo yabudi baki zaimin magana kenan Uztaz yadafa kafadun Lamiɗo sannan yace "Kai fillancin kunnan ya ishemu haka. Uhmmmmgihkyoioo iyoo nyaaaanyaaa gusal garrrrr 6emu,warrr duk kukadai,habaaa! kun ishemu da yare bamusan ko A dakuke faɗa acikin sa ba" dan duk hirarrakin nan cikin yaren fillanci mukayishi.

Kabir yace "wayasani ma ko gulmar mu akeyi" Auwal ya hararashi sannan yace "kaikuma zaka fara koh?" shidai Lamiɗo dariyansu kawai yayi sabida yasan baswaji shiyasa tun fari yamin yaren wanda harmuka gama conversations ɗinmu basusan memuke cewa ba.

Bamuyi wani tafiya mainisa ba naji gaba ɗaya kafafuna sungaji,duk kokarina na ganin nadaure nayi tafiya kamar yanda sukeyi seda nakasa,nakoma Ina tafiya slowly anma dan jaraba naqi fadama kowa ciwon da kafata takeyi sabida karsu hanani binsu gobe. Lamiɗo tunyana tsanmannin jin nace nagaji harya haƙura yazo ya durkusa agabana yana nunamin bayansa yace "hauuuu tunda bazakiyi magana ba" ƙin hawa nayi sabida tun goyona da Gwaggo Suwaiba tayi Ina jaririya babu wanda yasake goyani senaji abun wani iri shiyasa naki hawa bayannasa atake dukda kuwa ina tsananin bukatar agajin daya kawomin ɗin. Jin nayi shiru kuma banhau bayan nasaba yasashi juyowa yana kallona yace "awww baki gaji da ciwon da kafafunki keyiba kenan?" kaman meshirin fashewa da kuka nace "Nagaji" yace "Toshine bazaki hau bayan nawaba?" tura baki nayi gaba sannan nace "Zanmaka nauyi aitoh" hararata yajuyo yanayi irin Ƴar karama dake ɗinnan zakice zakimin nauyi,kinma rainama karfina wayau sannan yace "bayanki ko nawa? Allah inbazakihauba Ƴar birni tashi zanyi kuma babu mai taimakon ki anan. tafiyar mu zamuyi mubarki anan har dare yayi zaki da birurruka suzo suyi badali dake" yakarashe maganar yana ƙoƙarin tashi daga tsugunen dayake nayi saurin ɗalewa bayanshi.

Dariya su Uztaz suka shigayimun,inkun ganni yar fiyot abayan Lamiɗo kamar wata yar shekara takwas dan daman karamin jiki gareni,ga babu tsayi gakuma rashin ƙiba duk ni kaɗai. dayawa mutane insuka ganni ɗauka suke shekaruna be haura goma ba dukda ma fuskata nada ɗan faɗi da girma dake nuna na fara manyanta. Seda muka isa Babban buli sannan Lamiɗo yasaukeni daga bayansa yana nishi yace "aradu kaɗan yarage baki ballaniba Ƴar birni. Kinji kirjina da bayana kuwa? sekace wanda naɗauki buhun shinkafa biyar alokaci ɗaya?" dariya su Uztaz suka mai Haifiz nafaɗin "Kai Lamiɗo! Kai Lamiɗo buhun shinkafa biyar ga?" dariya shima yayi sannan yace "kunaganin kamar wasa koh? kugwada ɗaukanta kuji" Auwal yace "ba'ance ana rotation ba kaƙi" Lamiɗo yace "eyi banason azo ana min gori daga bayane shiyasa. I want to prove my words kaman yanda nafaɗa dasafe she's my responsibility through out this field work tohakan yake har agama insha Allah" nidai jan hannunsa nayi nace "Muje kugaisa da Gogodena in faɗa mata kaika goyani muka dawo gida tayi maka godiya" cikin sauri yakwace hannunsa daga nawa yace "a'a Ƴar birni bayauba,sauri mukeyi zamu tafi anajiran mu abaki kwalta tun ɗazu" bahaka nasoba anma tunda yabada uzurinshi yana iya? dan haka nace "to gobe zakazo kugaisa?" Murmushi yayi sannan yace "Eh Ƴar birni" cikeda Jin ɗadi nace "Kuma zaka faɗa mata zaka haɗani dasu Aunty jidda suzama siblings ɗina koh?" gyaɗa min kai kawai yayi yana murmushi.

Daganan nama sauran bye bye nanufi hanyar gida inajin cinyoyina duk sunmin nauyi sabida gajiya ahakadai harna isa gida. Gogode nazaune cikin rumfarta itada indo sunacin muruci da alamadai itace tsarabar data kawo mana daga cikin gari don ko haufi bazanyiba yautafita ganin kayan dake jikintane tun safe haryanzu gakuma gyalenta agefe. Jin shigowar mutum yasasu ɗagowa suna kallona, Gogode cikin sauri tatashi tataroni tana tambayana meyasamu kafana cikin sauri nacemata babu kawai gajiya ne,tana shirin fara korafi nayi saurin rufe bakinta tahanyar fara bata labarin abubuwan danayi a field yau dakuma kula dani dasu Lamiɗo suka dingayi, nafaɗa mata goyona dayayi tundagacan har muka iso gida, nafaɗa mata biscuits da juices ɗinda suka bani duka sannan nace mata Lamiɗo yace gobe zaizo su gaisa.

QADRWhere stories live. Discover now