Page One - Meet my Family

979 64 6
                                    

🌹 _*QADR*_ 🌹
( _The story of Rukayya_)

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

*One - Meet my Family*

Sunana Rukayya Umar Shattima. Ni da iyayena da wasu daga cikin dangin mahaifina muna zamane a cikin garin Bauchi. Asalin mahaifina bafulatanin Giyade ne dake jihar Bauchi wanda most of his family members suna zama acan,mahaifin Babana wato Kakana babban Malami ne acikin garin Giyade da babu inda zaka shiga agarin Giyade katambayi waye "Mallam Abubakar Shattima" ba'a kaika har gidansa dake hade da tsangayarsa na almijiran dayake koyarwa ba. Kakana nada mata hudu wanda kuma cikinsu babu wanda bata haifa masa Da ba, Ya'yansa dai dai har goma sha hudu,maza tara mata biyar wanda agurin mahaifiyar Babana "Innani" mahaifina da kanwarsa "Suwaiba" kadai tahaifa Allah ya karbi ranta. Kaf cikin Ya'yan Kakana mutum hudu ne kawai suka maida hankali kan Western Education yayinda sauran daga sunyi Primary school suke watsar da karatun su koma na alloh dakuma harkar gonan mahaifinsu. Kawu Idrissa, Kawu Sani,mahaifina sekuma autansu a maza Kawu Adamu ne kadai sukayi karatun boko sosai wanda acikin sunma Kawu Idrissa ne kadai yakai har matakin gama jami'a inda sauran ukun primary, secondary da diploma kawai sukayi. duk karatun dasukayi mahaifinsu beki goya musu bayaba dan kuwa sauran ma yaso suyi karatun hadin kaine kawai basu bashi ba, Kawu Idrissa daya gama karatunsa besamu aiki atake ba shikuma bayason komawa zaman kauye dan yariga yasaba da rayuwa cikin garin Bauchi tunsanda yake degree dinsa,kuma aganinsa inyakoma candin kaman ci bayane don wannan karatun alloh da noman ne zekoma taya mahaifinsu,wannan dalilin yasa yasamu mahaifinsu yanuna masa yanason yafara business cikin garin Bauchi kuma yagoyamai baya dari bisa dari. Haka Kawu Idrissa yasaida dabbobinsa dankuwa kaf Ya'yan babu wanda baida gona da dabbobin sa nakansa gakuma na mahaifin nasu daban. Shago yabude akasuwa inda yafara bussiness din kayan sakawa,kama daga kayan Yara readymade,shaddodi,atamfofi dadai sauransu while on the process yana kuma neman aikin gwamnati ko Allah zaisa adace.

Wannan dabara da Kawu Idrissa yayi shiyayi motivating sauran kannensa da sukayi karatun bayan sungama sukanemi abunyi abirni suma,Kawu Sani shagon kayan abinci yabude cikin kasuwa wanda gradually yadinga bunkasa inda Kawu Adamu suka hada jari da Kawu Idrissa sukacigaba da kasuwancin saida sutura dan daman dakinsu daya kuma daga baya Kawu Idrissa yazo yasamu aikin gwamnati shiyasa.

Mahaifina saida kayan miya, vegetables da fruits yazabi yi dan bashida burin saida duka dabbobinsa, he still have passion for kiwo awannan lokacin. wannan dalilin yasa yasaida kadan daga cikin dabbobin nasa donsamun na jari yayinda yabar sauran ma kanwarsa Suwaiba data riga tayi aure acikin garin Giyaden tahada da nata tanakula musu dashi. tare akayi auren Kawu Idrissa da Kawu Adamu sekuma Kawu Sani daga baya,mahaifina baiyi aure dawuri ba sabida har lokacin baisamu wanda takwanta masa arai ba.

Tunda su kawu Idrissa suka fara tara 'Ya'ya suka yanke shawarar suda suke gari daya why not su sayi katon fili suyi gini kowa da apartment dinsa, atleast suna zaune guri daya kuma kan iyalansu bazai rabuba,koda suka tashi sayan filin seda sukayima mahaifina magana dukda kuwa baida aure kuma ya amince dari bisa dari,yabasu kudinshi suka hada hannu aka tada gini. ba'a jima ba kuwa mahaifina yahadu da mahaifiyata dake zuwa daga kauyen Babban Buli saida fura da nono cikin kasuwa inda gefen inda yake saida kayan miyarsa ne,anan yayaba da tarbiyarta yakuma ji takwanta masa arai yafara nemanta,sanda aka gama gininsu yasa iyaye suka shiga cikin maganar.

Har Babban buli akaje aka nema masa auren mahaifiyata Hauwa'u inda akabasu aka kuma saka rana kasancewar Kakanmu sananne ne shiyasa ba'ayi wani dogon bincike ba.

Bayan aure mahaifiyata da mahaifina suna zaman lafiya cikeda so da kaunar juna. Matsalarta daya ne batajin dadin zama da matan Kawunaina,sun tsangwama mata,sun hade kai sun sakata agaba kasancewar tunda can su sunriga sunsaba,ga ratan shekaru dasuka bata dankuwa mahaifiyata tayi aurene at a very your age,inban mantaba mahaifina yacemin agidansa ma tacika shekaru goma sha biyar a duniya.

QADRWhere stories live. Discover now