29

817 19 0
                                    

💫 SANYI DA ZAFI 💫

        ✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣9️⃣
Ahankali Mama tace "ni yar jigawa ce, anan kauyenmu yake ance kakan kakana daga Morocco yake wai saisa mukeda haske, iyayenmu dani da Yayana Sama'ila suka haifa, iyayena nada gonaki da dama a kauyen mu, Babana is a very very big farmer har su CNN sunyimai interview, banda nashi gonakin yanama mutane managing gonaki kaman gonakin sarkin kano nan marigayi Baba Ali naji yarasu, Allah ya jikanshi da rahama" Ahankali Riyad yace "Ameen" yana kallon Mama jin she just mentioned Babanshi, Mama tace "dudda a kauye muke Babana yasani makaranta yace yanaso na zama yar jarida nima namai interview wata rana, yayana Sama'ila shi baiyi boko ba tare suke komi na gona da Babana, kauyenmu ba school wani next village yakesa yayana Samaila na kaini makaranta kullum a machine dinsa saina dawo da dakaina" tai shiru tace "ina JSS 3 akwai wata rana nazo gida naga wasu maza guda biyu sunzo gidanmu na gaidasu natafi dakin Mamana, so daga bayane Baba kecemin ai sarkin kano ne da kaninsa Al Mustapha sunzo wajen Baba, nace Baba ina doki bangansu da kayan sarakuna ba, to alokacin nasan ashe sarakuna na private outing suyi normal shiga kaman kowa, gasu basu wani girma sosai ba Babana ya girmesu duka dan yadan manyanta, bayan kwana biyu Baba yacemin Kanin sarki na sona" Mama tadanyi murmushi tana kallon wani zoben dake hannunta tace "kafin kace me haka akamana aure anan kauye aka tafi dani gidan Sarautan Kano".
Wani irin kallon Mama Riyad keyi to be honest besan Mama ba, dudda yasan labarin lokacin auren anata cewa Baffa yakaro aure daga kauye and Baba supported him shiyamai auren, shida baison shiga mutane, banda hakama yawancin idan zakaga matayensu da Alkyabba zaka gansu unless you're very close to them ko kana zuwa bangarensu you hardly knows fuskansu, ko first wife na Baffan su is because tana zuwa wajen Mom akai akai yasa yasan ta daba hakaba dabai santa ba. Ahankali Mama tace "Riyad even though Mujitappa Baban Rashida yayi hurting dina deeply bazan taba iya ignoring the fact cewa that Man loves me and care for me kaman ba gobe ba, bai bar kowa ya hantareni ba, dakanshi yake koyamin etiquette na gidan Sarauta da sauransu, yasa aka cigaba da koyamin karatu a gıda, ya kuladani Riyad bai bar kowa yayi hurting dina ba hatta Jummai kishiyata" tadanyi murmushi tace "ance tana kishi dani alokacin sabida bata haihuba then nikuma bayan bayan 1yr da aurenmu saiga ciki watan cikin daya ajikina nafara ciwo sosai da saida aka kaini asibiti lokacin anmin all test but banda HIV banda komi nadawo gida yacigaba da kuladani yana nan nan dani itama Jummai surprisingly tana kula dani, tadena min kallon kishiya, she was so happy then zan haifa musu Baby" Mama tadanyi shiru kafin ahankali tace "ina around 5month Baba na da Mama na sukai hatsari a motan dazai kawosu Kano dubani, kawai abin yakara birkita jikina ina shiga 6month nai landing hospital ciwona was serious dahar ICU aka sani cus banajin magani, banci bansha na rame kaman tsinke, akamin test dayawa the next thing was inada HIV!" Mama tai shiru tareda fuzar da iska idanunta yayi ja tace "imagine ina around 1-2 months da ciki anmin all test ba'aga HIV ba ina 6 months da ciki ace inada shi dole Muji ya yarda maza nakebi da cikina da aka fadamai inada HIV, an sashi yazo yayi test din shima da matarshi Jummai sukayi su negative abinda yasa yasake yarda da zargin inada HIV sabida laulayin ciki yasa babu abinda ya shiga tsakanina dashi tundaga watan farko harna 6 din nan cus bana iya komi Riyad mugun laulayi nayi" Mama tai shiru tace "haka nadanji sauki aka sallameni yatafi dani gida naje na samu an kira yayana Sama'ila an tara jama'a a fada dan Muji bai iya fushi ba" ta share fuskanta chan tace "koran cin mutunci, koran toxarci, koran tijara akamin agaban kowa ana nunani ana shiga barayina bayi na watso kayana waje wai sabida cikin nema ba'amin duka ba aka korani no one! No one Riyad, Babu wanda a masarautan nan ya tsayamin ba mai Martaba Baba Ali ba! Ba mai Babban daki ba! Ba sauran matan sarki ba! Babu ne kawai aka koramu ni da Sama'ila ana tunkudani" runtse idanu Riyad yayi Mama tace "munafita daga fada Sama'ila yahau zubamin Allah ya isa bai yafemin ba wannan tijaran dana jamai da cikina ina fasikanci karna sake na bishi, Riyad haka yatafi ya barni dan uwana na jini biyar babu a hannuna ni da aka sallameni daga asibiti da safen ranan, nahau tafiya a hanya yunwa menene menene naje wani gidan abinci na wanke kwanuka na kusan kwana goma sannan natara kudi natafi kauyenmu nan ma Samaila yace ban isa na zauna ba, bashi bani nace to araba gado abani yace yaji haka yaraba yabani miliyan biyu nadawo nazo ina neman gida ahaka na sami gidanmu dakake gani nasaya akan miliyan daya agine ahaka nasai yar katifa nadan natsu nafara tunanin rayuwan to me yafaru? HIV Taya zan samu? Banda Mujitapa babu namijin daya taba rikemin hannu aduniya sai Babana da Yayana.

Nai tunani nai tunani narasa tayaya nasamu, nama kaina fada natashi natafi general asibiti, na hadu da Mrs Bugaje tun tana matsayin resident Doctor ta taimakeni da shawarwari da abubuwa da dama, dakuma ilimi kan yanda ake rayuwa da HIV, duk yanda zanbi nabi dan na samu Muji ya saurareni yaki bansan ya akayiba ko bibiyata Jummai take haka ta gano gidan nan ita tazo ta fallasama kowa na anguwan mu inada HIV nice Matar kanin sarki aka koroni menene menene, dabadan nina sayi gidan ba da sun koreni tuni, ahaka cikin wahala na haifo Rashida duniya ta CS, ban bata nono ba gudun karna bata cutan, duka kudadena na gado suka kare a siyamata madara da sauransu hakan yasa na dage nafara aikatau still ina zuwa asibiti ina karban maganin HIV da ake bamu free sabida y'ata banso na mutu inaso nataso da ita inaso na rayu nayi accepting ni mutum me HiV ce,  nacigaba da renonta harna soma gazawa ta karba aiki awajena tun tana primary school sabida Rashida nada kwazo" hannu Mama tasa ta share fuskanta tace "Gidan Sarauta wani irin gidane da bada kowa ya dace ba kaman ni yanzu I'm one, haryau bansan yanda na sami ciwon nan ba but nasan it's connected to gidan, banason wani alaka da gidan nan har abada!".

SANYI DA ZAFIWhere stories live. Discover now