15

944 22 6
                                    

💫 SANYI DA ZAFI 💫

        ✍🏻M SHAKUR

EPISODE 1️⃣5️⃣
Da gangan Munir yabar wayanshi awajen yadauke car key yafice, tashi Riyad yayi yawuce yasaka pajamas yadawo ya kishingida tareda lumshe idanu, wayan Muneer ne yahau ringing hakan yasa yabude idanu kadan yakalli screen din ganin Mom R yasa yayi shiru yana kallo wayan na dab da katse wa yasa hannu ya dauka yakai kunnenshi yaki magana daga ta dayan bangaren Mom tace "Son" ahankali yace "Mom ina yini" ijiyan zuciya Mom ta sauke she really miss him chan tace "sabida I questioned you zakai zuciya kabar gidan? Riyad when did you grow dahar zakabar min gida sabida namaka fada? Riyad I still see you as my little baby boy da I have to guide every step of the way, your are my purpose, you are the reason I become a Mom, did you really leave house yau kwana biyu sabida na tambayeka game da abu Riyad"? Mom tai maganan muryanta na tsinkewa kaman zatai kuka, Riyad yayi shiru Mom abin ya matukar bata mata rai tace "ko kakai 100yrs of being a man I will always see you as my little child, I will always tell you do this and that, I agree raina abace yake ranan datamin maganan dan kunnen nan and I wasn't thinking clearly, but still inada right nai fada, Babanka yayi aure aure but tell me menene fa'idan hakan yanzu? Kullum gidanshi cikin rikici makirci da fada ake, kalli Baffan ka tunda yama Amaryanshi koran kare bai sake marmarin kara aure ba sabida yaga implications din gashinan shida Jummai are living peacefully and happily, wat I'm saying is mata dayawa masifa ne, bazan taba bari ka auro wata wacce ban sani ba ko ban aminta da ita kaman Haleematu ba kafin azo arabani da d'ana that is the reason namaka fada and asked you ranan, and gashi nakosa naga Haleematu tai ciki amman shiru, dakaina nakai yarinyar taga gynecologist ance she's fine kaine dai baka cika nemanta ba, kuma ita Haleematun tagayamin yawanci koka nemeta ba rannan ovulation dinta bane saisa har yanzu batai ciki ba, mesa kakemin haka Riyad? Kai ba dan gidan nan bane bakaga yanda matan yayyinka ke haihuwa shekara shekara ba? Duk shirin da Babanku yakema yaranshi maza tun suna yara kaima an maka amman narasa mesa kakeda sanyi a harkan raya sunna" da sauri Riyad yacire wayan daga kunnenshi yanajin wani irin kunya da nauyi idan Mom namai irin maganganun nan, danna wayan kawai yayi a speaker ya ijiye agefense yana jinta. "Kap yaran family nan wlh basama matansu wasa kai har rama matan suke sabida yanda yaran Mai Martaba Baba Ali fire for fire ne akan matansu" wannan karan Riyad baisan sanda ya dafe kanshi yace "Mom can we change the topic please" cikeda bacin rai Mom tace "Kaci gidanku da change of topic Riyad, nabaka gobe come back home and continue kaga yanzu kayi skipping 2days babu abinda ya shiga tsakaninka da Haleema, kubani grandson nagaya maka saida safe" ta kashe wayan, ijiyan zuciya ya sauke yakoma ya kwanta tareda lumshe idanunshi.



Har Muneer yadawo a kwance yasameshi yace "ina tuki natuna wani abu daya faru dazu yanda dayar ma'aikaciyar yarinyar tace ma Masifaffiyar mamanta nada HIV" dagokai Riyad yayi yamai wani shegen kallo yace "and so"? Dan sosa kai Muneer yayi yace "bakomi kawai natuna abin ne" juyar da kansa yayi sai chan yace "HIV is just like any other ciwo, having it doesn't mean you are bad ko karshenka yazo, stop with the stigmatization" dasauri Muneer yace "haba noo bana stigmatization sai kace Baffan mu da akace ya kori matarshi mai ciki da akace tanada shi, ko tana ina oho"? Tashi Riyad yayi yace "let's eat" abinci suka shiga ci he ate alot kam yana gamawa yadauki laptop yafara aiki daman yunwa yahanashi yi.

Cikin bacci taji ana tabamata kai sabida tsabagen yanda bacci yau bai shigeta ba taba cikin tashin hankali firgigit ta farka.

Cikin dare sau biyu cikin dare Dr da Nurses sukazo duba Mama duk tana zaune bata runtsa ba harsaida Dr yace "kihau gado ki kwanta kusada ita mana ko ga babban sofa kihau" girgizamai kai tayi tana zaune kan yar kujeran dake gaban gadon, cikin sanyin murya tace "zan zauna anan" gyadamata kan Dr yayi yawuce harzai fita tace "ina bill dinmu?" Dan juyowa yayi yace "your bill has been cleared receipt duk suna cikin ledan drip dinta" yana maganan yabude kofa yafice from yanayin mutanen kawai yasan Mai Martaba taimakonsu yake.
Tashi tayi dasauri tawuce wajen ledan drip din da duk za'a sama Mama tabude taciro takardun receipt wanda na farkon na meal tagani 2 person breakfast 2person lunch dinner da snacks na 3days taga 270k, abincinta itada Mama kullum 30k for 3days 270k zaro idanu tayi takai hannunta tana dafa kirjinta, tadauki dayan receipt din single room dasuke dakeda gado sofa fridge da bayi is 25k per day kwana uku 75000, sai magungunan Mama gabaki daya da drip da allurai taga 497,250 wannan karan saida ta fada kujera ta zauna, duka kudin 842,250naira, kusan miliyan daya ta ina zata fara neman kudaded nan? No gobe zatasa a sallamesu, but ko an sallamesu sunyi kwana daya which is 25k daki, sai kudin magunguna 497,250 dole saita biya ta ina zata fara, hawaye taji sun zubomata sai kawai ta gogesu da sauri tahada duka receipt din ta linke tasa a jakanta tadauko kudinsu ta kara kirgawa duka savings dinsu kenan 150k tadade ahaka saita maida jaka ta kama hannun Mama ta rike har aka kira asubahi idanunta biyu tashi tayi tawuce bayi tayo alwala tafito tabude jaka ta ciro dadduma anyi alamun gabas aşaman dakin hakan yasa ta kabbarta salla ta idar tai azkar tana zaune kan dadduma Dr yakara shigowa dasauri ta tashi ta linke dadduma Dr yaduba Mama yajuyo yakalli Rashida datai zuru zuru yace "Alhamdulillah BP yasoma sauka, maganin zai saketa soon zata farka bada jimawa ba" gyadamai kai tayi, murmushi Dr yayi yace "Maman ki will be fine kinji" gyadamai kai tayi ahankali tace "thank you" wucewa yayi  yafita

SANYI DA ZAFIWhere stories live. Discover now