Part 1

31 1 1
                                    


Karatu takeyi setaji muryan mahaifiyarta hajiya khadija na kwala mata kira nan fa da sauri ta tashi tana fadin na'am, mummy ganinan xuwa.
Tana shiga dakin ta tadda yanuwa ta a dakin tare da mummy suna sauraron xuwanta.
sallama tayi irinta addinin musulunci "Asaalamu alaikum warahmatullah wa barakatuh"
salma ta amsa cikin murmushi "wa alaikum assalam warahmatullah wa barakatuh " yawwa dama ke kadai muke jira, dawo daganan.
halima ta xauna tana ne kallon yan uwanta biyu salma da kuma humaira sannan tace au kuna nan?
humaira tace eh muna nan muna tattaunawa kan aurenki xamu sama miki miji tunda kinqi kowa.
"Gayamata dae " muryar yaya abdul taji babban yayansu yana fadin haka.
halima tayi murmushi tace uhum! mummy ta kalleta tace kowa yana nan yana hira ke kina chan kina me? "karatu nadan yi sbd gobe inada test da safe karfe 8 mummy kuma course din yanada dan wahala" halima tafada tana me murmushi.
"Allah ya temaka "mummy tace sannan tace
ke kinqi fito da miji kinqi sauraron kowa ko to kiranki nayi nayi miki kashedi na qarshe ki fito da miji, girma kike. mahaifinku ya rasu ya barmin ku kuma aurar da ku shine abinda yanxu keda mahimmanci a gabana.
kin kusa gama karatunki kuma kinada ilimin addini me kuma kike so halima ? aure shine ynx kawai abinda ya dace dake ba kuma shawarar ki nake nema ba umarni ne, do you get it ?
"tohm mummy" tafada tana mai sunkuyar da kanta kasancewar halima me kunya da kuma nutsuwa.
kinji dae nagaya miki dama abinda na kiraki mu tattauna kenan you can go.
halima ta tashi sannan ta tafi tanata tunane tunane a xuciyar ta. ta shiga dakinta ta xauna ta cigaba da karatun ta yayin da lokacin sallar magrib yayi ta tashi tayi sallah sannan ta karanta addu oin t kamar yadda ta saba a kullum
ta shiga kitchen ta dibawa kowa abincin sa sannan ta samu wajen xama taci nata ta gama, ta gyara inda yakamata sannan ta nufe dakinta.
sallar isha ta idar ta qara komawa karatun ta. tana cikin yin karatun taji sallamar salma cikin dakin " Assalamu alaikum " ta ajiye littafin tana me amsa sallamar "wa alaikum Assalamu warahmatullah wa barakatuh " Salma tace ya halima har yanzu karatun ne?
Eh Shi nake ta duddubawa kinsan dr abubukar Akwai tsauri ya iya bada questions hm!
Ah ya halima dama Shi yake muku? Cab ai kuwa kuyita addu an Allah yasa ku huce lafiya naji yaya Abdul yana bawa mummy labarin kowa tsoron exam dinshi yake a school dinnan.
Kasancewar salma ce qarama sunfi shaquwa da halima. Salma na son halima fiye da yadda takeson humaira saboda halima nada haquri kuma da kulawa sosai Akan yan uwanta da kowa ma Wanda ya rabeta.
Salma yau ba baccin kenan. Hm! Ai xuwa naxo mudanyi hira kuma karatu kike karna takura miki so I'm going back seda safe!
Tohm seda safe karki manta da azkhar!
Tohm Insha Allah bye!
Halima tashi tayi ta gyara wajen kwanciyarta sannan ta koma karatun ta
Bayan halima ta gama karatunta ta ajiye littafin ta, tayi alwala sannan tayi azhkar ta kwanta.
Kiran sallar asuba takeji sannan ta motsa tana fadin "Alhamdulillahillazi ahyana ba adama amatana wa ilaihin nushoor" ta qarasa addu'o'in ta sannan ta tashi ta nufe toilet tayi addu a ta shiga domin yin alwala, bayan ta idar ta fito ta shiga dakin salma da mummy da humaira ta tashesu domin suyi sallar asuba.
Bayan ta shigo ta idar da sallar ta se xauna tana karatun Al quran kafin ta fara aikacen ta gida.

Fitowa tayi tayi tsaf ta shirya don ta wuce tasha abayar ta ruwan qasa tayi tsaf xata makarantar t sbd test din da takeda da kuma lectures.
Taje dakin Humaira ta tadda ta tana kwance tana chart tace da ita, Tohm ni natafi, ba yanxu xaki tafi ba ke ko, umayma tace kaiii what's this halima kinsan ni ai se 12 xan fita baxan iya irin wahalarki ba ta juya tana harare harare ta cigaba da chart dinta.
Halima tace bye!
Tace wajen mummy tana gyara Kayan dakinta na tare da limcy me aikinsu sannan tayi sallama tana fadin Mummy nagama ynx xan wuce insha Allah
Tom halima Allah ya tsare. Halima tace Ameen nagode mummy.
Sannan Tafita makaranta tane me musu sallama natafi sena dawo.

RayuwataDonde viven las historias. Descúbrelo ahora