part 2

107 10 0
                                    


HAIRAN 🥰♥️😭💔

No.2

Ayshatuuu

*Turare_by_ruky* I repeat *turare_by_ruky* are you a fan turaren wuta? Luxurious turare? Ko Kuma irin royalty scent dinnan kike so? Oils ne da khumra kike bukata? Then wannan brand din Kar ya wuce ki, turare ne da duk Wanda ya jishi se ya kalle ki saboda heavenly scent din shi, ga shi pocket friendly, lemme tell you ita kadai ce me turaren da Naga tana koyar da yadda zaki turare a gida, body scrubs and more, abinda muke cewa *DIY* Kuma duka free. Your's is just to follow her on TikTok ku bani labari.
https://vm.tiktok.com/ZMrhL6Ljy/
Contact her on WhatsApp👇🏼👇🏼👇🏼
https://wa.link/nuv5fy

*ISLAH FOODS!* Har yanzun surfe kike idan zakiyi kunu? Har yanzun wahala kike Sha idan zakiyi kunun Aya! Ya kike Yi idan kina marmarin tuwon dawa Dana alkama  and you have to undergo processes kafin kiyi? Ina masu Yara da zasu fara feeding din su da semi solid, ba dai har yanzun kashe kudi kuke a siyan cereals na gwangwani ba? To kuzo na Baku labarin *ISLAH FOODS* , na maimaita *ISLAH FOODS* wadda ta kawo Mana wannan garin kunun, garin tuwo na dawa da na alkama, garin kunun Aya, pap powder na Koko, ga custard powder processed and fortified cereal na Yara a saukake, daga ziplock se tukunya, a tsaftace Babu ruwanki da surfe da Kuma nika. Contact her 👇🏼👇🏼👇🏼

https://wa.link/fnx1ev



                             ***

Yadda yake da kyakyawar alaka da yaran shi yasa suke fahimtar duk yanayin da yake ciki, na dadi ne ko akasin hakan. Hanifa wadda ke zaune a gaban motar ta gefen shi, tana kallon yanayin yadda yake tuki kamar a gajiye akasin tahowar su da yake cikin farin ciki amma yanzun duk yayi wani irin, haka itama anata bangaren ta lura Anty Hairan din ma kamar kuka tayi saboda yadda idanun ta sukai jawur. Ta saki ajiyar zuciya tace

" Abbu!"

Ya Dan juyo kadan ya kalle ta yace

"Hanifa"

Tayi shiru saboda rasa me zata fadawa mahaifin nata se tayi shiru ta cigaba da cin abincin da take ci. Bai ce Mata komai ba ya cigaba da tukin shi a gajiye. Duk zuciyar shi a dagule take, tunanin shi a cushe yake, gaba daya ya rasa ta Ina zai fara, shi dai yasan har zuciyar shi komai da komai na jikin shi son Hairan suke, kaunar ta yake, wani irin so yake Mata me wuyar yayi bayani akai. Tun ranar da ya Fara ganin ta yaji gaba daya komai na shi ya koma gare ta, tausayin ta, son ta, kaunar ta komai ma Yi mata yake. Ya Kuma lokaci guda zata birkice kamar ba ita ba tace wai su rabu, a bar shi tace su rabu Amma a kalla ya kamata ta fada Masa dalilin wannan hukuncin nata ko?

Ya saki ajiyar zuciya lokacin da yake tsayar da motar kofar wani gida cikin daya daga cikin anguwayen dake garin na Zaria. Gida ne dai Wanda aka Dan Yi Masa kwaskwarima amma ko da daga unguwar zaka San asalin ghetto ce, ya samu yayi parking sannan ya dubi Hanifa da take kallon shi da wani irin excitement a fuskar ta, dole se da yayi murmushin ganin farin cikin da take ciki, juyawa tayi ta dakawa A'isha duka a cinya, ta bude idanun ta tana cona baki zatai fada se Kuma taga inda suke, da sauri ta bude kofar motar ta fice, Hanifa ma ta mara Mata baya, a hankali ya fito ya bude trunk din motar shi ya fito da manyan bakaken ledoji ya samu almajiri ya shigar da su ciki, se da ya rufe motar sannan ya shiga bayan ya gaida da few mutanen da ke wajen, dukda Bai gane su ba, Amma su din sun gane shi.

Da sallama a bakin shi ya shiga, Yana Jin Yaya tana fadin

" Ku fa Kuna da wauta, ya zuka bar Baban naku a waje?"

Sallamar shi tasa sukai shiru, ya shigo da murmushi a Saman fuskar shi, ya tsugunna har kasa ya gaida sirikar ta shi wato Yaya, cikin mutunta juna suka gaisa sannan ya Mike yace zasu juya saboda biyu da rabi har tayi, ta mike ta shiga daki babu jimawa se gashi ta fito da bakar Leda tace

HAIRAN🔥💥♥️Where stories live. Discover now