7

274 28 7
                                    

Yau ne ranar daurin auren Khalil. Tunda Batul ta tashi da asuba gabanta yake wani bala'in fadi ta rasa duniya me zatayi taji sanyi a zuciyarta. Ita dai tasan tabbas ba wai tana san Khalil bane, ko daya. Balle wai ko tayi tunanin kishi takeyi. Tana alakanta abunda takeji a zuciyarta da rashin sanin makomarta a wannan auren wanda har yau babu wanda yasan dashi face su uku. Kuma batasan yaushe za'a san dashi ba. Watakila har ya mutu babu wanda zaiji balle ya gani.

Tunda tayi sallar asuba take zaune kan sallaya babu abunda takeyi sai istigfari. Har yau bata manta da maganganun da Malama Hauwa tayi mata ba, ko da wasa Batul bata wasa da ibada da kuma rokon Allah. Kofar dakinta taji an kwankwasa saida gabanta ya fadi. Gidan cike yake makil da mutane, amma tasan hakan bazai hana Maama yin wulakancinta ba idan taso.

Tashi tayi jiki a sanyaye taje ta bude kofar. Ganin daya daga cikin masu aikin tayi wacce ta mata dan guntun murmushi. "Gashi inji Hajia tace wadannan kayan zamu saka yau." Tana fadin haka ta mikawa Batul kaya cikin leda ta juya ta wuce abunta ba tare data jira amsarta ba.

Batul komawa tayi cikin dakin ta bude kayan tana dubawa. Kusan wata daya daya wuce dama anzo an dauki awon kaf masu aikin gidan, to wata kila wannan dinkin ne za'a masu. Yau zasuyi 'mother's eve' a gidan bayan an kawo amarya da maraice. Da mahaifiyar Yusrah da Maama kawaye ne tun suna secondary school har yanzu, dan zama ka iya cewa sun zama aminai balle yanzu da suka hada auren yaransu.

Dalili kenan Maama tace ita zata shirya masu mother's eve wanda suka gayyaci kawayensu na nesa dana kusa. Dole Maama tayi masu wannan hadadden dinkin don kuwa bazata so ace ta gaza ba koda kuwa ta fuskar ma'aikatan gidanta ne.

Batul wanka tayi ta shirya amma bata saka kayan ba sai anjima zata saka. Fita tayi ta kama ayyukan da suka kasance nata duk kuwa da cewar sadidan Maama tayi hayar wani cleaning company sukazo suna gyara gidan tun lokacin da bakin biki suka fara yin yawa dan mace ce mai matukar kaunar tsafta.

Tana ta kallon agogo har karshe sha biyu tayi. Bayan Sallar Juma'a za'a daura auren Khalil da Yusrah kamar yadda aka daura nasu auren bayan sallar Juma'a. Ko zai tuna da nasu auren? Yar dariyar bakin ciki tayi dan kuwa tasan bazaiyi ba. Koda ya tuna saidai dan bakin ciki ba wani abun ba.

Aikowa akayi Maama tana kiranta bayan duk mazan sun wuce masallaci. Gabanta ke dukan uku dan ita har gobe tsoron matar nan take. Gashi har yanzu batayi mata maganar abunda ya faru bayan sun dawo daga kasuwa ba wanda tasan wannan aikin Abba ne dan inba dan haka ba kashinta da ya bushe a cikin gidan nan.

Koda ta gaisheta hade da matan da suke zaune cikin falon nata babu wanda ya amsa gaisuwarta. Saima daya daga cikinsu da tace, "Wannan ce wannan K'abilar da kike complain about?" a tare sukaja tsaki suna yan maganganu. Wasu har da cewa sai tayi hankali dan tsafi a wajen Igbos karamin abu ne ba babba ba.

Ita dai Batul kanta a kasa ko dagowa batayi ba har Maama ta gama abunda takeyi ta dago tana kallonta. "Bangaren Abba zaki gyara. Banso nazo naga koda digon datti a wajen, kina jina?" Ta furta murya cike da tsananin tsana.

"Eh Hajia." Ta amsa muryarta tana rawa. Harta juya zata fita taji wata mata tayi magana da fulatanci wanda hakan yasa Maama kiranta.

"Ke, dawo nan!" Maama ta furta da alamar bacin rai a muryarta. "Ba'a kai maki kayan danace zaku saka bane yau?" Ta tambayeta a hasale.

"An kai min," Batul ta amsa tana dukar da kanta gabanta yana tsananin faduwa.

"To me kike nufi da kayan dake jikinki?" Wasa Batul ta farayi da yatsunta dan batasan amsar da zata bata ba.

"Kiyi hakuri yanzu zanje na saka." Wani dogon tsaki Maama taja alamar ta bace ta bata waje. Da hanzari Batul ta fita daga falon har tana kusan tuntube tun kafin wata kuma ta kara wata maganar.

K'abila...Where stories live. Discover now