Page 1

5 2 0
                                    

*DALAL DALEEL*
         By
Fateema Mrs Ahfat

MIKIYA WRITING ASSOCIATION

Bismillaahir-Rahmaanir-rahim

Page 1

KANO STATE

Tsarin da Ubangiji ya yi wa halittunsa dole dukkan wani mai sauran numfashi ya gode masa da ni'imar da ya yi masa, musamman idan muka yi duba da yanayin da muke ciki a yanzu na Sanyi. Sassanyar iska ce me daɗi ke kaɗawa tana saukar da nutsuwa a zuciya, samaniyya ta duhu saboda tsananin hazon da ake yi masu lalura irin su Asthma suna cikin gida kamar yadda a gefen DALEEL al'amarin yake haka.

  Zaune take kan ɗaya daga cikin haɗaɗɗun kujerun parlorn ta harɗe ƙafa tana danne-danne a waya fuskarta ba alamar walwala, ta haɗe cikin riga da zani na atamafa ta sha daurin house wife adon nata ya ƙara futowa da asalin kyawunta.Jiran fitowarsa  kawai take yi ta sauke mai kwandon rashin mutunci. Cikin takunsa na ƙasaita yake sakkowa daga upstrais, kyakkyawan  matashin saurayi ne mai jini a jika dogo mai matsagancin jiki fari tass idanunsa dara-dara lumsassun wanda suke yanayi da kamar yana jin bacci baƙin sajen fuskarsa kwance yake luff-luff haka ma bakinsa da hancinsa  mai kyau wanda ya dace da fuskar sa, sanye yake cikin jeans da riga masu kyan gaske designers, parlor ya sakko kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai, ƙoƙarin wuce ta yake ta da katar dashi da faɗin "kai DALEEL!" tsayawa ya yi cak bai kuma juyo ba, a fusace  ta miƙe daga zaunen da take  ta ce  "kai wani irin banza ne mara hankali daƙiƙi?"  kai a ganinka zaka iya ja dani? To; bari na faɗama muddin ina raye a doron duniya ni HAJIYA A'ISHA sai na wulakanta rayuwarka kare da kake gani sai ya fika amfani shashasha  mashayi kawai, mu zuba mugani dani kake zance" tunda ta fara mgnr bai ce komai ba harta gama zancen da take, domin shi a zance ya ɗauki mgnr tata, ka faɗa kawai ya ɗage alamon ko ajikinsa ya fice daga parlors.

Murmushin mugunta ta sake tunu da mugayen shirinta akansa,  wayarta ta ɗauka latsa number HAJIYA ZUWAIRA  ta yi,  bugu biyu ta daga ba ko sallama ta ce "kina ina?" "gidana" ta bata amsa "ok ganinan zuwa ina fatan ke ɗaya ce?"  "Eh"  ba tace komai ba ta kashe kiran, ta ɗauki handbag ɗinta ta fita daman da shirinta.

DALEEL na fita parking space ya wuce kai tsaye bakar motarsa honda mai kyau da sheki  ya shiga  key yasa mata yabar gidan a ɗari, bai tsaya ko ina ba sai gaban wani babban gidan gonansa  dake Hotoro, danna horn ya yi ba ɓata lokaci mai gadi ya buɗe mai get ya shiga, yana paking ya fito ya wuce ciki ko gaishesa da mai gadi keyi bai samu daman amsawa ba sai hannu daya daga masa"

zubewa saman kujera ya yi ya lumshe lumsansun idanunsa da suka canja launi abubuwa da dama sun hadu sun  masa yawa a kwakwalwarsa, bude idanunsa ya yi yana mai furzar da iskan bakinsa hade da yamusa sumar kansa, zuciyarsa na kwaɗaita masa shan abunda baya son sha har cikin ransa, tausayin kansa da rayuwarsa ƴa ke, lumshe idanu ya yi ya shiga karanto addu'ar samun nutsuwa da kwanciyar hankali a zuciyarsa"

*"Allahmma inni as'lukath sabbath fil amr, Wal azimatu alar rushdi, wa as'aluka shukra ni'matika wa husna ibdatika,wa as'aluka kalban saliman wa lisaanan sadikan, wa as'aluka min khairi ma ta'alam wa a'uzubika min sharri ma ta'lam wa astgfruka lima ta'lam innaka anta allumul gayub*."

Sannu a hankali  damuwan dake damun zuciyarsa ta ragu cikin kaso dari hamshi duka ya ragu".

Da sallama ta shigo parlor  HAJIYA ZUWAIRA  zaune ta sameta ta yi dai-dai saman kayatacciyar kujera na alfarma gabanta cike yake da kayan motsa baki iri-iri"
Amsa sallamar ta yi tana murmushi hade da cewa" sannu da zuwa HAJIYA A'ISHA giwar mata"
Kasetattciyar murmushi ne ya subuce mata lokacin da take  zama kan kujeran dake kusa da nata ta ce" wlh har kin tunamin da Al-sheikh" murmushi itama ZUWAIRA ta sake ta ce" hmmm ai mutumin ba wasa, but me ya  faru na ganki cikin damuwa?"  Numfashi  HAJIYA A'ISHA ta sauke hmmm!
"Dole ki ganni cikin damuwa Zuwaira Alhaji zai dawo yau ga wannan dan iskan yaro tun last week ya dawo ga baki daya  bani da tsukuni ya samin ido duk wani motsina yana sane, in takaice miki yanzu haka kafin nazo sanda na fadamai magana son rai na"
Tunda ta fara mgn ZUWAIRA ke binta da kallo tana tabe baki harta gama labarta mata komai, Sanan ta sauke  numfashi ta kai Apple  din dake hannunta baki  ta gutsura tana taunawa a hankali ta ce"  wannan duk mai sauki ne kin manta irin gwagwarmayar da ki kasha a baya ko kin manta da irin abubuwan da kika aikata ne? har wannan dan abun zai daga miki hankali  Ki kwantar da hankalin ki insha Allah mune da nasara sai abunda ki ke so zaki yi, Kin san bamu da matsala da dawowar Alhaji duk abunda kike so zaki iyayi ba abunda da zai sauya zani, yaron nan DALEEL kuwa da ubansa  zaki  haɗa su  tunda ya tsani uban ba shiga har karsa yake ba Kinga da kansa zai karkata kayansa ya kara gaba tunda ba zama ya cikayi a kasar ba kinga shikenan kin samu abunda ki keso.
Murmushin jin dadin shawarar kawar tata ta yi ta ce" ai kuwa hakan za ayi sai dai ina da gudirin da nake son cimmawa kanshi.
Baki Zuwaira ta tabe tasan ko me yen gudirin ta kan DALEEL bazata bari ta cimmaci ba har sai nata gudirin ya cika, Hira suka shiga yi tsakanin kawaye sosai Hajiya Aisha ta  gamsu da shawarar kawar ta ta sosai suka sha hira kamin ta mata sallama ta wuce gida ta fara shirye-shiryen zuwan Alhaji."

*Adamawa Yola*

Boddo!"Boddo in kin san Allah ki sauka daga bishiyar nan haka mugudu tun kan  mai bishiya ya gammu mu shiga uku, kinsan Malam Iro bai da mutunci garama Malam Ilu akan shi yanzu jikin mu ya gaya mana.
" Ya gaya miki dai ke kadai banda ni wlh kuma Mangoron nan da kike gani na ciro
Tallanshi zanyi, ta fada lkcn da take dirowa saman bishiyar.
Zaro ido Indo ta yi adan tsorace ta ce" tallah kuma Boddo baki da hankali ne?" Harara Boddo ta watsa mata ta ce"  kin ganni da igiya a wuya an daure ni ko?" Ko kuma kin ganni  ina babbakar dariya kamar sabon dauri?

" A'a nifa ba haka nake nufi ba"  toh me kike nufi ehee?"  Kinsan halin Baffa wlh  in yaji labarin Tallan nan  kashin mu ya bushe."
Tsaki ta ja da  Allah manta da magarna Baffa ai in da baza'a ganmu ba zamuyi abun mu gida-gida zamuna shiga hamsin-hamsin ashirin-ashirin zamu sayar da kayanmu"
A'a wlh nidai tsoro nakeji bular Baffa akoi zafi aradu.
Du ka Boddo ta kai mata a baya ta ce" Allah ki fita idona na rufe tun wuri ki dauki mangoron nan mu wuce gidan ku mu dauki tire mu wuce Tallar nan ta fada tare da daukar wani ta yi gaba, itama dauka ta yi tabita a baya"
Tiren suka dauka suka jera mangoron a ciki Boddo ta aza abunta suka wuce, gida-gida suka shiga bi duk inda suka shiga dai ba sa'a haka zasu fitoh, kallon Indo ta yi cikin jin haushi ta ce" anyah ba hannu aka samin ba kuwa ace ko na ashirin ce ba wanda ya saya?" Dariya Indo ta yi ta ce" uhmm! yanzu muka fara ai" hmmm kawai ta fada lokacin da suka shiga gidan Malam Garba ko sallama bbu Boddo ta ce" asai mangoroo ga dadi ga garɗi ga kamshi ga ruwaaa....ha da idon da Boddo ta yi da wacce batayi sammanin ta bane ya......

Comment and shared fisabililahi 🥰

Mrs Ahfat

DALAL DALEEL Where stories live. Discover now