Page 5

0 0 0
                                    

*DALAL DALEEL*

By Fateema Mrs Ahfat

*Mikiya writers association*

Bismillaahir-Rahmaanir-rahim

Page 5

Bata san sanda ta kurma ihu saboda azaba daya ratsa ilahirin jikinta ba, take ta zube kasa tana  virgimar kamar zata shiɗe don azaba gaba daya kukan kasa fita ya yi, salati Baffa yasa yana kallonta da mamaki kwance a fuskar sa ya ce" kee Boddo me ki ke a saman katanga da daɗdare bayan yanzu na barki kwance kina bacci?" kuuu! cikinta ya ba da ganin Baffa ya ganota tasan yau kashinta ya bushe dole ta nemi mafita tun kafin ya kai mata wani dukan, hadiye kukun da take tayi  haɗe da  canja muryar  ta  ta ce" kai bil-adama me ya fito dakai lokacin da muke zagaye a tsakar gidan nan,har zakasa hannu ka ɗuki daya daga cikin mu toh dole mu dauki mataki a kan ka, in kuwa kanaso mu yafe ma toh ka wuce dakin ka ba tare da kai yi mgn ba ka kwanta duk motsin ɗa zakaji kar ka kuskura ka fito har sai gobe in ba haka yanzu mu mai daka biri."
Gyara tsayuwa Baffa ya yi Rai bace  ya ce "  ba biri zaku mai dani ba ko bera ne ba in da zani, bari mugani da ni daku wazai mai da wani biri, ya fada tare da daukar sanda da niyar kara sauke mata shi a kai ya sata saurin cewa"Baffa  ni ce wlh ni ce" ke wa?" Baffa ya tambaya wlh Boddo ce ta fada tana kokarin tashi ta gudu Baffa ya rikota ya ce" ina kuma zaki dawo  har aljanun sun fita a kan kinne  kai ta girgiza ta ce" eh eh, toh yanzu sai ki fadamin  ina ki ke kokarin zuwa a wanan lokaci ko inci kaniyar ki mara kunyar banza har ni ki ke tunanin zaki  tsorata ni da karyar aljanu ko?" Kuka Boddo ta sa har da jan majina ta ce" ka yi hakuri Baffa  Allah na tuba bazan sake ba nasan karo dakai ba dadi,  ni fisari na fito shine fa naji kamar motsin mutun yasa ni lekawa amma ka yi hakuri ka ji. tsakin ta Baffa ya yi  ya ce" toh na ji wlh idan na kuma ganin ki saman katanga sai na balla kafafunki ke bake jin tsoron kiji ciwo ko wani abu ya sameki cikin daren nan, ki sani rashin kunya da kin jin magana ba abunda zai amfane ki a rayuwa sai akin dana sani kinji, kai ta girgiza mai, ya ce" to wuce maza kije ki kwanta,toh ta fada ta wuce sai da ta bari ta isa kofar dakinta ta kalli Baffa ta ce" gaskiya ni dai ana shigan hakkina a gidan nan ba dama mutum ya fita da daɗdare sai a wani duki mutum kamar haushin sa akeji, tana fadar haka ta shige dakinta da sauri tasa ma kulli ta rufe, kai kawai Baffa ya girgiza yana murmushi wato sam Boddo bazata canja ba ya fada tare da wucewa dakin shi."tana shiga dakin ta sauke ajiyar zuciya ta ce" gaskiya na bugu sosai har wani zuuu nake ji ajikina Allah dai yasa kar Baffa ya kassarani tun banyi Aure ba da kuruciyata ta fada hade da kwanciya sabar son fitar nan da take ta raba daki da Inna kar tasa mata ido gashi ita bata samu fitan ba sai rabon wahala data samu .

Hajiya part din Alhaji ta wuce a parlor ta sameshi zaune ya yi nisa cikin tunani,  karamin tsaki ta ja ta karaso  ta zauna kusa dashi tana kallonsa wanda shi bai ma lura da shigowar ta ba,har sai da ta rike hannayensa kana ya dubeta,cikin kwantar da murya ta ce" Alhaji na wai me ke damunka tun dazun na shigo baka ma san na shigo ba kana can duniyar tunani please ka fadamin abunda ke damunka ko zan iya taimaka ma ko da addu'a ne, lumshe idanu ya yi a hankali ya ce" ba komai Hajiya  kawai tunanin yaron nan DALEEL nake ace ina mahaifin sa ban isah na sama mgn ya dauka ba ki duba fa ki gani gida daya muke dashi na dawo ace wai yakasa zuwa ya dubani shekara na kusan daya da tafiya bai ta ɓa daukar waya ya ki rani ba,  na dawon ma bazai zoɓa abunda yaga dama kawai ya ke aikatawa gaskiya lamarin sa ya fara isata wlh.
Murmushi Hajiya ta yi a zuciyar ta tace" hmm har yanzu da sauran ka"  a fili kuwa marairaice fuska ta yi ta ce" please ka dai na sawa ranka damuwa akan DALEEL kar wani abu ya samar min kai,  ina lura dashi tun lokacin da mahaifiyarsa ta rasu ya canja gaba daya kamar bashi ba, kasan ni tun da can ma ba kaunata yake ba ko zan kwana masa mgn bazai kulani ba, shawara daya kawai nake ganin zai iya canja shi ya dawo kamar yanda yake a ɗa,wani irin shawarane wanan  Alhaji ya fada yana tsareta da idonu, me zai hana kai masa Aure kawai! Aure kuma?" eh shi kaga Aure na daya daga cikin cikar Kamala mutuncin dan adam Mace ko namiji hakan zai kara fahimtar dashi yanzu shi din ba yaro bane daga lokacin daya fara tara iyali zai fahimci abunda ya ke yi ba dai dai bane.
Ajiyar zuciya Alhaji ya sake ya ce"hakane toh amma ina zamu samu yarinya wacce zata dace dashi?"ko yana da wacce yake so ne?" Hmm Alhaji kenan kamar ba kasan halin dan naka ba, murmushi kawai ya yi ta ce" eh man amma kar ka damu ni daman akoi yarinyar da na gani kwanaki da muka je Adamawa yar dan uwankan nan gaskiya  yarinyar tamin sosai naga tana da hankali sosai me zai hana kawai ayi tuwo na mai na kaga zumuncin mu zai karu ko yaka gani.
Murmushi Alhaji ya yi ya ce" gaskiya kin kawo shawara mai kyau daman tunanin zuwa dubasu nake nan da sati daya kinga idan naje sai mutattauna batun.
Murmushi jin dadi ta yi ta ce" Allah ya kaimu masoyina shi yasa nake kara sonka a ko yaushe ina alfari da kai, nima haka ina alfari dake tashi mu shiga ciki yau aji dani domin a gajiye dake wlh, murmushi du kansu su kayi suka wuce bedroom.

Akleema zaune take bayan ta kammala cin abinci tana kallon wani series a tashar Bollywood tana kallo tana cin cingom, sallamar Aadil a parlor ne yasata dago kai ta kalleshi tana amsa sallamar cikin tsakin fuska ta ce" sannu da zuwa Ya Aadil, yawwa kanwata yaushe a gidan?" Wlh yau  ina wuni ta fada da murmushi, lafiya kalau da fatan kinzo lafiya?" Lafiya kalau, ma sha Allah mutumin na ciki?" Eh ta bashi amsa tana kallon hannunsa dake rike da basket, shi kuma bedroom din DALEEL ya wuce da sallama ya shigo dakin, DALEEL da ke zaune sama sofa ya amsa sallamar iya kancin ci lips dinsa idan ba lura da bakinsa kayi ba zaka dauka ya yi mgn ba, dire masa basket din a gaba Aadil ya yi tare da zama gefen bed yana kallon mutunmin nashi  dake wani yatsine fuska ya.....

07061204735

Mrs Ahfat

DALAL DALEEL Where stories live. Discover now