DALAL DALEEL
By
Fateema Mrs AhfatMIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
Bismillaahir-Rahmaanir-rahim
Page 2
Ha ɗa idon da Boddo ta yi da wacce batayi sammanin ganinta bane ya sata tsakin tirin da ƙe kanta ya faɗi kasa. Inna ta gani zaune saman tabarma ita da aminiyarta Azumi wacce tun taso warsu suna tare har yanzu, barkan haihuwar amaryar malam garba da basu samu damar fitowa bane ya fitoh dasu, Baya-baya suka fara ja da sauri suka kwasa da mugun gudu sukabar gidan suna jiyo muryar Azumi da ke kwala musu kira Boddo! Boddo!!" amma ina sai ma kara gudun da sukayi, basu tsaya ko ina ba sai bayan gidan su Indo, Nunfarfashi suka shiga saukewa a tare sbd ba karamin gudu suka shaba, Kallon Boddo Indo ta yi kamar ta yi kuka ta ce" Shikenan kin jawo mana masifa da bala'i kan son kudi irin naki gashi kin samu a uku ga Baba Azumi da shegen munafurci yanzu ta samu a bakin duniya.
Tunda ta fara mgn Boddo ke sauke mata ruwan harara kamar idanunta zasu faɗo ta ce" keee! Indo fitah idona na rufe kar kiga ina raga miki wlh sai na mance da kawata ce ke naci mutuncin ki, ke ba sun kudin ne dake ba? da yanzu mangoron ya samu shiga ai ke ce nan Zaki fi amfani da kudin. Ganin Boddo ta bata rai yasa Indo ta ce" yi hakuri kawata yanzu dai ya zamuyi da Baffa ni fa tsoronsa nake duk iya shegena idan na ganshi nitsuwa nake.
Hmmm! bari kawai ni jikina ma har rawa-rawa yake amma kar ki damu ba abunda zai mana kawai ki yi duk abunda nace miki "Toh Indo ta fada tana dan tsakin fuska tasan mutumiyar ta ta tunda har ta ce ba abunda zai faru toh fa babu ne.Tafiya sukaci ga ba da yi kowa da abunda ke tsakawa a ransa kawai suka hango Halima yar gayu da saurayinta Haladu suna tafiya suna hira tamkar Romeo da Juliet duk wanda ke anguwar yasan suna matukar son junansu. Kallon juna sukayi Boddo ta ce" toh fa ga masoyan asali gaban mu yau zamu ga kalar tasu soyayyar wani iri ce. Kallon Karen Maman bile dake kwance a bakin shagonta ta yi kare ne mai masifar tsiya gashi da cizo, Maman bile ma sai ta daure shi da sarka take samun tsukuni shima sai yai yi ta damunta da haushi, yau zamuga karyar soyayya Boddo ta fada tana kallon Indo dake zaro ido tana kallonta ta ce" me kike nufi ba dai kwance Karen nan zakiyi bako?" ke dai ki zuba ido ki sha kallo, kafin Indo ta ce wani abu Boddo ta ruga da gudu ta nufi in da Karen ke kwance leka shagon Maman bile ta yi ganin bata ciki yasata lallabawa a hankali ta kwance Kare hade da kai mishi naushi a kafa ta ruga da gudu nan ta ke Kare ya bi bayan ta da mugun gudu sai haushi yake yana fiddo harshe Indo na ganin Boddo ta ruga itama ta ce kafa me naci ban bakiba ta bi bayan ta, wani mugun bangaja su Boddo suka musu kafin suce wani abu sukaji haushin kare da sauri suka juyo dukan su ganin Kare kusa dasu sai haushi ya ke yana fitar da harshe alamun kai far maki yasa suka kwasa da gudu Haladu na gaba Halima a baya sbd takalmin kafarta mai tudune ba ta sa ba tafiya dashi ba yauma tama masoyinta kwalliya ne dashi sai kuma aka samu akasi, ganin Kare ya kusa cimmata sai tasa kuka mai karfi tana cewa" wayyo Baby Haladu ka taimaka min kar ya cizeni na shiga uku, Haladu dake gaba ya ce" karo sauri dai masoyiya bazai cize ki ba abar kaunata idan ya cizeki ai ya jamin asara sbd cizon karen ba sauki kamar ma naji ance a fuska yafi cizo ai wlh ko kumatunki masu maka da tomatori ya ciza ai bansan ya zanyi ba balle kuma ace ya taɓa min kyakkyawan dogon bakin nan naki ina ga kishi zai sa na hadiye zuciya na mutu.
HAJIYA A'ISHA na komawa gida masu aiki tasa suka gyara ko ina na gidan ita kuma ta shiga kitchen ba bata lokaci ta hada masa tuwun semo miyar agushi daya sha naman rago sai kamshi ya ke dama Hajiya A'isha ba a baya ba wajen iya girki musamma ma idan tanaso, a part dinshi ta shirya mishi duk abunda zai bukata sannan ta wuce bedroom dinta ta tsala wanka cikin tsadaɗɗen lace dinkin bubu ta haɗe a ciki daurin ture kaga tsiya ta doka, ba karamin kyau ta yi ba tana cikin fesa turare wayarta ya fara rings batabi ta kan wayar ba taci gaba da fesa turaren sanda ta gama komai ta karaso bakin bed in da ta ajiye wayar ta dauka ganin Ustaz ne ya sata sakin murmushi ta zauna bakin bed din ta yi masa messages tana sending ta fito daga part dinta ta wuce na Alhaji tasan zuwa yanzu ya karaso."
Da sallama ta shigo kasettaciyar parlour da ya gama tsaruwa da zallar ababen more rayuwa aciki kamshin Air-freshener na tashi ta ko ina.
Zaune ta gansa saman lallasar kujera na alfarma yana waya, dan karamin tsaki ta ja ta karaso in da yake cikin takun kasaita da zallar duniƴanci ta zauna gefensa tana mai jifarsa da wani irin kallo, sun dauki lokaci a haka kafin ya ajiye wayar yana kallonta, murmushi ta sakar masa tana lumshe ido kadan ta ce" sannu da dawowa" murmushi ya danyi yana kauda kansa daga kallonta ya ce" A'isha banyi sammanin haka kike ba" kirjinta ne ya buga da karfi amma ta yi karfin halin cewar me kuma nayi daga dawowata Alhaji?" Ta fadane tana tsareshi da ido ganin ko ya gano shirinta.
Hmmm! A'isha kenan ki sani na dauki lokaci mai tsawo tare dake nasan halin ki ko da ace ba duka ba, na dauki kusan shekara daya da tafiya ko sau daya baki taba nema naba hakama dana nemi kizo cemin kikayi bazaki iya zuwa ba waya idan na miki baki dauka me kike shirin aikata wane?" Ya yi mgnr fuska ba wasa aciki.
Tunda ya fara mgn gabanta ke faduwa zuciyarta ke bugawa da ya ke ta iya duniyanci bata bari ko a fuska ya fahimci wani abuba ta sauke ajiyar zuciya ta kama hannunsa tare da marairaice fuska kamar tasa kuka ta ce" am very sorry ban taba dauka wannan abun zai bata ma rai har haka ba, ka sanni kafi kowa sanin halina kasan abunda zan aikata da abunda bazan aikata please karka sawa kanka damuwa ko shakka wani abu a kai na, kasan tunda ka tafi aminiyata HAJIYA ZUWAIRA ta samu matsala a kafa komai nike mata, ga DALEEL ya dawo sati biyu da suka wuce shiyasa kaga hankali duk na kansu kaga dukan su suna bukatar kulawata kuma naga aike ya maka yawa shiyasa ban cika son ina damun ka ba amma ka yi hakuri please ta fada guntun kwalla na sauka saman fuskarta."Toh me ye na kuka kuma daga mgn shikenan naji ki yi shiru karki bata fuskar ki, but DALEEL na gidan nan bai zo ya dauke ni ba? ko bai san da dawowata ba?" Ya sani mana na a zama shiya dauke ka a airport" no driver ne ya dauke ni, a masa uziri kila aikine ya masa yawa, kai ya geɗa zuciyarsa na kuna, ganin halin da yake ciki a ranta tace anzo wajen kallon Alhaji ta yi sweetheart muje kaci abinci ka huta kaji kar kana sawa kanka damuwa akan yaran yanzu musamman idan yaro na tabawa sai ana hadawa da addu'a, shidai bai ce da itah komai ba harta kammala zuba masa abinci ya ci sosai sannan ta ja shi zuwa bedroom.
DALEEL bai bar gidan gona ba sai mitsalin karf'e biyar na yamma yau kota-kota bai leka office ba duk da bukatar sa da suke, ya nemi zama shi kadai ne ko zai samu sassaucin abunda ke damun ruhinsa da gangar jikinsa.
Direct gida ya nufa ko da ya isah sosai ya yi mamakin ganin motar Dad dinsa a parking space hakan na nufi ya dawo kenan tunda ba mai amfani da motar sai shi, lips dinsa ya ciza ya wuce cikin parlour ko ajikinsa kokarin taka upstairs yake ya haura sama ya.....07061204735
Mrs Ahfat
