Page 3

1 0 0
                                    

*DALAL DALEEL*

By Fateema Mrs Ahfat

Mikiya writers association

Bismillaahir-Rahmaanir-rahim

Page 3

Mummunan faduwar gaba ƴaji lokaci daya idanunsa suka sauya launi zuwa ja, tunda ya ke bai taɓa jin maganar data taɓa zuciyar sa kamar na yau ba, tattausar murmushi ya tsake
Wanda rabon da ya yi makamancin sa harya manta,kamar wanda akaima sakon mutuwa haka ya sake murtuke fuska kai kace ba shine yake murmushi ba, bedroom dinsa ya shige cikin takun nitsuwa hade da kasaita saman modern grey 3 steater sofa ya zauna hade da zaro waya cikin aljihun wondon jeans din dake jikinsa ya dan yi danne-danne na wasu mintu na ya ajiye tare da rage kayan dake jikinsa ya shige toilet watsa ruwa yayi tare da dauro alwala ya fito gaban mirrow ya tsaya yana karema kanshi kallo daga sama zuwa kasa,kamar wanda yake neman ganin wani abu a jikinsa kuri yai ma kyakkyawar fuskar sa da take kwance da saje wanda ya kara kawata kyawun fuskar tashi gami da lallausar kasumba idanun sa masu girma da haske ya zubawa mirror din yana mamakin yana yin sa da yanda rayuwa take juya masa kamar bashi ba haka yake ganin kanshi acikin lokaci ɗaya, kiran sallah daya rasa kunnuwansa ya sashi sakin boyeyyen ajiyar zuciya tare da dauko whiskey smoke perfume mai sanyin kamshi ya feshe jikinsa dashi ya nufi wardrobe white quality jallabiya mai taushi yasa tare da fita daga bedroom din cikin sauri ya nufi parlor jin har an fara kokarin ta-da sallah, kokarin fita daga parlor yake su kaci karo da Akleema dake shigo da akwatin ta parlor,bai bi ta kanta ba ya wuce zuwa Masjeed. Murmushi ta bi bayan shi dashi ta shige parlor tana kwalawa Hajiya Aisha kira da karfi Hajiyaaa... Tsaki Hajiya dake kwance tana chats fitar Alhaji kenan zuwa Masjeed ita kuma ta dauki wayarta duba sako kawai ta jiyo muryar Akleema,  a fili ta furta kaii na shiga uku da wannan jarabibbiya yarinya dole na dauki mata ki a kanta tunkan ta ruguzamin shiri naga kanta na rawa sosai,ta fadi hakan dai-dai lokacin da Akleema ta turu kofar bedroom din ta shigo ba neman izini bare sallama ta ce" Hajiya daman DAL ya dawo shine baki sanar da ni ba?" Wani kallon banza Hajiya Aisha ta watsa mata fuska dare ta ce"  ke din wace  da har zaki rasa parlor na ki shigo har bedroom ɗina kina min hauka?" Toh ki sani in kinason zaman lafiya dani ki dai na shigan abunda bai shafe kiba, ki sani nan gida nane abunda nakeso kawai ake yi akasin haka kuwa hmm!kema kinsan sauran... Kallonta kawai Akleema keyi tana jinjina kai ta ce" hakane zancen ki dutse gara da kika tunamin duk da kuwa ba mancewa nayi, ta fada fuska dauke da murmushi ta fice daga bedroom din.
Kai Hajiya ta dafe tana ajiyar zuciya duk sai taji ta tsargu da murmushin da Akleema ke yi ta san kan kayanta ciki da bai mundin ta bari abunda take hangowa a kwayar idanun Akleema ya tabbata komai  zai iya faruwa bazata bari shirinta na shekara ashirin da hudu ya lalace a lokacin da take gap da cinma nasara ba....

Boddo gida suka nufa tun a kofar gida suke jin muyar Inna na zuba matsifa kamar ta ari baki, zaro ido Indo  ta yi a tsorace ta ce" tab gida zani bazan shiga ba kawai mu haɗe da daren,Tsaki Boddo ta ja ta ce" baki isah ba dole mushiga tare bazai yu na shiga ni kadai ba, ta fada tana kamo hannun Indo dake kokarin guduwa, dan Allah ki bar ni na tafi wlh tsoron Baffa nake ji" toh ni ce miki akayi bana tsoronsa kawai jahadi zamuyi mu shiga komai ta faru mu muka jawa kammu, Aa wlh ke dai kika jawo mana ina zaman zamana Baba Malam ya sani dibar ruwa na kai wa dabbobi  susha na yi fatali da bokitin na biki gashi abunda kika janyo mana wayyo Baba Malam ka yafen" Kee da Allah rufe mana baki mu shiga cewar Boddo tana turata cikin gidan suka shiga da sallama kamar munafukai sai zare ido suke suga ta ina zasuga Baffa ganin kamar baya nan ya sasu kallon juna suna murmushi, Inna da ƙe  zaune saman taburba ta daure fuska tana kallonsu ta ce" toh marasa kunya daga ina ku ka fitoh?" Basuce komai ba sai ido da suke binta dashi ganin ba wasa a fuskarta, zakuyi mgn ko sai naci gidan ku, Lungoɓe fuska Boddo ta yi ta ce " Don Allah Inna ki yi hakuri bazamu tsake ba sharrin shaidan ne, shi ya shiga ya fitah har yaci nasasar samu yin abunda bamuyi niya ba, gashi  yanzu ma shi yake tunzu raki kike jin kamar ki rufemu da duka ko Indo?" Eh eh hakane Allah rabamu da sharrin shaidan kamar hadin baki suka tsaki kuka a tare suna fadin Amin" tsokoko Inna ta yi tana kallonsu tana mamakin rashin kunya irin nasu yarane ko yaushe da maganar da zasu dauko wa mutane yanzu nan da ƙyar ta samu bawa Malam Iro hakurin shigar masa gona da suka yi suka masa barna  ɗa ya ce bazai hakura ba amma mutuncin dake tsakanin su ya sashi hakura ya fice yana babbami, gashi yanzu suna gaya mata sharrin shaidan ne" tsaki Inna ta yi ta ce" zaku rufewa mutane baki ko sai na tashi na sameku a gurin munafukai kawai ba wani shaidan dake saku yima mutane rashin kunya sai shaidanun dake kanku, ganin Inna ta fara masifa ta inda take shiga ba nan take fitah ba, yasa Indo tsulalewa ta bar gidan Boddo kuma ta shige daki ta kwanta saman gadon ta mai rumfa irin na gargaji na ɗa, tana tunanin yanda zata sati hanya ta fita da dare gashi tasan dai Baffa bazai taba bari ta fita ba tana tare dashi a dakin karatu dole sai tasan yanda zatayi ta fito.

DALEEL bai bar Masjeed ba sai da akayi sallah i'sha a hanyar dawowa ne suka haɗu da Daddy daga gaisuwa ba wanda ya tsake mgnr  cikinsu har suka shigo cikin gida,Daddy ya wuce part dinsa shima ya wuce nasa, a parlour kasa ya samu Akleema hakimce saman kujera ta daura kafa daya kan daya tana lasa waya, kallo daya ya mata ya dauke kai ya wuce kamar bai ga wani halitta zaune a parlor ba,ganin zai haura sama bai ce komai ba ya sata kiran sunanshi da tsanyayyiyar murya ta ce "  Yaya DAL"
yanda ta yi mgnr a tausashi ya sashi tsayawa  bai juyo ba kuma bai ci gaba da tafiya ba, ganin hakan ya sata mikewa tazo gabansa ta tsaya tana kallonsa ta ce" wanan miskilancin naka mugun burgeni yake sosai i likes it too much! But  Yaya DAL yaushe ka dawo bamu da labari......

07061204735

Fateema Mrs Ahfat✍️

DALAL DALEEL Where stories live. Discover now