MAFARI

16 1 0
                                    

Bismillahi rahmanir rahim ya rabb yanda ka nufe ni da farawa ka bani ikon gamawa lpy
Allah ya kara wa annabi daraja (S.A.W).

***
Yamaltu Gombe State, Nigeria.
Sauri sauri take ta qara sa sharar Gidan dabbobin dan an kusa fara shirin da take balain so ko na minti daya bata so a huce ta shiyasa ta maida hankali ta gama aikin ta da wuri saura in da take kadai ya rage

Abun da bata sani ba shine ba lallai ma yau kallon ya yiwu a gurinta ba, ko kuma ma kwanakin da ke da kusanci da yau din

"Ba xaka taba sa ka mutum abu yayi maka shi dai dai ba har dai baka tsaye a gurin yanxu fisabilillahi meye haka iye boddo, nace meye haka bana son fa wannan qiwar taki da baqin halin da ki ka kwaso a can haka, amma in ba ma salon barna ba da kin raina ni ba haka ake rude nace haka ake rude? Duk kin barnata gari to tun muna gane juna ki xo ki gyara shi kan a ji mu da ke tunda ke kullum in baki sa mutum magana ba ran ki baya dadi, ki maxa ki gama sharar ina nan ina jiran ki.

Muryar gwoggo ke tashi tana ta faman fada akan ruden da boddo tayi

Gwaggo nafi fa na daki ko xata dan taimaka min da debo ruwa kan in gama sharar, in na xuba musu ruwan sai na xo na gyara

Ungo nan nace ungo naki boddo wata kam naga alama rainin ki ya samu qaruwa kwana biyu a gidan har da ni ki ke son maidawa tsarar ki ko?

Ah! ba laifi xan yi maganin ki mara kunyar banxa to naji tana dakin ba ita nayi niyya ba ke din naga dama kuma ke xaki yi.

Qas qas qas ka ke ji a tsakar gidan sautin taunar chewing gum ko ba a fadi ba ta sani ba kowa ba ne sai adda ai, ita ke wannan dabiar karuwan kana cin abu na nesa da kai taku goma na jiyo sauti, fitowarta daga wanka ke nan

"Ke ! zo ki kai mun guga gurin jamilu" abn da tace kenan kawae ta shige cikin dakin su ba tare da ta ko kalli fuskar boddon ba bare ta san yanayin da ta ke ciki, umarni ne kawae ta bayar me cike da gadara

Tana tsaye taji dirar abu a fuskar ta qullin kayan adda ai ne set daya ta jefo mata tare da fadin ta zo ta amshi kudin, ko yunqurin taba kayan ba tayi ba balle ma ta riqe su, dirar kayan a qasa kuma yayi dai dai da leqo da kan addar daga daki

"Kan uba" abn da ta fadi kenan tana qarasa fitowa daga dakin lallai wuyan ki ya isa yanka abu, yau naga sabuwar fitsara ki ka tsiro da ita a gidan tun daga bayi nake jin turka turka da ake dake a gidan nan kuma yau ba sai gobe ba zan sauke miki ita da duk wani rashin jin da ki ke ji da shi, ko numfashi bata ja take rattabo wannan mitar ma boddo tare da yo kanta gadan gadan

Bata ko yi gezau ba balle ta motsa daga inda take, ba kuma alamar razana a tare da ita Ba yau ne rana ta farko da take kaiwa adda ai guga ba in xata tafi gantalin ta da sai lokacin da ta ga dama ta ke shigowa amma yau dai kam ta yanke cewa ba xata ba ko da me hakan zai janyo mata kua don yau ji take tana dai dai da duk wanda ya shiga shirginta kuma ko da waye bata cire kowa ba.

Ta daga hannu zata xabga ma boddon mari ke nan su ka jiyo abn da duk ya ja hankalin su ga qofar, har tana sauke hannun ta ba tare ma da tasan hannun ya saukan ba bata ida nufin ta ba

"Balki, balki, wai kina ina ne? Murya baffa da shigowarsa kenan ke qwalla kiran da alamun yana cikin firgici ko wani abu makamacin hakan don yacce ya shigo gidan kamar an jefo shi

"Haba malam wannan kira haka kamar an ce maka na samu kurumta ai ka bari ka ida sa shigowa gidan goggo ta amsa shi tana me hada fuska dan ranta ya gama baci ba tare da tasan dalilin kiran nasa ba, kuma tasan ma ba wai lallai dalilin kiran yayi mata dadi ba, haka dai ta qarasa tabarmar da ya xauna tana kumbure kumbure

Kallon mai cike da gargadi da qasqanci adda ai ta bi boddo da shi tare da dibar kayanta ta bar gurin don tana son jin me baffa ya zo da shi

Qara murje idonta take don ta tabbatar da abn da take gani ba gizo bane, hannu ta kai zata taba ya janye ledar daga gabansa ya maidata gefen sa yana mai jan qaramin tsaki

"Dadina dake rashin haquri balki, ai abn da ya dawo dani kenan, kan ma ya ce komai har ta saki fuska tana faraa tun bata ji bayani ba, ba wannan ne a gabanta ba burinta bai wuce ya gama xancen sa ya yaga mata kason ta ba ko ma ina ya samo su ita ba abun da ya shafe ta bane.

Tiryan tiryan ya mata bayanin da  ya sanya fuskar ta qara hadewa fiye da farkon dawowar sa tare kuma da jefa ta cikin tunani

"Boddo" baffa ya qwala mata kiran da sai da gaban ta ya fadi ture kayan da xata ninke din tayi ta nufi kiran da yayi mata, kiran da ya yanke tunanin da goggon ta take don bata yi tsammanin yanxu baffa ya tsara sanar da boddon ba saboda sanin halin ta, ta dau zai jira ya ji shawarar ta ko yaya ne

Tsugunawa kawae tayi kanta duqe a kasa ba tare da ta ko kalli fuskokin su ba bare ta karanci wani canji ko kuma har ta lura da wani abu dake gurin bayan baffa da goggon da ta riga tasan da wanzuwar su

"Boddo, Ina so ki bude kunnen ki da kyau ki saurare ni, bawa baya wuce qaddarar sa kuma duk abun da ki ka ga ubangiji ya yanke akan bawan sa hakan shine mafi alkhairi ko da shi bawan ba haka ya so ba, zan so ki bude zuciyar ki ki fahmici hakan

A yanda baffan ya tausasa murya da kuma maganganun da yake da bata fahimci inda ya dosa ba yasa dago kanta dan ta ga yanayin fuskar sa, ko xata fuskanci wani abu, akan kudin dake gefen sa idon ta ya sauka

Yaga sanda idanuwanta suka sauka kan kudin dan haka ya yi amfani da damar don shima bai san ya xai fara mata bayani ba a taurin kanta da ya sani.

"Sadakin ki ne Boddo" muryar sa ta katse tunanin ta duk da taji xancen ne kamar bada ita yake ba don bata san ana bada sadaki kafin aure ba, banda ma haka ita ba su yi xancen aure da musan ta ba, qarasa daga kai tayi suka hada ido don tana da buqatar hakan

Kan sa ya gyada mata yana mai bata tabbacin eh abn da ya fadi hakan ne

"Yanxu daga gurin daurin auren ki gida kawae na zarto, hamman ki Tukur shi ya bada ke ya kuma daura auren yau ina fata ba xaki bashi kunya ba"  ya fada da siga lallashi.

Iya auren ki kawae taji ta shiga tunani, to musa ya zai yi mata haka kuma wani tunanin da ya xo kanta a lkcn take ya saka kyawawan idaniyar ta soma rikida zuwa launin ja don bata ma ida sa tunanin nata ba tayi saurin qara kallon baffan nata, tana so ta tambaye shi abn da ke yawo a cikin zuciyar ta amma kamar an dinke mata bakin, ya mata nauyi don bata san wacce amsa xata samu ba, in sabanin abun da take son ji ne qwaqwalwarta ba xata iya dauka ba sai kawae taci gaba da bin sa da ido

Shiru gurin ya dauka kowa da saqar da yake a zuci, sai bayan kamar minti biyar ta tsinci bakinta na maimaita Kalmar

"Aure" ni?

Wani dan murmushi ne ya subuce mata
Tace ko dai adda ai ka ke nufi baffa?

Kamo hannun ta yayi ya riqe yace ke aka daura ma aure yau ZAINABU, yau kin zama matar MODDIBO.

Dinn din din
To fah ya ku ke gani za a qare anya kuwa Boddo xata karbi auren nan?

Wace ce boddo?

Hamma Tukur ya kyauta kua?

Modibbo?

Labarin su mai tsaho ne......

FUREN TUMFAFIYAWhere stories live. Discover now