Wayewar garin yau ba wanda ya shiga sabgar ta, ita ma bata kula shirgin kowa ba ayyukan da ta saba yi kawae tayi, ta koma qasan bishiyar da ke tsakar gidan na su tayi xaman ta, yar dama kawae take jira ta aiwatar da abun da take son yi.
**** Asokoro Abuja, nigeria
"Wai ni habibi xai wa kishiya, kuma ma qaramar yarinya, qanwar bayana ko ma ince yar cikina, a yanda ya fadi wai shekarar ta sha biyar" ta fada tana mai jin wani baqin ciki yana kawo mata iya wuya"Ina ga xama na da shi ya qare mummy.
Fauxa ce ke waya da mahaifiyarta tana labarta mata irin cin fuska da a ganin ta habibun yayi mata
"Dadi na da ke gajen haquri, daga dauro aure amaryar da bata ko kai ga tarewa ita xaki sallamawa miji, mijin ma irin naki me wuyar samu da ko ni ban yi saar irin sa ba xaki barma wata?
Toh maxa ki dawo hayyacin ki kan raina ya baci wlhy".
Zumburar baki tayi kamar tana ganin uwar
"To ni mummy wlhy yau gida xan kwana"
"Yanxu ki ka xo da xance, da haka ki ka ce tun fari ba xa a ji kan mu ba, ni ba xan hana ki nuna fushin ki ba sbd gskya an miki laifi amma in baka iya kama barawo ba ai shi sai ya kama ka,
Ki dauko dan abun da xaki buqata ki taho din sai mu san abun yi.***
Raguwar zirga zirga da aka samu a tsakar gidan da daukewar numfashi saboda rana da ta bude da daman wannan lokacin take jira, sai ta saci jiki cikin sanda ta ficeZaune take da tsohon cikin ta haihuwa ko yau ko gobe ta ji sallamar qanwar ta ta, abar qaunar ta, ba tayi mamakin zuwan nata ba saboda ta tsammace ta dama, tana da tabbacin xa ta xo din ranar da zata zo ne dai bata da tabbas.
"Waalkmsslm boddo am, jabbama"
Tana fadada faraarta tare da nuna ma boddon daf da ita ta xauna
Maimakon xaman xua tayi ta rungume ta da cikin tana mai sakin wani marayan kuka, runguma ce mai cike da qauna, kewa, kai kuka a inda mutum ke sa rai xa ayi masa adalci
Kukan ta cike yake da radadi irin na maraici, da maganganu da basu faduwa a yayin da harshe yayi nauyi, zuci yar masoyan haqiqa da makusanta kadai ke fahimtar hakan.
"Adda, kice hamma tukur don Allah ya aura min musa, musa kadai nake so" tana mai cigaba da kukan ta mai dauke da saqon zuciya,
"Don Allah kiyi haquri boddo, yanxu dai ki bar kukan nan sai muyi magana"
Share hawyen ta tayi cike da tausayin kanta don bata ga wannan tausayin, irin wannan jin qan da ta saba gani gurin adda ta ta ba wannan karon, har zullumi ta shiga amma dai ta sani adda ta ba zata taba goyon bayan a zalunce ta ba, ji tayi hankalin ta ya kwanta ta sauke ajiyar rai, tana mai sassauta riqon da tayi ma addar,
Ruwan dake gefen ta ta bama boddon ta sha sbd dama tana buqatar ruwan, ta sha rana ga zafin dake jikin ta ya mata yawa, ga zafin zuciya ga na rana da ta sha.
Zamewa tayi ta kwantar da kai kan cinyar addan, ita kuma tana shafa kanta cike da tausayawa da rarrashi, rarrashin da tun da aka sanar da ita wannan baqin labarin ba wanda yayi mata irin sa ko kwatankwaci, sai shawara da xata ce an bada wacce take cike gori da isgili.
"Ni kaina bai gaya min xai aurar da ke ba boddo, amma ya fada min ya daura miki aure a lokacin da bakin alqalami ya riga da ya bushe
To mi xan iya yi an daura aure? babu boddo sai dai in miki fatan alkhairi, kinga yanda yanayin jiki na yake ba dadi nake ji ba ko girki ban iya wa sai in su hajjo sun yi su kan sammin ko in sha fura, asibiti sunce wannan watan xan haihu
YOU ARE READING
FUREN TUMFAFIYA
RomanceDuk zakaran da Allah ya nufa da cara..... Tafiyar mai tsaho ce, kuma cike take da qalubalen rayuwa iri iri, sanin kanku ne ruwa da Wuta basa haduwa, haka ma haske da duhu dole sai daya ya rinjayi daya, kwatsam sai qaddarar aure ta fada ma USTAX HABI...