RIKICI

4 1 0
                                    

***
"Nagode da wannan karamcin ustax, ba xan taba mantawa ba, ka min abun da ni bani da damar yi, Allah ya faranta maka yanda ka farantamin abokina, Allah ya biya maka buqatun ka na alkhairi, ga amanar boddo nan
Na sani na hadaka da aiki, ba kuma mai sauqi bane, saboda ita din ba mai sauqi bace ko kadan, dole riqeta sai tsayayyen namiji irin ka, ga tarin yarinta don Allah sai kayi a haquri da ita duk da nasan xaka iya Allah ya dafa maka nagode"

ya qarasa fada idon sa na fito da qwallar farin ciki mai hade da murmushi, wani irin mixed emotion ya ke ciki, amma murna da yake ciki na jin yau ya sauke wani nauyi da ya kamata ya sauke tafi rinjaye.

"Ameen ya rabb"

Itace amsar kawae da ya iya bayar wa ga aminin nasa, bayan ya dago sun hada ido,

Don shi bai dau duk abn da yake fada wani abu mai girma, yarinyar ba matsalar sa bace, duk kuwa dai bai san ta ba, amma baya jinta a cikin matsalolin sa , qaramar yarinya irin wannan ba ya jin xata tabe xa me masa matsala, matsalolinsa sun girmeta, shi yanxu damuwar sa yanda habibty sa xata karbi auren da ma yarinyar baki daya, ba shi da matsala da innar sa, amma yana tsoron rikicin matar sa
Ya sani cewa tana da haquri, amma a alamarin kishiya mata su kan mance da kalmar haquri,
Gashi tun ranar da ya sanar da ita zai nemi auren bai qara samun ta ba a waya,

anya bai yi gaggawa ba kuwa?

"Anya yayi adalci? "

Shi kadai yake saqe saqen sa a zuci

"Za muje ka ganta ne?"

Ko sai ranar da xaku huce,  muryar hamma tukur ta katse masa tunanin sa.

"Mu tafi gida kawae kaina na dan min ciwo".
Murmushi kawae hamma tukur yayi ya kama hanyar gidan sa, dan bashi da abn cewa, ya sani abokin nasa na buqatar lokaci shi kadai ya samu ya yi tunani dan haka ba xai takura shi ba, zai barshi ya huta

Minti goma ce ta kaisu gidan a guesthouse din ya sauka hamma tukur ya qarasa parking space ko da ya gama gurin iyalan shi ya nufa sbd ustax ya samu kadaicin da yake buqata.

Ruwan dumi kawae ya sakar ma kansa sbd zazzabin da yaji yana neman rufe shi, ya sa kaya mara sa nauyi ya sha tea duk da cewa ya samu an kawo abincin amma bashi da appetite, in da ya sha tea din mai zafi sosai anan bacci ya dauke shi.

****
Tabbas ba wasa tsakaninta da baffa, da sai tace zolayar ta yake, kwance take a qasan dakin nasu tantagaryar sumuntin take wannan tunanin dan yau ko yar shimfidar tata da ba komai bace illa tabarma da tsunmokaranta bata samu ba, ji take kamar jijiyoyin jikin ta sun daskare, wani iri, kamar mafarki a sad reality, that feeling you don't even know what you are feeling, tunanin ma bai yiwuwa kamar tana nan amma zuciyar ta bata nan ne dai,

Tunda ta xame hannun ta a na baffa, a jajayen idanuwanta da ba ko kwalla a cikin su, haka tana ganin jiri ta samu ta qaraso dakin nasu take a gurin har yanxu da aka yi maghriba, yinin yau ko abnci bata ci ba, ba sallah bare salati

Kamar an tsikare ta, zumbur ta miqe ta nufi rumfar da ta san war haka goggan na can,

Gaban goggon tata ta je ta zube, fuskar ta dauke da qoqan barar ta a wannan karon ba fitsara sai sanyin jiki, da miqa wuya irin na me neman taimako,

"Gwaggo don Allah ki ce a ware auren nan, ban son sa, ban san shi ba, ni musa nake so wlhy,
Gwaggo bana so".

ta qarashe fada tana me sakin kukan dake cin zuciyar ta da bai samu dafar fitowa ba saboda tafasar da zuciyar keyi sai yanxun.

Shiru gurin ya dauka kowa ya maida hankalin sa ga baddon, dama ba kowa bane a rumfar daga adda hanne (yarinyar goggo mace ta biyu) ita dama ba wai ta cika shiga shirgin da be shafeta bane, bata da hayaniya kamar adda ai kuma ita din ma ba kirki gareta ba da dai Sauqi akan yan uwan nata, sai kuma nafi dake kusa da goggon.

"Mstweee iska na wahalar da me Kayan kara"

Cewar Nafee tana me tashi ta bar gurin.

"Boddo shi aure nufi ne na Allah, kuma rai ne da shi, tunda ki ka ga Allah ya tsara haka ina mai baki shawara ki karbi auren nan ki haqura ki xauna, aure in da rabo akai yunqurin kashe shi kisa yake, kar ki ja min silar ajali, kiyi haquri ki karbi auren nan ki rufawa kanki asiri da maraicin ki,

Kina gani rayuwar nan dama lallabata ake, tunda Allah ya kawo sauqi ya kawo miki miji har gida ba tare da tashin hankali ba me zai hana ki karba?

kiyi haquri kawae tsarin Allah ne, kina gani dai ga su Ai nan mijin suke nema har yau shiru, nima kuma bada ni aka tsara auren nan ba yanda ki ka ji shi haka naji, shi wanda ya miki auren ai ba xai miki zaben tumun dare ba ko ya jefa ki mugun hannu, ki kwantar da hankalin ki

Allah dai ya baki xaman lpy ya sa abokin arziqi ne"

Goggon ta qarasa fada da siga lallashi

Binta kawae boddo take da ido, duk da kalaman gwaggon sun so suyi tasiri akan ta amma dai sun rage mata radadin da take ji, xancen karbar aure kua be ma taso ba

Wani lallausan murmushi ne ya subuce mata wanda be kai zuci ba

"yauwa ko ke fa, dadi na dake fahimta, nima ba son auren nan nake ba amma tunda Allah ya riga yayi hukuncin sa ai ba ka masa shishigi ba sai ka zubawa sarautar Allah ido, ki samu nutsuwa ki je ki watsa ruwa ki dan huta ( ba tayi sallah ba duk da tasan ba ta yin ba amma ba damuwar ta bace)

"Ko ke fa yar Albarka"

Shigowar adda ai ne ya katse xancen, boddon ta tashi kamar kwai ya fashe mata tayi waje, adda ai ta bita da kallon banxa tana me kaiwa xaune gefen goggon

"Lallashin ta ki ke ne? yo kar ma ta haquran mana da ta samu ma aka rufa mata asiri dama ai irin auren da ya dace da ita kenan"

ta fada tana dariyar shaqiyanci.

Dariya goggon tayi

"Abun ai sai da siyasa kin santa da tauri sai an bullo mata ta bayan fage, ni ma da ai naso nasa baffan a kashe auren amma naga ba dabara a ciki, tunda Allah ya kawo mana Sauqi an rage mana nauyi, kuma naji baffan yana kamar malami ne angon ai sai ya dauke ta suyi ta yawon tsangaya"

Fadin gwaggo suna tuntsurewa da dariya.

Jairar yarinya ai ba xata qara kwana uku gidan nan ba Allah ya raka taki gona.

"Kije ki yi sallah ki kai qara gurin ubangijin da baya bacci"

Shawarar da zuciyar ta ta bata kenan ba ko second thought ta nufi bayi dan yin alwala,

Ko da ta idar da sallah kuka take tana neman taimakon Allah har sai da ta ji zuciyar ta tayi sanyi, in da ta idar da sallar nan ta kwanta tana tunanin sabuwar mafita don nutsuwar da ta samu, irin wannan nutsuwar da zuciya take samu bayan sauke farali, kwanciyar hankalin da duk dan adam yake samu bayan ganawa da maqagin sa, irin sa ta samu.

Ji tayi zuciyar ta da kwakwalwarta gaba daya sun bude

"Adda mairama" ita ta fado a ranta sai taji ta samu salama kamar ta samu maqullin dakin da xata rufe matsalar ta.

Ta manta adda mairama qarqashin wani take ita ma sai yanda aka yi da ita

Wanin kuma shine waliy da ya daura mata aure duk idonta ya rufe.....

FUREN TUMFAFIYAWhere stories live. Discover now