RAYUWAR AYRAH part 1&2

28 2 2
                                    

Written 🖊️by
Queen Bee 🐝🥰

Salmerty 💖 😘💯

Mrs Shitu 🥰❤️💜

*YAR LELEN NAZARI WRITERS ASSOCIATION 📘📕🖊️*

*NAZARI WRITERS ASSOCIATION 📘📕🖊️*

_cikakken Nazari Kafin Rubutu Yana Damfare Da Bin Ka'idojin Rubutu🖊️🖊️✍️✍️ _

*Nazari Kafin Rubutu Yana Kayata Duniyar Adabin Hausa✨🤩🌟*

*🖊️Alkami Yafi Takobi⚔️⚔️*

Bismillahir Rahamanir Rahim ✍️✍️

"Ayrah Ayrah bazaki fito nan ba shegiya mai mugun hali irin na uwa da uba sun mutu sun bar min bala'i bazaki fito ba, Mama kyale yar iska mai sufar aljanu bara in shiga na gani ko uwar me takeyi ake kiran ta baza ta ansa ba, yawwa alawiyya ta yar albarka shiga ki fito min da ita,koda tashiga dakin ganin ta tayi akan prayer mat (Dadduma)tana azkar janyo ta tayi au ke ga shegiya kina ji umma na kiranki kin ki amsa wa saboda sa'ar uwarki ce ita,agaban umma alawiyya ta dungurar da ita tace umma kinga yar iska wai sallah takeyi kuma ta idar amma taki amsa kiran da kike mata,Ayrah ce tace umma kiyi hakuri azkar ne keyi ne shiyasa amma dan Allah kiyi hakuri"umma tace au dan uban ki to wa zai dibo ruwan gidan?nice umma dama yanzu zan fito wallahi umma kiyi hakuri, alawiyya ce taje fa mata bokiti tace kije ki dibo ruwan nan kuma yau sai kin cika komai na gidan nan dan uwarki,mikewa tayi ta dauki bokiti tana kuka ta fita ta abakin bohole(tukatuka) ta tsaya ganin layi amma layin ba yawa ji tayi andafa ta joyawa tayi taga kawar ta "Khadija ce "Ayrah yana ga idonki yayi jawur kuka kika yine Ayrah ce ta fashewa da kuka Khadija meyasa umma bata sona sai kace ba matar kanin mahaifi na bah koda yake shima baya sona alawiyya ma bata sona wani laifi na musu haka a rayuwa ta suka tsaneni fashewa tasa keyi da matsanan cin kuka mai taba zuciya,kiyi hakuri Ayrah komai zai wuce inshallah hakuri ta dinga bata har tayi shiru suka dibi ruwan suka tafi koda tashiga gida Baba ta gani yana zaune juyaye ruwan tayi ta tsugunna tace ina kwana Baba ko kallan inda take beyi ba kara gaisheshi tayi ya juyo da fada yace menene mayya kin wani isheni da ina kwana angaya miki ina bukatar gaisuwar ki ne shegiya mai mugun hali mikewa tayi jiki ba kwari taje kara sa debo ruwan.

Umma tace malam ai kamin daidai daka mata haka ta sane ita zata zo ta hura wuta amma ta tsaya tana gaishe ka saboda munafurci,Ni wallahi dan kinki min ne da tuni nakai yarinyar nan gidan marayu amma kince aa, haba malam ai baza ai haka ba kabar ta nan tadinga mana aikin gida,to shike nan tunda haka kika ce.

"Ayrah farace sosai irin farin nan mai kashe ido ga hanci mai tsayi bakin ta dan karami ne fuskar ta ba ta da fadi sosai ga idanuwa manya manya masu daukar hankali atakai ce ma dai kamar ta daya da buzaye,bata da hayaniya ko kadan, Khadija kawar ta ce tun suna primary school kuma islamiyyar su daya shiyasa Ayrah bata boye mata komai haka itama bata boye mata komai. Akasin Alawiyya bata da kunya ko kadan iyayen ta ma bata raga mawa ba gata bawani kyau ba amma sai iyayin tsiya jin kanta take kamar yar governor ko a makaranta bata da kunya shiyasa ba ko da yaushe take zuwa makaranta bah islamiyya dama ba zuwa take yiba tun suna class 4 tadaina zuwa.

Koda tagama diban ruwa wuta ta hura ta dakko tuwo tayi warming (dindime) sannan tasa ruwan wanka sannan taje kofar dakin umma tace,tace umma nagama dindumen tuwon,kisawa alawiyya da baban ku sannan kici roguwar,toh umma tasa ma alawiyya da baba akula sannan tazuba nata taci ta wanke kayan da akaci abincin dare tayi sannan tashiga wanka tafito cikin uniform dinta na makarantar Boko,umma zan tafi makaranta,to na rike miki kafa ne shegiya kawai,mikewa tayi ta tafi makaranta.

LABARIN IYAYEN AYRAH ✍️

Garin kano unguwar dabai

Malam Abdullahi Muhammad da Usman Muhammad(Baba) wa da kani ne tun suna kana na iyayem su suka rasu suka bar musu gadon gida da shagon da mahaifin su yake saida kayan hatsi Abdullahi ne babba saboda haka shiya cigaba da zama a shagon yana lura da Usman sosai yakai shi gurin aikin Kanikan ci shikuma yana lura da shago alhmd suna samin rufin asiri.

Mahaifiyar Ayrah asalinta yar Niger ce agarin Niamey sunan ta Amina tana zaune tare da maman ta ne a Niamey dalilin zuwan ta Nigeria bayan rasuwar mahaifiyar ta kuma bata da wasu yan uwa hakan yasata zuwa Nigeria garin Kano tana aiki agidan wata mata sosai matar take kula da Amina saboda yadda take da hankali.

Awata ranar alhamis ne Amina taje siyan gero shagon Abdullahi anan ne fah Abdullahi yace yaga mata tundaga ranar Abdullahi yake bibiyar ta har ta yadda tafara sonsa sona son junan so sosai koda Amina tabawa Abdullahi labarin ta bai damu ya ce bavkomai ahaka har aka daura musu aure inda shikuma Usman yasamu wata yarinya mai suna falmata(umma) abinci take siyar wa abakin garage(gareji)din su Usman bata da kunya ko kadan Usman yanemi auran ta aka bashi saboda suma iyayen ta ta ishe su tunda akai auran Usman da falmata gidan ya lalace tunda gida daya suke zaune falmata tana kishin sauri da Amina,amma Amina bata kula ta shi ke karawa falmata jin haushin ta.

Amina ce tafito daga dakin ta tana amai koda sukaje hospital ana ma Amina test aka ga tana da ciki 2 month falmata taji haushi sosai har saida tafada ma Usman ce mata yayi ai murna yakamata kiyi ko kema Allah yaba mu namu mai albarka ka,ko kadam bahaka falmata taso bah saboda haka tasa mu kawar take gaya mata nan kawar ta tace mata suje gurin boka kawai tako yadda suka tafi wani daji baka jin komai a dajin sai kukan tsuntsaye amma su ko tsoro basa ji,wata murya sukaji tana ce ku taho da bayaya aiko suka juya suka taho da da bayaya har zuwa wata bukka suka shiga zama suka yi bokan ya daka musu tsawa bai sai kunce komai bah munsan abinda ke tafe daku baza ku iya wa Amina komai ba ko yarinyar dake cikin ta saboda itama tana da masu kareta sai dai muyi wa mijin ki da dan uwansa zamu sama Abdullahi ciwo har ya mutu shikuma mijin ki sai yadda kikayi dashi kutashi ko tafi tsinanun Allah yan wuta kawai hhhhh.

Tun ranar da falmata suka dawo daga gurin boka Abdullahi ya kamo da wani matsanan cin ciwo ga dan uwanshi baya kula dashi abinci daza suci dakyar suke samu ranar da Amina ta haihu a ranar Allah yayi mata rasuwa bayan ansa ma jaririyar suna Hauwa amma suna kiran ta da Ayrah bayan kwana 7 Abdullahi shima ya rasu matar data dauki Amina ne ta ke shayar da Ayrah.

RAYUWAR AYRAHWhere stories live. Discover now