RAYUWAR AYRAH part 13&14

5 2 0
                                    

Written by

Queen Bee 🐝❤️💜

Mrs Shitu 🥰❤️💜

Salmerty 💖💜

*Yar Lelen Nazari Writters Association ✍️🖊️*

*Nazari Writters Association✍️📘*

*Cikakken Nazari Kafin Rubutu Yana Damfare Da Bin Ka'idojin Rubutu ✍️🖊️*

*Nazari Kafin Rubutu Yana Kayata Duniyar Adabin Hausa 🌟✨*

*🖊️✍️Alkalami Yafi Takobi ⚔️

*GARGAD'I* wannan litttafi k'irkirarran labarine ban yishi dan wata ko waniba idan yayi kamanceceniya da rayuwar wata ko wani Arashi ne"aguji sauyashi ta kowace siga sbd hakk'in mallakata ne.

Dedicate to All my fans 💖💔

Wacece Pretty?

Pretty da janan sun hadu ne a university inda pretty takasance yar lesbian kuma tana bin maza tun haduwar pretty da janan pretty taci alwashi koya mata lesbian saboda janan ita bata lesbian amma tana bin maza da shayeshaye

Awata ranar Monday ne pretty takira janan tace tazo gida zasuyi magana janan koda taje ta tarar da pretty daga ita sai pant and bra bata damu takara sa tace yane sisy maganar me zamuyi bata bata amsa ba tafara kissing din ta ina ganin haka nafice daga dakin ina daga waje inajin sunata wasu surutai koda na koma dakin janan ce rugume da pretty tace,my love dama haka less yake da dadi kuma dama ke yar lesbian ce,eh tunda naganki naga kina matukar burgeni shiyasa nace saina koya miki kema kiji dadin da akeji,uhmm ina sonki my pretty.(Allah katsare dukkan nin musulmi daga wannan dabi'ar ta yahudawa suma masu yi Allah yashirye su ameen)

Ayrah ce keta kici kicin daura bokitin kunu akanta tana daurawa tace umma natafi,bata amsaba dama itama bata sa ran zata ansa ba inda sabo tasaba gwara yanzu ma tadan samu sauki saboda tana zuwa mata talla tana bata kudi kuma Allah yanasa tana siyar wa tunda kunun bai wuce na 1000 shiyasa take samu ana bata abinci amma da wani lokacin ba'a bata abincin ma gaba daya saidai taje gidan su Khadija taci.

Tana zaune inda take siyar da kunun ta wani dan shayeshaye yace"ke abani kunu na naira 50 bata kalle shiba ta dakko tamika mishi yatafi.

Wani saurayi ne tun zamanta yake kallon ta yake lashe baki kamar maye yana zaune da abokansa yace baba wallahi wannan yarinyar ta hadu fa"eh kabari anjima tana wucewa ta wani lungu sai mubita mu kamata ko ya kace"kai baba shiyasa nake sonka ai naga kunun ma yakusa karewa bara muji ra ta ko"okay.

Safwan ne yake driving Ajmal kuma yana mazaunin gaba yana danna wayar shi safwan ne yace"yaya unguwar dabai zamuje ko?eh can zamu daganan ba wanda yasake magana acikin su.

Hada kudin kunun tayi ta tashi zata tafi tana tafiya a hankali tana zuwa lungun taga su baba suna ta busa sigari 🚬 ratsa su tayi zata wuce suka kamota "ina zakije yanmata ai yau kinshiga koma ta"dan Allah kuyi hakuri kabarni intafi "hhh haba ai yau baki ba tafiya saina biya ma kaina bukata ta.

Safwan ne yazo wucewa tawani lungu yaji kamar kukan mace shima Ajmal yaji amma ya basar safwan ne yayi reverse da motar nan ko yaga wasu samari nata kokari cirews wata budurwa hijab amma taki yadda parking motar yayi ya fito Ajmal ko kin fitowa yayi amma hankalib shi na gurin zuciyar shi nata bugawa koda safwan yashiga lungun kokarin hanasu yake amma ina sunada yawa Ajmal ne yafito cikin zafin rai yayi hanyar lungun.....................

*NASIHA ZUWA GARE KU ƳAN LESBIAN, ƳAN MATA DA SAMARI (5)*

*YA KE ƳAR UWA, MATAR AURE KIKE KO BUDURWA KO BAZAURA, KU GU JI SAKA PICTURES NAKU AKAN DP*

Jan Kunne Zuwa ga *Ƴan LESBIAN* da Suke Kokarin Ruguza mana tafiyar mu ta Da'awah da Yin Wa'azi da Kuma Sada Zumunci a WhatsApp. Wallahi Ku ji Tsoron Allah Kuyiwa Kanku Hisabi Tun Kafin Allah Ya Muku, a Ranan da Dukiyar Ki, Ƙuɗi, Mulki, Matsayin, Muƙami. Duk Ba Za Su Tsinana Muku Komai ba Sai Faɗawa Cikin Tarkon Halaka.

Ƴan Mata da Matan Aure Zaurawa, Ku Gu Ji Sanya Hotunan Ku Akan DP Naku, Domin Yawan Sanya Hotunan Ki, Ki Cire Wannan Ki Sa Wancan a Kullum Sai Kin Chanja hoto a Dp Kin Yafi Sau 2, Kina Sani Cewa Yawan Saka Pics Barkatai Akan Dp yanada Matukar illa Gare ku Mata, Musamman a Wannan Zamanin da Muke Ciki. Yanzu Allah ya Kawo mu Wani Zamani da Hanyoyin Ɓarna Sun yi Yawaita Ƙofofin Halaka Sun Yawaita sai ɗai Kawai Wanda ya Tsare Shi.

*Ƴa LESBIAN* Suna nan a Cikin Groups naku ba su Yin Posting, Ba Su Yin Magana Kullum Suna bi Suna Ɗuba Dp Na Members ɗin Group Yayin da Kika Saka Pic Naki Mai Ƙyau Sai Suyi Notice ɗin ki Suna Biyayyar Wata rana Ƙwasam Sai Ki ji ai An yi Miki Magana ta Private ke Baki San Waye bane Amma Su Sheɗanun *Ƴan LESBIAN* Sun San ki Kuma Duk Pic naki Sunan tare dashi Tili-tili Babbar Burin Su ya Za'a yo Su Ƙulla Qawance dake ɗan Kisa ba Dasu Kuma Su San inda Kike da Kuma Ra'ayin ki.
         Binciken da Muka yi ya Nuna Cewa Maza ne Suka Fi Aikata Wannan Ɓarnan, Sannan Akwai Matan Aure ma Masu Tura Hotunan Tsiraicin Mata da Maza da Videos da Stickers na Tsiraici, Sannan Akwai Ƴan Mata Dukka a Cikin Wannan Halakan, Suna Shiga Group ɗin da Aka ce Mata Zallah ne Su ɗinga Biyayyar Dp ɗin Mata danganin Pic ɗin Su idan Kina Yawan Saka Pic ɗin Banza to Ke ce Zaki Zama tasu Sai Su fara Bin ki ta Private, toh Wallahi Wajibi Ne Gare ku Matar Aure kike Ko Budurwa ko Bazaura Ku Kiyaye Saka Pic ɗin Banza Akan Dp naki Ki san Irin Pic ɗin da Zaki Rika Sakawa a Dp Naki Karki Manta fah Pic a Internet yakan Shiga inda bakiyi Sammanin Shigar shi ba a Duniyar nan. Ina Amfanin Kin Sa Pics naki an Wuce dashi ana ta Yawo dashi?

Wallahi Mu Farka Mu San Wannan Ɓarna, Wannan Ɓarnan da Ake Aikatawa a Yanzu ba Maza ba Mata ba Duk Aikatawa Ake yi Ko Tsoron Allah Babu, Kuma *Ƴan Lesbian* Sun yi Garkuwa da ita Abinda Suke Aikatawa Kenan Yanzu Biyayyar Mata suke yi ta Private Wallahi Kar ki Yarda Ki ce Yau Zaki Ƙullah Qawance da Wacce baki San ta ba, Kar ki Taɓa Yarda Ki Ƙullah Abota da Wanda Baki San Shi ba, Ki San da Waye Kike Yin Chat dasu Mata ne Ko Maza, Ki San Kuma da Waye Zakiyi Abota, Ki Gujewa Faɗawa Cikin Halaka ko Faɗawa Wutar Jahamnama. Annabi Muhammad Mai Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata Agare Shi Yana Cewa, Ɗayan Ku Ya Ɗuba da Waye Yakamata Yayi Abota.  Bawai ki Tsaya Ko Naki ke Baki Ƙin Kowa ba.

Yana ɗaya Daga Cikin Ɓarnan da *Ƴan Lesbian* Suke Aikatawa a Yanzu, Suna Bincikar Duk Wani Sirrin da Kuma Mijin ki Hartakai ga Suna Ɓaki Shawaran Banza Suna Gayyatar ki izuwa Faɗawa Cikin Halaka ke Kina Ganin Kamar Taimakon ki Suke yi, Suna Miki Tayin Saurayi Wanda Zai ɗinga Zuwa Gidan ki idan Mijin ki ya fita Aiki. Wal'iyazu Billah. Matar Aure Ku Ji Tsoron Allah Wallahi Ku Ɗena Shiga Cikin Group Kuna Hiran Jima'i da Kuke Yi da Mazan Ku, Ku Ɗena Shiga Cikin Group Kuna Cewa a Koya Muku Yadda Ake Yin Jima'i, ku Ɗena Shiga Cikin Group Kuna Ɓaje Sirrin Mazan Ku, Yin Haka Haramun Ne, bayan Haka ga illar da Zai Faru dake. Wajibi Kuyi Gaggawan Tuba Zuwa ga Allah. *Ƴan Lesbian* Suna Bincikar Ma'amalar ki da Mijin ta Aurw, Yayin da Suka Ji Cewa Kin Fito Kina Bayani a Cikin Group Mijin ki Baya iya Gamsar dake ta Fannin Jima'i, Sai Suyi Miki Tayin Wani Namijin, ko Kuma Wanda Kike Chatting dashi Yace Yana Son Ki.
    Wallahi Mu ji Tsoron Allah, Ku Rike Sirrin Mazajen Ku, Ku Sani Cewa Shi Zaman Aure da Kuke Yi Zama ne na Ibadah, Ibadah ce Kuke yiwa Ubangijin ku, Kamar Yadda Kuke Yin Sallah Kuke Yin Azumi Kuke Neman Lada a Wajen Allah Haka Zaman Auren ki Yake.  Kada Ki Ƴarda Wata Sha-Sha-Shan Banza ba Gidajiya Wacce ko bata dashi Kuma bata San Darajar Auren ba Bata san Ɗaɗin Auren ba, bata San Ni'imar da ya ke Cikin Auren ba, Wai Ki Ƴarda ta Ƙashe Miki Auren ki Kuma ta Jefa Rayuwar ki a Cikin Halaka daga Karshe ta Gudu ta Ɓar ki Cikin Kogin Nadama da Yin Danasani a Rayuwar ki.

Wallahi Musani Cewa Allah Ya La'anci Macen da take Fitar da Sirrin Mijin ta, Allah ya La'anci Macen da take Cin Amanar Mijin ta, Kenan Duk Matar Auren da Zata Shiga Group ta Baje Sirrin Mijin ta ko tace Mijin ta Baya Gamsar da ita Ko Kuma a Koya mata Yadda Ake Jima'i Domin ta San yadda Zata Tarɓi Oga, Ki Sani Cewa Kina Cikin La'anan Allah. Ki tuna fah Zaki Mutu Zaki je Ki Haɗu da Ubangijin ki, Shin da Me Zaki Tsirar da Kanki daga Wannan Ranar dake Tafe? (( Rana Ce da Wani Rai Baya Iya Mallakar Kome Domin Wani Rai Al'amari, a Ranan nan ga Allah (ɗai) Yake. Duba Cikin (Al-infitaar 19)
      Wallahi Ƙuɗi, Mulki, Matsayin ki, Muƙami, Ƙyan Fuskar ki ko Halittar Ki, Yawan Ɗangin ki, ko Masoyan ki, Ba Zasu Ƙuɓutar dake ba Face Ƙyawawan Ayyukan ki da Kika Aikata Su a Gidan Duniya, Gidaje Guda Biyu Ko Wuta Ko Aljannah Dolen ki Zaki Tsinti Kanki a Cikin ɗaya yi Kokarin Zama Musulmar Ƙwairai Domin Samun Rahamar Allah Zuwa Aljannah.

Ya Allah Ka Tsare mu ga Faɗawa Cikin Halaka, Ya Allah Ka Tsare mu daga Shiga Jahamnama, Ya Kasa Mu Cika da Imani Ameen.

Edited by
Queen Bee 🖊️
Mrs Shitu 🥰

RAYUWAR AYRAHWhere stories live. Discover now