RAYUWAR AYRAH part 3&4✍️

19 1 0
                                    

Written by

Mrs Shitu 🥰❤️💜

Queen Bee 🐝❤️

Salmerty 💖💜

*🖊️✍️Yar Lelen Nazari Writters Association ✍️📘🖊️*

*✍️NAZARI WRITERS ASSOCIATION 📘🖊️*

*Cikakken Nazari Kafin Rubutu Yana Damfare Da Bin Ka'idojin Rubutu✍️🖊️*

"Nazari Kafin Rubutu Yana Kayata Duniyar Adabin Hausa🌟✨ *

Tunda Ayrah takai shekara 6 umma tace batasan wani zance bah sai dai baba yaje ya dakko Ayrah daga gidan awar rikon Amina dalilin dayasa umma cewa a anso Ayrah saboda bokanta yace mata in har Ayrah tana gidan nan to zata samu rayuwa mai kyau,haka koh akayi baba yaje ya dakko ta tunda aka dakko ta bata kara samun hutu ba itace dibo ruwa akai komin nisan guri Ayrah ke zuwa makaranta ma dakyar umma tabar ta take zuwa shima bata zuwa da wuri sai ta gama aikin gida wani lokacin ma ko abinci bata bata sai dai taje gidan uwar rikon mahaifiyar ta hajiya fatima taci sannan ta wuce makaranta a haka har takai shekara 16 inda suka taso tare da alawiyya wacce arana daya aka tashi aka ga umma da cikin alawiyya sam bata kama da da baba(Usman) itama alawiyya bata san Ayrah ko kadan saboda tafita kyau shiyasa ta tsane ta.

MUDAWO LABARI ✍️✍️

Nasarawa estate unguwa ce ta masu kudi acikin jahar kano wanda unguwar ta tara yan kasuwa,yan siyasa,da masu aikin government daka shigo zaka gane unguwa ta masu ji da kudi ce.

Wata mota ce kirar parado baka har daukar ido take tashiga wani katon gida irin gidan da ake cewa aljannar duniya wani matashi ne yafito bazai wuce shekara 35 ba yana tafiya kamar bazai taka kasa ba kyakkyawa ne ajin karshe fari ne amma ba sosai ba yana da dogon hanci ga gashin kanshi kamar na yan India fuskan nan a murtuke ba fara'a juyawa yayi yace safwan baza kafi to bane wanda aka kira da safwan ne yace sorry yaya Ajmal gani nan,dama kana ganina nafito amma ka tsaya danna waya?ya hakuri bazan kara ba, shiga cikin gidan yayi safwan na bayan shi,laaaa mommy yaya Ajmal sun dawo da yaya safwan,wata mata tafito tasa Swiss lace blue doguwar riga tayi kyau sosai tace, hmmm amrah kenan ai dama ke kadai ce bakisan yau zasu dawo ba amma kowa yasani, haba mommy shine ban sani bah kinsan yadda nayi missing din su yaya kuwa,inji amrah,yar kanwar mu muma munyi missing naki sosai Ajmal ko bai ma kalleta ba ya wuce ya zauna akan kujera mommy ina wuni,lafiya qlau ya hanyar ya aikin, lafiya qlau ina daddy dazu munyi magana dashi nace masa muna hanya yace shima yana hanya zuwa gida,eh yadawo yana bedroom din shi yana wanka yanxu zai fito, okay bara naje nima nayi wanka anan yabar mommy da safwan da amrah suna hira.

Page 5&6✍️

stair ya hau yashiga wani daki komai na dakin Ash and white color ne wani corridor yashiga wanda yasa dasa da bedroom din shi wanka yashiga ya kusan 30 minutes sannan yafito daure da towel a kugun sa dawani dan karamin towel a hannunsa yana goge sumar kanshi wacce daga gani kasan tasha mayuka masu tsadan gaske karasa wa gaban dressing mirror yayi ya shafah lotion da turare mai dadin kamshi gaban drower ya karasa yasa white t-shirt and black jeans kayar sun matukar amsar sa phone dinsa ya dauka kirar iphone 16 pro da Samsung Galaxy S10 ya sakko dining area ya nufah a lokacin safwan shima yayi wanka ya canza kaya sai amrah dake ta zuba surutu yana zuwa tayi shiru,kije daki na akwai akwati ki dauka naki ne, thank you Yaya Ajmal, safwan ne yace nima kije daki akwai wani akwati shima naki ne mikewa tayi tana jin dadi taje dakko akwatin,wani dan karamin box Ajmal yafito dashi yace mommy wannan naki ne budewa tayi taga sarka mai kyau da gold,kai Ajmal wannan sarkar tayi kyau Allah yakara arziki da ameen suka amsa daddy ne ya sakko daga stair ya zauna Ajmal da safwan suka gaisheshi ya ansa cikin jindadi da kaunar Yaya nasa.

Alhaji Muhammad Ali ya kasan ce dan kasuwa mai tarin arziki sosai yana da mata guda 1 Hajiya Hafsat da yaransa guda 3 Ajmal, safwan,Amrah.

Safwan ne babba baya da hayaniya ko kadan gashi muskilin ne na karshe baya daukar raini ko yaya yake saboda haka ne koda Amrah baya wasa akasin safwan mutun ne mai wasa kuma ba ruwan sa da muskilan ci amrah ce karama dan yanzu 16 year take tana ss1 yanzu a Hamdan Academy kano.

Ayrah ce ke wanke wanke tana ta sauri saboda lokacin makaranta yayi dan karfe 7:30am tayi tagama wanke wanke taje ta sa uniform dinta zata fita Kenan ji tayi ance ke dawo nan kara sawa tayi tace gani alawiyya ce ta watso mata kayan wanki tace ki wanke min anjima zansa in fita dasu,dan Allah kimin hakuri inna dawo zan wanke miki dauke ta tayi da wani wawan mari ina wasa dake ne mara kunya har zance kimin wanki kice sai kin dawo in kikayi wasa wallahi baza ki kara zuwa makarantar ba,kiyi hakuri bara na wanke miki kwashe kayan tayi ta wanke bata gama bah sai karfe 8:10 sannan ta tafi makaranta tana zuwa ana tsaran late malam ne yace yau ma kin sakeyin late koh, 😐 dan Allah kayi hakuri wallahi nashirya zan fito aka sani wanki kayi hakuri,tashi ki tafi amma gobe in kikayi late bazan kyale kiba hanyar ss1 ta nufa tashiga class din su kusa da Khadija ta zauna Rubutu ✍️ tafara saboda har anyi nisa.

Please 🙏 🥺 kudinga following dina please 🥺 🙏

*🖊️Alkalami Yafi Takobi⚔️*

*🖊️Alkalami Yafi Takobi ⚔️*

RAYUWAR AYRAHWhere stories live. Discover now