RAYUWAR AYRAH part 7&8

10 0 0
                                    

Written by

Queen Bee 🐝❤️💜

Mrs Shitu 🥰❤️💜

Salmerty 💖💜

*Yar Lelen Nazari Writters Association ✍️🖊️*

*Nazari Writters Association✍️📘*

*Cikakken Nazari Kafin Rubutu Yana Damfare Da Bin Ka'idojin Rubutu ✍️🖊️*

*Nazari Kafin Rubutu Yana Kayata Duniyar Adabin Hausa 🌟✨*

*🖊️✍️Alkalami Yafi Takobi ⚔️

Ajmal ne ya sakko daga stair yana waya yagama haduwa ya saka wani yadi milk color da hula akan sa gashin kanshi yayi kyau sosai direct dining area ya nufah safwan ne da amrah da mommy da daddy kowa yana cin abinci shi cikin natsuwa amrah ce take ta zuba surutu yana zama yace good morning daddy, morning son yawwa yau za kaje gidan Alhaji Adam ka kai masa file dinan yau bazan samu fita ba, okay dad inshallah inna fita office kan nadawo gida zanje, okay,yaya dan Allah yaya Ajmal tunda yanzu zaka fita kayi dropping dina a school please 🥺,ko kallan ta beyi ba,hakan ya sata yin shiru.

Yana gama cin abinci shi yace oya tashi mutafi, thanks Yaya, mommy natafi, Allah ya tsare son da ameen ya amsa suka tafi shima safwan mikewa yayi ya musu sallama yata fi office din shi,yana yin dropping amra a school ya wuce office sai 4:00pm
Ya dauki hanyar Tudun Yola a wani katon gate gidan ba laifi ya hadu horn yayi aka bude masa gate yashiga da motar sa yayi parking fitowa yayi yana tafiya a hankali ya karasa inda wani dattijo sa'an daddy ne mutumin yana rike da jarida a hannunsa ta daily trust yana karantawa,Brk da hutawa Baffa dagowa yayi yace Ajmal har ka iso kenan,eh Baffa ga file din, okay Allah maka albarka, ameen Baffa wata badurwa wace tafito baza ta wuce shekara 25 ba hannun ta dauke da ruwa da chi exotic da cup(Kofi) tana tafiya tana rangwada ta karaso tace Baffa gashi,okay zuba ma yayan naki kallon shi takeyi kamar ta cinye shi gaba daya ya tafi da imanin ta, Baffa nagode basai nasha ba daga office nake alhamdulillah,
Bakin shi kawai take kallo yadda yake magana kace ba shine yake maganar ba,tohm Ajmal ka gaida daddy naka, inshallah sai anjima,har yabar gurin tana Duniyar tunani sai da Baffa yace janan lafiyar ki kuwa, lafiya lau Baffa ta tashi tashiga cikin gida,Baffa koh tsaf yagama karantar yar tasa murmushi yayi yaci gaba da karan ta jarida.

Page 9&10

Tana shiga gida ta kwanta kan cinyar mama tana murmushi,mama tace janan lafiyar ki kuwa,mama wanene Ajmal,dan gidan daddy ne aminin Baffan ki,dagaske?eh zan miki wasa ne, mama wallahi yana da kyau, iyyye janan yana da kyau a ina kika ganshi to gurin Baffa yazo,okay,taci gaba da murmushi mama ta fahimci abinda janan takeji dan haka itama murmushin tayi.

Janan itace ya tilo guda 1 agurin Alhaji Adam da matar sa Hajiya maryam suna san ta sosai hakan yasa suka shagwaba ta da kudi da jindadin rayuwa da kuma boko dan islamiyya bata zuwa tun tana class 2 lokacin da aka dake ta bata kara zuwa ba bata jin magana ko kadan tunda tafara university ta hadu da yayan masu kudi irinta suka kara bude mata ido sune zuwa club gurin party duk wani guri dai na iya shege na yayan masu kudi zakaga janan,Baffa baisan tana zuwa irin guraren nan ba amma mama tasani kuma bata hana ta zuwa acewar ta zata daina da tayi aure.

Ranar Sunday(lahadi) Ayrah ce take ta aikin gida tana gamawa umma tace ke shegiya zo nan,gani umma,yau talla zaki je na kunu,umma talla kuma?eh tallah ko bazaki bane dan ubanki?zani,to maza kije ki hura wuta kidama,tohm umma hura wuta tayi ta dama kunun sai kamshi yake na kayan kamshi ta dakko bokitin penti tafara kullawa a leda tana sawa a bokitin sai da tagama kullawa duka tace umma nagama, yawwa ko kefah yanzu jeki shirya ki fito ki tafi,tohm umma fitowa tayi tashirya tasa hijab din duk yaji jiki amma hakan bai hana kyanta fitowa ba dauka tayi tace natafi umma,kada ki kuskura ki tabamin ko biyar acikin kudina kuma ki tabbata kinsiyar dashi duka kin jini koh?eh inshallah.

Bata dawo bah sai ana kiran sallar Azahar Allah ya taimaketa ta siyar duka tana shiga gidan da sallama abakin ta Alawiyya ce ke zaune amma bata amsa ba dakin umma tashiga tace umma nadawo ga kudin,ah ah har kin dawo bani kudin,gashi irgawa tayi taga sun kai tadinga murna lallai nasamu sana'a yau akwai cin dadi alawiyya zo kije kasuwa kisoyo min nama, okay bara nagama dauraye jikina,umma bara ne nayi sallah,sannu lemamiya je kiyi tunda nidai kin kawomin kudi ai shikenan in kin idar saiki jajjage kafin alawiyya ta dawo ki dafamin nama kuma kada ki kuskura ki cimin nama, tohm tashi tayi taje tayi alwala tai sallah tana addu'a tana kuka tana fadama Allah bukatun ta.

11&12

Can nahango alawiyya a wani daki tana fadin wallahi dan lami kabani kudi na ka ce nazo inmun gama zaka bani 5k amma zaka ce yanzu 3k zaka bani wallahi baka isa bah haba alawiyya zan cika miki 2k din yanzu dai ki ansa wannan 3k din, wallahi ranar Monday zaka bani 2k daga haka ta tafi kasuwa siyo naman.

Koda tadawo Ayrah har tayi komai naman kawai take jira tana shigowa ta wulla mata ledar gayinan,dauka tayi ta wanke shi tass sanann ta daka citta,kanin fari tasa a tafashen nan kashi yacika ko ina tayi ferfesu mai dadi tana gamawa ana kiran sallar magrib tasauke tukunyar ta kaiwa umma taje tayi salla tasa tuwo tana ci,umma ne da baba agefe da alawiyya suna cin naman data dafa sai da suka ci ma ishi sannan suka bata sauran dan kadan ne ma ba yawa ta ansa taci tana gama ci tace umma sai da safe,ko kallan ta batayi ba dama inda sabo ta saba dan haka ta tafi taje ta kwanta abinta tayi addu'a bacci.

RAYUWAR AYRAHWhere stories live. Discover now