Written by
Queen Bee 🐝❤️💜
Mrs Shitu 🥰❤️💜
Salmerty 💖💜
*Yar Lelen Nazari Writters Association ✍️🖊️*
*Nazari Writters Association✍️📘*
*Cikakken Nazari Kafin Rubutu Yana Damfare Da Bin Ka'idojin Rubutu ✍️🖊️*
*Nazari Kafin Rubutu Yana Kayata Duniyar Adabin Hausa 🌟✨*
*🖊️✍️Alkalami Yafi Takobi ⚔️
*GARGAD'I* wannan litttafi k'irkirarran labarine ban yishi dan wata ko waniba idan yayi kamanceceniya da rayuwar wata ko wani Arashi ne"aguji sauyashi ta kowace siga sbd hakk'in mallakata ne.
Dedicate to All my fans 💖🥰💃
Page 15&16
Lungun yashiga yaga safwan yana ta kokarin kwace Ayrah a hannun su baba amma yakasa saboda sun masa yawa saida yakusan 5 minutes sannan yaga safwan yaka sa a hankali yake tafiya saboda yadda kirjin sa ke bugawa yana karasawa ya janye safwan baya yafara dukan su baba kamar dan sanda singham dasukaga yafi karfinsu suka gudu.
Ayrah kuwa tuni tafara jin jiri na diban ta ta zube sumamma safwan yakara sa dasauri ya tare ta dakko ta yayi
Yayi hanyar mota da ita yana kokarin bude murfin mota Ajmal me yace"safwan me kake kokarin yi"zamu taimaka mata ne mukaita hospital"what bamun taimaketa ba yanzu kuma wani hospital zamu kaita"haba yaya bakaga ta suma bane please ka taimaka kabari akaita hospital
Shiru yayi yace okay but kasata a baya"okayHanyar MURTALA MUHAMMAD hospital suka nufa direct suna zuwa aka kaita emergency safwan ne yashigo cikin hospital din shikuma Ajmal yana mota
Doctor ne yafito daga dakin da aka kwantar da Ayrah yaga safwan yace masa ya bishi office
Safwan na shiga office din doctor yace zauna zama yayi yana facing din doctor din dagowa yayi yacire farin glass din face din shi yace kaine wanda ka kawo patient dinnan"eh nine"okay patient din daka kawo taji zoro ne shine abinda yajawo ta sume but bayan wannan tana da wata damuwa saboda yadda zuciyar ta ke bugawa I think wani abu na damunta inshallah gobe zamu iya sallamar ta"okay thank you doctor"yawwa akawo mata kayan da zata canza saboda naji kinta sun yage da kayan fruit maybe ta iya ci sannan zan rubuta ma drugs din da a siya mata"okay thank you...
Gurin parking space din hospital din yakarasa yaga ba Ajmal aranshi yace kai yaya Ajmal you have alot of problem gate ya nufa abakin titi yatare keke napep yau
Ganin magrib yayi yasa umma cewa "ko ina wannan shegiyar yarinyar ta tsaya wallahi ta dawo sai na karya abar banza"alawiyya ce tashigo ba sallama ta dauki buta tayi bayan gida saida takusan 10 minute sannan tafito umma nata zagaye tsakar gida alawiyya tace"umma lafiya kike ta wani zagaye tsakar gida sai kace me jin Kashi"hmmm ke alawiyya wannan yarinyar ce har yanxu bata dawo ba tunda ta fita da kunu"to umma mai ya dameki kila ma tana can yawon ta Allah sa daga haka kada ta dawo gidan muma ma huta"ke kudin na fa ai wallahi tazo taban kudi na saita koma yawon ta"hmm kedai kika sani umma to me kika dafa"ban dafa komai ba dama Ayrah ke dafawa kuma bata dawo ba yanzu kinga sai kishiga kitchen kidafa"kikace me?nace kishiga kitchen kidafa "ahayye lallai umma ai wallahi sai dai a kwana da yunwa nice zan muku girki ashe baza kuci ba ni yanzu ma bara nazo nafita gidan tunda baki girka ba"to shikenan ni bara na girka amma yau in wannan yarinyar ta dawo saina mata hukunci mai kyau"ni natafi "to kidan taho da tsiran nan da ake siyo miki"naji
Har alawiyya takai zaure baba yafito daga daki yace"alawiyya zonan ina zaki ana shirin kiran sallar isha'i "aa malam kabar ta tafita ni na aike ta gidan aminiya ta kinji alawiyya tafiyar ki"zai kara magana umma ta zabga mishi harara sai yayi shiru yafita zuwa masallaci...
A kofar gida mai napep ya sauke safwan dubu daya yabashi yace gashi"aa mai gidan kudin ka dari biyar ne ba dubu daya ba"ok karike canji"nagode Allah kara arziki duniya da lahira"da ameen ya ansa yashiga gidan koda yashiga mommy yagani zaune a parlour tana danna laptop yace"mommy sannu"yawwa safwan wai ina katsaya naga Ajmal ya dawo"hmm mommy kinsan halin yaya Ajmal wata yarinya muka taimaka mawa shine muka kaita hospital wai kafin na fito harya tafi"to yarinya kuma"eh mommy wallahi yarinyar tana cikin damuwa wasu samari ne suka tare ta a lungu suna neman mata rape(fyade) shine muka tsaya agurin saboda suna dayawa nakasa saida Yaya Ajmal yashigo koda suka tafi yarinyar ta sume wallahi taban tausayi"amma banji dadi ba wallahi yanzu yarinyar tana wani hospital?MURTALA MUHAMMAD hospital"okay bayan isha'i sai muje muga jikin ta ko"to bara nayi wanka naci abinci"okay itama za a hada mata abincin da za a kaimata..
Janan ce kwance acinyar mama tana danna waya kamar an tsungule ta tace"mama kinma baffah maganan Yaya Ajmal"aa yau dai zan masa magana"mama dan Allah kimasa magana wallahi ina sonsa sosai"to naji zan masa magana shikenan"eh ai gara inba haka ni dakaina zance masa ina sonsa wallahi
Bude ido take a hankali tagan ta akwance a asibiti shiru tayi tana tunanin mai yafaru da ita ne a hankali ta tuna abinda yafaru tashi tayi tasaka hijabin ta tafara dube dube taga ba kudin umma na kunun ta ihu tafashe dashi saiga nurse ta shiga tana riketa tana fisgewa tana cewa wayyo yau nashiga uku da umma wallahi sai ta kasheni wata nurse ce tace "je ki kira doctor"ok..
Mommy ce tashirya ita dama Amrah tace safwan muje ko"ok zasu fita kenan saiga Ajmal ya sakko daga stair yace"mommy ina zakuje haka?zamuje hospital ne"hospital kuma gurin wane?gurin wannan yarinyar da muka taimakawa dazu"okay"kai bazaka bane?eh mommy"okay mota suka nufa sukayi tafi asibiti sunayin parking Amrah ta dakko basket din abinci suka shiga dakin da Ayrah take ganinta sukayi doctor nata bata hakuri amma ita tace gida zata tafi mommy ce ta karisa tace"yata menene? yawwa hajiya dan Allah kice su Maida ni gida wallahi umma na zata dake ni kuma na zubar mata da kudin kunun kuka tafashe dashi "to kiyi hakuri kinji ina ne gidan naku?"dabai sabon rami to yanzu kici abinci kiyi wanka ki sauya wasu kayan saina kaiki gida"to"Amrah zuba mata abincin,zuba mata tayi tuwon shinkafa da miyar egusi taji ganda da kifi da nama😋 mika mata tayi tace gashi sis dagowa tayi taga Amrah ta mata murmushi itama murmushin tayi ta ansa abinci tana ci a hankali mommy na shafa kanta tace"yata me sunan ki,tace"HAUWA ABDULLAHI amma anace min AYRAH"Masha Allah suna mai dadi, Amrah ce tace sis sunan ki dadi...
RAYUWAR AYRAH ✍️
Written by
Queen Bee 🐝❤️💜
Mrs Shitu 🥰❤️💜
Salmerty 💖💜
*Yar Lelen Nazari Writters Association ✍️🖊️*
*Nazari Writters Association✍️📘*
*Cikakken Nazari Kafin Rubutu Yana Damfare Da Bin Ka'idojin Rubutu ✍️🖊️*
*Nazari Kafin Rubutu Yana Kayata Duniyar Adabin Hausa 🌟✨*
*🖊️✍️Alkalami Yafi Takobi ⚔️
*GARGAD'I* wannan litttafi k'irkirarran labarine ban yishi dan wata ko waniba idan yayi kamanceceniya da rayuwar wata ko wani Arashi ne"aguji sauyashi ta kowace siga sbd hakk'in mallakata ne.
Dedicate to All my fans