Da Farko

9.2K 389 43
                                    

"Hajo! Hajo!! Hajara!!!"
Kira na uku ke nan ya ke ma ta, amma bai ji ta amsa ba.Ran sa ya kara baci, saboda ya san dalilin kyaliyar ta. Kuma ba yau ta fara saka shi gaba ba, kan son zuciyar ta. Karin ban haushi ma, ya san duk rintsi sai ta cimma burin ta. Amma ban da wannan karon, domin abin da ta nema ya fi karfin sa.
Kamar ya bi ta zuwa dakin ta amma sai ya hange ta ta na zuwa a hankali tamkar kwai ya fashe ma ta a ciki, ga fuskar ta a murtuke kamar ta kurbi kunu da zafi. Ta yi ma sa kallon isgilanci kafin ta kawar da fuska.
'Gani. Me ye ka ke kira ta?" Muryar ta cikin maqogoron ta, cike da tsaurin ido.
"Yanzu Hajo, duk kirar da na ke mi ki tun dazu bai ci a ce kin daga muryar ki kin amsa ba? Wato darajar tawa ba ta kai nan ba ke nan ko?"
Ta kalle shi a lalace, "Wannan kuma kai ka sani. Idan akwai abin da zaka fada min ne to ka fada, idan babu zan koma daki na, ba sai ka saka min ciwon kai ba."
Zuciyar sa ta kara tafasa amma ya daure, ya yi nuni da ledodin da ke ajiye kan wani teburin katako mai fadi. A wurin ya saba ajiye cefanen sa idan ya kawo gida, "Yanzu ke Hajo ban fada mi ki mu na da baki yau ba? Shi ne tun dazu na turo Sa'idu ya kawo cefanen abincin da za'a dafa mu su na rana, amma don tsabar wulakanci sai na zo yanzu na tarar ba ki taba su ba? Dubi yanzu karfe nawa? Karfe daya da rabi ne fa".
Hajo ta buga wani irin tsaki mai karar bata ran mai sauraro, ta ce,"Da ma na san labarin gizo baya wuce na koki. Aikin ke nan ci,ci,ci kamar gara. Ba abin da kuka sani sai cikin ku. To ban dafa ba don kuwa muddin ba a min abin da rai na ke so a gidan nan, to ni ma ba zan yi ma abin da ran ka ke so ba. A ka ce ma ka baiwa ce ni?"
Kokari ya ke, na ci gaba da danne zuciyar sa, "Hajara, ni ki ke gaya wa haka? Me ki ka nema na hakkin aure da ba na miki? Na rage ki da ci, sha ko sutura?"
Ta tabe baki ta ce,"Ai sai ka yi da Ali Garu. Ni din me ye ne ba na yi a gidan nan?"
Ya lura tsayuwar sa a wajen ba komai zai magance ba. Sannan matar sa ta hau tsini ba za ta saurare shi ba, "To shi ke nan. Ki ci gaba don Allah, kar ki fasa!" Ya yi ficewar sa.
Ta tafa hannayen ta, ta dora da gatsine, "Ai kuwa yanzu na fara, don kuwa ni da kai, shege ka fasa! Wallahi mu je zubawa mu gani, wa ya ki a jika- mai gishiri ko mai goro?"
Hajo na maganganun nan tuni keyar sa ta yi nisa. Ta sake kallon ledodin cefanen nan, ta kara tunzura, tare da kudurin ba za ta taba su ba balle ta bude su. Kai, ba za ta kara taba komai ba a gidan nan, muddin Sadiq bai kawo ma ta abin da ta bukaci ya kawo ba.
Don me ye ba zai kawo ba? Ai shi ya furta ma ta tun suna zance a gida, cewa idan ya aure ta, komai ta nema a wajen sa zai ba ta. Don yanzu ta bukaci abu, sai ya ce ba zai ba ta ba? To kuwa tabbas, zai hadu da takaici iri-iri, kwatankwacin wanda ya dora ma ta.
Ta koma daki ta iske Maimuna, kawar ta na tun asali, don tare suka tashi tun suna yara. Muna ta kalle ta sosai, "Yaya na ji ke da Sadiq din naki kuna hayaniya? Anya Hajo, ba ki girme wa hakan ba yanzu?"
Hajo ta harare ta tare buga tsaki, "Don Allah rabu da shi. Aikin banza! Ni za a yi wa wulakanci?"
Muna ta zauna da kyau,"Ai kuwa Sadiq ya na daraja ki Hajo. Na ga komai ki ke so ya na mi ki. Yanzu mene ne wulakanci a nan?"
Cikin tsaurin ido ta ce,"Ni kuwa ban san ya na yi ba, muddin bai saya min mota ba."
"Mota!?" Muna ta furta da karfi tare da dafe kirjin ta cikin mamaki.
Hajo ta harare ta,"To me ye? A kan ban kai a saya min ba ne?"
Muna ta yi 'yar dariya,"Aaah, kin kai man, mutuniyar. Wallahi kin cancanci abin da ya fi mota ma. Amma naga kamar kin dauko dala ba gammo ne. Sadiq ya na da halin da zai saya mi ki mota ne?"
"Ohon sa! Wannan kuma shi ya sani. Ni dai kawai abin da na sani, ya kawo min mota."

WUTAR KARA Where stories live. Discover now