Son Zuciya

7.2K 269 61
                                    

Muna ta ce, “To amma me zai hana ki bishi da lallami da tareraya har ya saya mi ki? Nifa kin ga haka nake yi wa Idris. Cikin ruwan sanyi na ke samun biyan bukata.”
“Idris daban ,Sadiq daban. Ke kin saba wa mijin ki da rarrashi, ni kuma na saba ma Sadiq da zafi. Don idan ba hakan na yi ba, ba na samun biyan bukata.”
In ban da kayan takaici, ba na shekaru na shida tare da Sadiq,’ ya’ yan su biyu, amma a ce yar motar nan dai da a ke yayin saya wa mata, ya ki saya mata?
“Wai kullum yara na su kare da mai mashin ne zai kaisu makaranta, ya dawo da su? Ni kaina idan zan je anguwa wai sai na jira shi ya dawo ya kai ni, ya koma ya dauke ni? Ni to gaskiya ya ishe ni.”
“Haka ne kawata.” Inji Muna. “Amma dai ki kara nazari dai, domin naga shi kan sa Sadiq, Vespa ya ke hawa. Amma ki ce ya saya miki mota, ai sai ya shiga bakin duniya. Ba cin fuska na ke mi ki ba, ke ma kin sani.”
“Ni ina ruwana, in dai zan samu biyan bukata ta ba shi ke nan ba? Yanzu bai ji dadi ba ma don ina neman rage ma sa wahala?”
Muna ta mike ta nufi bandaki da niyyar alwalar azahar, ta kalli kawar ta,“Shi ya ce da ke ya na wahala?”
Wannan karon Muna ta tako kulli. Cikin fushi Hajo ta mike ita ma, ta na hararar ta, “Ya fa ishe ki haka. Wai wa ki ke goyon baya ne? Ni, ko shi?”
“Zan goyi bayan ki ma na ko yaushe don bayan kawancen mu, ke mace ce ‘yar uwata, kuma dole zan so ki da karuwa.”
Hajo ta sake fuskarta,“Yauwa, yanzu na ji daidai. Amma a ce shekara ta shida,‘ya’yana biyu, amma ya na jan kafa wajen saya min mota? Ga waccan tambadediyar da ko babban kashi ma ba ta ajiye ba balle haihuwa, amma ki ga Tasi’u ya saya ma ta mota? Ba ta ma iya ba, amma har da nema ma ta mai koya matadon wahalar banza. Sai wani fadi ta ke yi, ta na rigima ta na kallon mutane cikin wani ji ji da kai.” Muryar Hajo na nuna takaici.
Ta ya ya ma za a ce yarinyar da ba ta dade da zuwa ba ta fi ta? “Ai in Allah Ya yarda ni ma sai na mallaki motar kai na.” Ta furta wa kan ta, fiye da wa Muna.
Muna ta girgiza kanta,“Ni ban ga abin da Bilkisu ta tare mi ki a cikin gidan nan ba da komai mijin ta ya ma ta sai ki ce  Sadiq sai ya miki. Tasi’u ya canja ma ta sarkar gwal ke ma ki ka sa Sadiq ya ba ki kudi ki ka canja ta ki, har ki ka sayi wata. Tasi’u ya dinka ma ta leshin dubu tamanin, ke ma ki ka ce sai an mi ki kaya ma su tsada. Ga shi yanzu ya saya ma ta mota, ke ma kin ce Sadiq ya saya mi ki. Kishi ki ke yi da ita?”
Hajara ba ta ba wa Muna amsa ba kan wadannan tambayoyi. Hakika komai za su kira shi, su kira, don kuwa ba zai yiwu ba ne a ce ta na matar yaya babba amma komai sai dai a gan shi wajen matar kanin mijin ta ba.Shin ita ba mace ba ce? Da me Bilkisu ta fi ta? Kyau ko asali?
Mutane ba za su gane ba, rayuwar yau nera ke ma ka komai. A yanzu yadda ta kasance matar yaya babu komai sai a raina ma ta wayo. Ga shi tun ba a yi nisa ba ma, kannen mazajen su idan sun ziyarce su, wajen Bilkisu su ka fi zama.Wani lokaci gaisuwar da suke ma ta ma sai ganin idon Sadiq. An mayar da ita saniyar ware. Don haka tilas ta kwato ‘yancin ta.
“Ba na ki shi da ita don kuwa ba ta kai na yi da ita ba wallahi. Amma ba za ki gane ba ne Muna. Hatta uwar mazajen mu fa ta fi son Bilkisu a kai na. Ni dai kawai uwar jikokin ta ce. Kin san cewa ko zuwa nan ta yi, aikawa ta ke yi a kai ma ta su Ilham da Farida ta gan su? Kamewa ta ke yi ta tare a gefen Bilkisu, ba ta ma fa lekowa sam!”
Muna ta ce,“To ai wannan bai kama ta ya dame ki ba, don wanda ya so jinin ka ai kai ya ke so.”
Hajo ta ja tsaki sannan ta fice daga dakin, ta furta “Ke dai yi alwalarki kawai.”
Madafi ta nufa, da niyyar dafa taliyar da za ta baiwa kawar ta, da su Ilham don sun kusan isowa gida. Ta san duniya ba za ta fahimci halinda take ciki ba, don babu wanda ya san yadda ta ke ji, sai ita. Sam babu. A ce ta na babba amma ita ce baya?
Kuma ma ai Hajo ce ta su, domin auren dangi a ka ma ta da Sadiq, Bilkisu kuma bare. Duk kowa ya daukaki bare a kan ta. Ba a son laifin ta don kawai mijin ta ya na da nera. An raina mu su don ba su da komai.
Ta sake jan tsaki tare da jin haushin Sadiq. Lusari kawai, wanda ya gagara tsinana komai wa rayuwar su. Tun da ya gaza, ita za ta zage ta fidda wa kanta kitse cikin wuta. Sai ta gwada musu! Bari su gani.
Ta bude durowar da ta saba ajiye ashanar da take kunna risho din ta ba ta gani ba. Babu ashana, dame za ta kunna? Ta kwalla kira ma ‘yar aikin ta Dije ta zo ta ba ta kudi ta sayo mata ashanar. Ita kuma ta tsaya ta na jira, ta na kokarin toshe hancin ta don kar ta ji kamshin girkin da ke fitowa daga bangaren Bilkisu. Ta san ba zai wuce ta na yin ferfesu ba ne ko wani girkin kwalama. Ita Sadiq ya tara ma ta masara da shinkafa, wai ta yi wa bakinsa girki. Mtsww ta sake jan tsaki. Zai ji jiki kuwa in dai ita ce.
Bayan wani lokaci Dije ta dawo amma ba ashana, don masu shagon sun rufe sun tafi yin sallar azahar. Kuma yawancin su bayan sallar, su kan koma gidajen su su ci abinci tukunna su sake budewa. Kamar al’adarsu ce hakan.
Haushi ya kara kamata. Ita kan ta yunwa ta ke ji, ga yara ‘yan makaranta za su iya shigowa a ko yaushe. Don ma wani lokacin sukan bi wajen kakar su ta ba su abinci. Allah Ya sa yau din ma can za su wuce.
Amma ya ya za ta yi da bakuwar ta Muna? Sai ko ta bar ta da yunwa, zuwa lokacin da za a sake bude shagunan, don kuwa ba za ta leka sashen Bilkisu don tambayar ashana ba. Kaskancin zai yi yawa. Ba za ta iya ba. Da wannan ta shiga dakin ta ta tarar Muna ta na sallah, sai ta koma falo.

WUTAR KARA Where stories live. Discover now