DUNIYA CE 1-50

3.2K 38 0
                                    


Please like comment and votes!!!

*1-5*
ĎUNIYA CE
*NA NANA DISO*
Tsawar da mumy tayi shiya rikirketa tunanin ta! "Ke Fatima ina tunanin dake nake magana, " a
tsorace ta sauka kasa babu inda ta nufa Sai bangarin Yaya Arif sallama tayi ya amsa, da kyar ta'iya
hada ido dashi.
Cikin gadara da isa yaja wane guntun tsaki sannan yace lafiya? " fatima tace hajiya ce tace k'ak'aine
asubuti!. " malama fita in nagama abunda nakeyi zan fito.
Tafiya takiyi babu laka ajikin ta "Shamsiya taje tana ke fatima kizo inje Alhaji Kuma kiyi sauri bawai
kina tafiya Sai kace wata mumina ba.
Tana shiga ta tsugunna domin gaida alhaji, " Bama Sai kin gaida ne ba nagaya miki kifito da miji
nagaje Nabaki Nan da sati daya wallahi in baki fito dashi ba Sai Na hadaki da duk Wanda nayi niyya!
" hawaye ne yafara Bata fusarta da cutar daki damunta zataji ko kuma da matsalar gidanan? " au
kuka kikeyi kema shirya kuka ba yanzu ba? Suka saka dariya har mumy ai kam kuka ma Sai an
hadata da D'an baba Mai gadi, tashi kibane waje banza sha-sha-sha.
Da sauri ta karasa dakin ta zuciyar na k'una chan kuma Kuka tafarayi oh ni fatima wai indai babu ran
iyayenka babu abunda Baza ayi maka ba, wayyo ne bansan so waye iyaye ba bansan dadin su ba?
Tun shekaran jiya nake fama da ciwon hakuri Amma kullum Sai ace naji gurin Mai chemist, Duniya
kenan!!!
Kiran da taje ya tabbatar mata da Yaya arif ne mayafi ta dakko da wayarta, tana isa Mota yace " kee
mike Damunki? " ciwon hakuri ne, " aikin kenan baki da wata cuta Sai hakuri aikin kenan Sai shigen
son zuwa asubuti Sai kace mayya ai ne da kinbarne nacire miki da gudu ma, " kuka takara fashewa
dashi, " han bareta yayi, " babu shiri tayi shiru ga azabar hakuri ga azabar duka sun kuyar da kanta
tayi har suka isa.
Dr ammar ne ya kalleta fatima Mai isa ba kizo asubuti da hure ba, ga azabar hakori haba fatima Sai
kace ba y'ar alhaji ba, " Da taga alamun zaiyi mata fada tace Dr ammar wallahi nafada akawoni
asubutin aka k'i Sai yanzu suka ga dama, " bakomai fatima komai Mai hucewa ne yanzu ban number
ki zan kiraki ko ciwon kai kikaje kiyimun flashing kinje? " to ya bata magunguna yariko hanun ta har
bakin kofar mota, " ya Arif ga ya ammar, " da kamata tsawa yayi shige mutafi Dan uwarki.....
Urs Nana diso *5-10* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Haba yaya arif menene na zage? " Nima kike tambaya mari ya
wanka Mata , " fatima ta rike fuskarta tace lallai mutum bashida tausayi duk wahalar danayi maka
Amma Har da kai atsanata? Mai natsare maka a rayuwa? Ku bakwa tsoron wannan duniyar?? "
Malama yimun shiru cewar arif Sai Dai muje tsoron ubanki ko uwarki, ke bari kije daga yau nadawo
da gyaran part dina in bahaka ba zakiyi bayani, " banza tayi masa inda ta cigaba da tunani. Suna i'sa
gida ta cewa mumy sun dawo ta huce dak'in ta akwatin ta tagani duk an hargetsa da alamun an taba
Mata kayanta, tasan bazai huce shamsiya ba, gyarawa tayi sannan tasha magani, sakkowa tayi ta
shinfida tabarma ta zauna tana karatu, Kamar daga sama taji an taka mata kafa, shamsiya ce tace
ke Fatima nasaka kayanki tunda ubana ne ya siya miki, " fatima tayi murmushi ai shamsiya ba yau
kika fara ba Dan kin saka kayana ai Mai sauke ne da baki dauke kin bayarba, " dallah munafuka
yimun shiru bari ma na tafi gurin mumyna uwata ta kaina," Hmm Allah muma yajikan namu iyayen, "
shamsiya tace oho dai ba'adasu, " fatima tayi murmushi ta cigaba da karatun ta. Yau tana karasa
girke d'akin ta ta nufa domin ta gaji, gashi Yau baa kunna inje ba, da taga alamun baza'a k'un na ba
wanka ta fada tana fitowa ta saka wasu kayan baccin ta. Arif Yana chan Yana waya da Ameera gashi
charging wayar sa saura kadan, " sweetheart rike wayar bari na anso wayan fatima, " wane irin
lamshashiyar murya tasaki nifa nifa banson kayi nesa dani my arif, " Haba ameera cool down yanzu
zankiraki fa, " to to inajeran ka karka dadi masoyi na. D'akin fatima ya buga Amma shiru, tsake yayi
ya budi kofar ko'ina duhu ga wayansa babu charge lalubar wayanta yafarayi akan gado, daga bisane
yaje hannun sa ajikin ta, wane irin shork yaji, fatima ce ta tashi wanene a dakina ko shamsiya ce, "
Sai muryar arif taji yace bani wayar ki, " bazan bayar ba, " ko kibane ko nadanneki na amsa, " Sai
kace Dan iska? " Yana kokarin riqe hannun ta ta hankada shi waje sauri tayi ta rufe kofar da key tana
huce sai kuma kuka wallahi yaya Arif kusani *DUNIYA CE*...... *ASALIN SU* _urs Nana diso_ *10-15* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Alhaji munzali yana daga cikin manyan 'yan kasuwa wanda
duniya tasan dasu, yana da mata guda daya hajiya sadiya shekarar su talatin basu taba haihu ba, su
biyu mahaifiyar su ta haifa daga shi Sai hajiya sumayya wacce itace mahaifiyar fatima, ita kadai ce
'yar ta mace Sai yayan fatima wato mudassir Yana Bangaren baban su Dan achan yake karatu,
mahaifiyar su Allah yayi mata rasuwa kusan shekara goma sha shida bayan mutuwar mijin ta da
shekaru itama tarasu daga baya sanadiyar ciwon zuciya. Alhaji munzali yana son ta sosai sanadiyar
son da yake yi mata, Bayan rasuwarta shine ya dauke Fatima Bayan fatima tana gidansa har yanzu
Allah Bai bashi haihuwa ba ya riketa tun tana yarinya, bayan shekara 4 Allah ya basa haihuwar
shamsiya Allah yabata tsewa ga mugun son ace tana da kyau, aduniya babu wanda ta tsana irin
fatima shiyasa kwata kwata bata sonta takan yi mata abunda takeso ga wulakanci da bori. Fatima
bashir kenan yarinya ce duguwa idanu wanta suna da haske ga manyan hips dukiyar fulani kuwa ba'a
magana, atakaice Dai yarinya ce mai kyau kuma yar lukuta tun tana yarinya Allah yabata kokari ga
hankali Amma kuma bata son hayaniya, ko yaya take Nan da Nan Sai ciwon kai, Tunda tafara
makaranta take samun ta daya, hakan yakan burge baba Amma kuma hajiya sadiya ta matsa mata
kullum sharri, Abun yana batawa fatima rai Amma babu yarda za tayi haka take hakura Wataran idan
hajiya. sadiya tayi mata sharri alhaji yakan harzuk'a ya zane fatima, Amma fatima bata taba jin
haushin sa ko kuma tayi masa Allah ya'isa ba, masu aik'in gida almajirai k'owa son ta yak'eyi saboda
nutsu-war ta da kokarin taga ta taimakawa talaka, hakan yasa tayi kokarin karantar mass com wanda
a yanzu tana level 4 ita kuma shamsiya tana bangaren english, fatima takan zauna tayi ta tunani
wane sa'in tayi tayin murmushi idan ta tuna burinta ya kusan cik'a. Arif D'an abokin alhaji munzali ne
mahaifin sa a canada yake azaune wanda kowa ya sane da alhaji bello cikakken Dan boko ne ga kudi
ga mulki, y'ay'an sa biyu a duniya daga Arif Sai affan, Sai mahaifiyar su hajiya rahama wacce suke
kira da mumy, Arif matashi ne da baifi shekara talatin da biyu ba fari ne Amma siriri ne baida kiba,
ga hanci Sai lip dinsa pink yanada fushi ga fada ga nuna isa baya kula yara a 'yan matan sa Sai
wacce ta gama uni, kullum cikin naiman aure yake Amma Har yanzu bai samu mata ba, ga son aure
da Allah ya jarrabe shi, yadade da gama karatun sa wanda yanzu haka yanada kamfanoni, abok'anan
sa suna yawon tsokanar sa da "ka kiyaye mai nema! Kullum in k'iyarsa kenan, idan Arif yayi
murmurshi hushiryar sa ta k'an bayyana yan mata sukan muto akansa, affan kuwa likita ne Amma shi
bashida girman kai sai surutu... *Cigaban labari* Tun lokacin da Arif yabar dak'in fatima yake tunani
domin Kasa bacci yayi,yanzu haka yana rungume da Filo tunanin ta kawai yakeyi har yaushe yarinyar
nan ta girma? Mik'ewa yayi ya tafi k'asa domin yin breakfast yana sauka ya tarar duk suna zaune
gaidasu yayi, " Arif yau ka makara ko sallah baka fito ba lafiya? " wallahi alhaji ban k'wanta da hure
ba shiyasa, " shamsiyya ce ta narke murya yaya arif " kallanta yayi Kamar ya marita yace lapia? "
turo bakinta tayi sannan tace ice cream nakeson sha da daddare zaka Kaine, " alhaji ne yace in bashi
da abunda zaiyi ai Sai ya kaiku, " fatima ce ta shigo da dankali ahannun ta ta zubawa Kowa shayi ta
mik'awa ya arif Nashi a hankali tace ina kwana? " jiyayi jikinsa ya mutu a hankali yace lpya
"shamsiyya da take hararar ta, " alhaji danAllah zanje gidan goggo ya mudassir yadawo, " shamsiya
tace dallah malama bakije nace ya arif zai fita dani ba sai dai ko gobe, " bakomai yau da goben duk
daya ne Allah yakaimu, " hajiya tace to munafuka uwar mata uwar iya magana, " ke fatima ya zancen
mijin kin fitar, " baba danAllah kabari nakarasa makaranta tunda saura wata 2 inshaa Allahu zan fito
dashi kafin lokacin, " na amince Amma kisane in baki fito dashi ba lokacin da kika saka wallahi da
kaina zan baki wanda nakeso? " tohm na amince, tashi tayi ta tafi sama. Tana fitowa daga wanka
wane material tasaka na gown ta dakko mayafe ta yafa wayarta ta dauka sai zumudin ganin yayanta
takeyi, sallama tayi hajiya na tafi " a wacce motar? " ta haya zan hau, " Dama ai itace kalarki, tana
fita taga yaya arif da shamsiyya zasu shiga mota ko kallon su batayi ba ta huce, " fatima arif yafara
kiranta, " banza tayi mai " zata fita kenan ya fun ciko ta nan da nan ta wad'a jikinsa.... *Urs Nana
diso* *15-20* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Lok'acin da Fatima ta wa d'a jik'in sa bai an k'ara ba ya
rungume ta sauri tayi ta ture shi tare da fad'in ya arif wai Mai nayi mak'a ne? So na k'eyi naje naga
d'an uwana Amma k'a tare ne, " shamsiyya da tayi sororo duk jikinta ya mutu ga bak'in cik'in ya arif
bai zage fati, da taga haka kawai Sai tace lallai fatima bak'ida da k'unya ya arif k'ik'e gayawa hak'a
jak'a mahaukaciya, " hawaye ne yafara wank'e fusk'arta cik'in k'uk'a tace ya arif k'ayi hak'uri in na
bata mak'a duk acik'in zumude ne, " shamsiyya tace 'kaji munafuka kai k'ace gaske ne hmm, " wata
razanan niyar tsawa wacce Sai da ta tsorata, kai ba itaba har ma shamsiyya Sai da ta k'oma cikin
mota, " har ina k'irank'i k'ina wane takama da i'sa banza kowanne bunsurun ne sai so'ki gwara alhaji
ya bak'i duk wanda yaga dama, " shamsiyya da murna ta isheta Sai cewa tayi ya Arif katawo mu tafi
tohm sis gani nan. Wane matsanan cin k'uk'a ta fashi da shi daga bisane ta futa, bata dadi da
tsayuwa ba ta tsayar da mota k'uk'a ta k'eyi acikin ta bai ban tausayi, " Mai motar daya gaji yace
hajiya sai dai kiye hakuri d'an nasan bazai huce rayuwar duniyar nan ba kowa hakuri yakeyi ko kuma
kiyita add'ua komai zai huce, " tohm nagode, yauwa ai kowa ya cuceki k'arki damu *duniya ce* shiru
tayi masa tana k'ana nan tunanin ta sai da suka k'arasa ta bashi kudin motar. Sallama tayi da murya
mai sanyi goggo ce tayi tsaki sannan tace oh fadimatu ke dai Allah ya wadaran ki sai da kikaje Dan
uwanki yazo sannan kika zo koh? " shiru fatima tayi nadan wane lokaci, ta matsa kusa da goggo tace
inayini? " tsaki taja sannan ta kalle mudassir tace ga bak'ar kanwarka nan in banda bin maza babu
abunda takeyi, " mik'ewa mudassir yayi Sannan ya shige dak'in sa batare da waiwayan goggo ba, "
hakan yasa fatima ta bishe jikinta duk ya mutu da kyar ta'iya sallama ta shigo, " dariya ya sakar
mata au babu murna nadawo? Rungume shi tayi sannan ta fashi da kuka, " au Har yanzu baki daina
kukan ba? Haba fatima kinsan bazan taba yadda da zancen su ba, Duniya ce k'i kyale su ta ishe
kowa, nema da Nadawo bata kyale niba Sai da ta cimun mutunci dan haka ki cigaba da hakuri, "
share hawayen ta tayi sannan tace to yaya, tafara bashi zancen auren, " karki damu Allah Yana tare
daki gobe zaki koma makaranta kinga jarabawar karshe kike dan haka ki dage kinje? Kuma wa kikeso
a samarin nake? " cikin kunya tace Dr ammar nakeso, " tohm Allah tabbatar da alheri, " haka suka
dinga hira Har sai da Arif yazo suka tafi tare. Tunda ta shiga mota takeyin waya da Dr ammar sai
murmushi takeyi, " Ya arif yace Wai mune ko wa zai k'washek'i ya k'washe asara, ki dinga adduar
barin jiki ya fishe da dariya, " kallon sa tayi maganar tai mata ciwo Amma tayi masa banza, kiran Dr
tayi tana wane Nan narka murya, batasan sun shigo gida ba, " Arif yace banza karya Mai bin maza
wayasan ma... *Urs Nana Diso* *20-25* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Arif yace banza karya Mai bin maza wayasan ma.. " baba Mai
gadi ne yace Arif yaushe ka kuma haka karka manta yarinyar nan marainiya ce, " Fatima ce tace
haba baba ba sai kayi magana ai Duniya ce! " tabbas 'yar nan kinyi magana Allah ya ganar dakai, "
arif wane mugun kallo yayi musu sannan ya kalle Fatima ki kaimun abinci inajeranki " to tace sannan
ta nufi kofar shiga gida, wanka tayi sannan ta nufi dak'in hajiya a k'an gado ta sameta, sannu da
hutawa mai za'a dafa ne? " tuwo zakiyi sannan kiyi lemo kishirya anjima zan aiki ki gidan zainab
k'anwata, to hajiya. Kitchen ta shiga tafara girke sai gurin karfe 4 tagama jirasu tayi a dinning, tafara
wanke wanke arif yashigo dak'in ta tana zaune tana ta waya ita da Dr ammar Sai dariya takiyi,
lokacin da arif ya shigo tunda ta kalleshi ta cigaba dayin wayarta. Hakan ya batawa arif rai baisan
lokacin da ya k'wace wayar ba yace wato bakida da tarbiya ko? Natsaya ina yimiki magana kina chan
kina waya da Yan iskan samarin ki, " haba ya Arif kafi kowa sanin wanene Dr ammar Kuma yanada
cikin wa yanda nakeso a rayuwa ta kuma wanda nake burin kasance wa tare dashi, kuma lokacin da
ka shigo ba kayimun magana ba, " tsake yayi sannan ya cillar da wayar ta wannan ce wayar da k'ike
waya da Dr ammar na fasa ta inda abunda zakiyi sai kiyi, " k'walla tafarayi sai tayi gurin wayar tana
kuka dubi yadda ka fasamun waya bakomai duniya ce, " banza kawai nafasa ko kinada wane gata ne,
" banida kowa sai Allah, " dallah tawo mutafi. Dak'in hajiya ta huce ta sanar da'ita ta gama aik'in ta
bata sak'on gidan anty zainab, " ga sak'on nan in kinje sauran k'ike yi mata girke daga nan kubiya
gidan usman matarsa zata bada ank'on ku, " tohm hajiya. Arif ta tarar a mota ya nata hira shida
amira awaya, abunda k'un nanta yajiye mata shiyasata zama amotar tare da k'allon ya arif, " amira
kinsan dai ina bukatar mace kullum mumy maganar ta yaushe zanyi aure, kullum azumi da shan
magunguna, " amira tace karka damu bikin nawa ai baife sati biyu ba kadaina damun kanka, ni ta
kace, " tohm sweetheart sai nadawo mayi waya, "okay " fatima ce tace gidan anty zainab zaka kaine,
lokacin da ya dago idon sa yayi jajir, " sauri tayi ta kau da k'anta, " fati I can't drive! Jiki na yayi
sanyi, " fatima cikin tsoro tace tohm cikin kankanin lokaci suka isa gidan ta, " arif sai kallon ta
yakeyi, suna isa gidan da saurin ta tafita, dan k'ota yayi tanata fizge hannunta, kokari yakeyi ya
rungumeta " kuk...... *Urs nana diso* *25-28* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Arif ne yak'e k'ok'arin rungume ta " k'uka ta sak'a tana
k'ok'arin tureshi sai ga sadik d'an gidan anty zainab ya fito, Arif ne yayi saurin sak'arta, " itama ta
gyara mayafin ta da ya wado, " a'a fatima sai yau ak'aga damar zuwa? " Arif yayi saurin cewa ai ne
na matsa mata ma da bazata zoba, " gaskiya ka k'yauta yaya arif, " murmushi tayi ta gaida sadik
suna hira suka shiga cikin gidan, " Fatima bari naji nadawo ana jirana a office Amma ak'wai maganar
daya k'amata muyi which is very important, " okay Sai kadawo, arif yana zaune yana jinsu a palour
sai sake sake yakeyi yadda fatima ta kida farin jini, " tashi tayi ta shiga dak'in anty zainab sai
sallama takeyi Amma shiru a hankali ta bud'e dak'in anty zainab ta gani a zaune tayi ta gumi, zama
fatima tayi ak'usa da'ita ta janye hannun sannan ta kalleta da manyan idanun' ta "yaushe kikazo
fatima, " hmm kikuwa anty zainab maik'e damun k'e? ana ganin fuskark'i anga damuwa a cikin ta
duniyar nan dole sai muna hakuri, " anty zainab ce takalle ta sannan tace fatima rayuwar gidan nan
tafara i'sata kullum Hakuri nakeyi Amma Abu yace tura, baban su sadik ne yak'e neman mata ga
kuma shaye shaye, " subhanallahi cewar fatima garin yaya anty zainab tuntune baiyiba sai yanzu, "
wallahi fatima nayi hakurin nayi fadan Amma har yanzu na rasa yadda zanyi kullum addu'a na k'eyi
amma shiru.. Haba anty zainab k'i cigaba da hak'uri k'owa da irin kaddarar sa Kuma ki cigaba da
addua komai zaizo karshe, k'i dage da sallar dare da yawan sadaka kinsan tana maganin masifa,
Kuma gaskiya kema ki gyara shi namiji dan lallama ne k'i dage da tsafta kwalliyar nan irin ta zamani,
yawan kunshi da gyara kanki, Kuma ki dinga tararrayar shi karkiga wai kin kwana biyu, wallahi ahaka
karuwai suke kwace muku mazaje gurin kwanciya dai kinsan komai banda abunda zance k'in fine
sani, " gaskiya fatima Allah miki albarka mijinki yaji dadi nutsuwar ki da hankalin k'i kullum suke k'ara
burgeni Sai naji Dama Sai k'uma tayi shiru.." fita sukayi palour arif yana zaune takaici duk ya i'she
shi, " anty zainab ce tace au tare da arif kukazo ai baki gayan ba, " arif cikin fushi yace ina zata gaya
miki ai burinta ya cika tunda kun shanya ni yadda tak'eson, " ki tashi mu tafi kafin na k'wade ki, "
anty zee bataji dadi ba tace ga dubu uku kyasaka kati, " angode Sai anjima.. Tunda suk'a dawo gida
hajiya k'e faman yi mata masifa wai ta dad'i, " hajiya kiyi hakuri danAllah banson rank'i yana baci
domin k'in zamar min kamar tamk'ar uwa, " hajiya tace ke dai da kinada kishiya ta shiga uku yarinya
karama sai kissa, " shamsiya tace hajiya gobe zamu fara exam need your prayers, " karkida mu
shamsiya za k'ice ai ke kuwa Fatima naga ta inda zakice tunda bakida mai yi miki addu'a, " kuka
fatima tasaka tana fita taga Dr ammar ajikin mota karasawa tayi ta gaidashi, " fatima kina lpya tun
jiya nakasa bacci saboda banji muryar kiba, ina wayarki? " kuka ta saka masa, " ai nasan hakan zai
faru ga wata nasiyo miki, " wane satin za'a kawo kudi, ina tayi miki addu'a zakice jarabawa kinje, "
dariya tayi wanda yakara k'awata fuskarta " wane dadi Dr ammar yaji azuciyar sa, " banda bak'in yi
maka godiya, fatana na kasance tare da k'ai yadda zan nuna maka k'auna, " wane irin ajiyar zuciya
yayi kice tawa Kuma kinake so, yanzu inada aiki zamuyi waya later Tohm bye yace bye darling....
D'uk an cik'a a palour din hajiya 'yan gidan su duk sun taro, fatima tana kitchen tana ta girke tana
gamawa ta k'ai musu daga mai harara sai mai habaice, babu wanda ta k'ula, dak'in ta ta huce wanka
tayi sannan tasaka wata gown tayi mata kyau, fitowa tayi a bene ta hadu da arif " ke ina abinci na? "
Yana kitchen, " jan hannun ta yayi har tsakiyar palour hajiya wannan 'yar ta k'e ta raina ne abinci ma
bata kawo mun, " abdul ne Yace woow perfect match gaskiya kyan ta ace matarka ce, " arif ne ya
kalleta daga Sama Har kasa, " Amma abdul ka cuceni Mai zanyi da 'yar iskar nan? " ai batada
masoyi, " hahaha suka saka dariyar kowa yace gaskiya kam, " Fatima batasan lokacin da tafara k'uka
ba, Allah kadai yasan miji na, Kuma karku manta ne ma mutum ce, " shamsiya tace kinsan dai ya arif
yafi karfin ki, " dariyar ta k'aice fatima tayi sannan ta nuna arif, " haha wannan tuzorun mai zanyi
dashi? " ai Kowa yanasan ya samu miji nagare amma ya arif na tsane shi ban sonshi, " wane wawan
mari ya sakar mata..... *Urs nana diso* *28-30* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Wane wawan mari Arif ya sakar mata, " rike fuskar ta tayi
sannan tace lallai ashi kaje zafin maganar da nagaya maka? Hmm d'uk'an k'an ku da k'uka dage
kuna yimun dariya, ya arif yafi karfina Kuma shi ba sa'a na bani ba, Kudi, dukiya, kyau, ilimi duk
yanada su! Ke da Ke da ke shamsiyya dukanin ku burin ku ku same miji kamarsa ko kuma ku
kasance tare dashi, " to let me tell you na tsaneshi natsane ya arif babu wane Abu da zanso atattara
da kai, " duk palour sunyi shiru, " barin palour din tayi Sai data hau Saman bene taji an hankado ta, "
firgeta tayi tayi saurin rike karfin gurin, " Arif ne ya kalle ta yadda kika gayan maganar Nan Sai kinyi
nadama, " tsake tayi tashige dak'inta. Hakan yakara batawa arif rai dak'in sa ya huce, duk lokacin da
ya tuna maganganun da fatima tagaya mai zuciyar sa hassala takeyi, wata muguwar dariya yayi
wacce ta k'awata fuskar shi wanka yayi ya shirya zuwa gidan su amira, Lokacin da ya'isa abban ta
yana waje yana hutawa, Arif ne ya tsugunna har kasa ya gaida shi, " cikin sakin fuska suka gaisa. sun
dad'i suna hira sannan ya shiga cikin gidan, " amira tana dak'i tana shiryawa ta saka wane yadi pink
tayi kyau sosai ta shiga dak'in ummi, ummi na kallon ta tace ke yarinya karki raga masa gurin ansar
kudi in da hali ma ki ce masa miliyoyi karki raga masa, domin da Dan kudin zamu karamiki kayan
dak'i, " tohm ummi karki damu indai arif ne zai bani. Tana shiga palour ya cika da kamshi ita kanta
sai da ta lumshi idanu wanta, " ayayin da arif ya daga k'ansa ya kalle amira gajeriya ce kuma bata da
kiba, Amma fara ce kal ga hanci sai dai idanun ta kanana ne, shekarar ta 21 tagama makaranta
Amma mahaifinta bayason cigaba da secondary ba yadda batayi akan yabarta ba Amma yace ko da
zata shekaru ahaka sai dai tayi Amma makaranta Sai bayan ransa, hakan yakan batawa itada
mahaifiyarta rai saboda, saboda duk wane plan nata ya warga zamata. Wane kallo tayi wa arif Wanda
ya harge tsa shi, murmushi yayi mata, bashiri ta matso kusa dashi, " my sweetheart ykke? " yadda
kike haka nema nake, " opps Har naji wane dadi kullum son k'a k'ara shiga zuciya ta yakeyi, haka
suka dinga soyayya ya bata katin dinner da na kamu, " Amma katin yayi kyau, " yanzu mai kike
bukata na biki gobe zanyi tafiya, " kamar 2million sun i'sheni, " hmm Amira komai fa nayi Miki hatta
turare nasiyo zan bada dubu d'are biyu, " Bata rai tayi haba arif gaskiya sunyi kadan, " mik'ewa yayi
in bakyaso Sai in mayar, " tsake tayi sannan ta ansa. Fita yayi straight gida ya huce, kowa Sai shirye
shirye suke, hajiya anatayi mata kunshi, " shamsiyya tana gwada kayan su, " arif yace yayi kyau
d'ink'in ko? " eh ya arif Amma gaskiya banso aka yimana tare da fatima ba, " anty zee tace ki dai kije
tsoron Allah sannan ta fizge kayan fatima, tana dawo wa ta shiga daki anty zee tagano, a'a saukar
yaushe, " safe, ya jarabawa Ana final year Allah yabada sa'a, " lpylou jarabawa babu dadi Allah dai ya
bamu sa'a, " Arif yace ai dama ita jarabawar bata dak'ik'ai bani ba, " shamsiyya tace kwarai kuwa, "
ko kallon su batayi ba, " hajiya ce tace ke bawai kina jarabawa ba ban dora abinci ba, " anty zee
cikin mamaki tace haba Yaya tun zuwa na yakamata kigayan da tuni nagama, Amma fatima ta gaji,
bari naje na dora, " aa ba sai kinje ba anty zee kibarshi ne zan dora, " kitchen din ta huce taji ta
dora. Ke fatima ke fatima dallah malama ba kirank'i nak'eyi ba, " Wai shamsiyya ya kikeso nayi
karatu fa nakeyi, " kayan ta k'waso ta watsawa fatima to jaka gashinan na ankon ya Arif ne, " hmm
wai shamsiyya mai nayi Miki? " Arif Yana kallon su jira yakeyi yaji mai fatima zatace, " ubanki kikaye
mun banza jaka kayan bikine ko bakyaso? " haha ai basai nafada ba Mai zance nayi abikin ya Arif
banda lokacin zuwa cux natsane Naga fuskarshi, " zuciyar arif ki bugawa ya rasa mai zaiyiwa fatima
gaba daya kwarfota yayi bata ankara ba ta wadi tim... *Urs nana diso* *30-33* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Sa na d'iyar fad'uwar da fatima tayi hak'an yasa bak'in ta ya
fashi sai jini! Nan da nan hankalin arif ya tashi ya matso Yana kokarin rike hannun ta ta fisge, cikin
kuka tace karabu dani, " bai san lokacin da yaja hannunta sai bandaki ba, cikin k'ink'ina yake magana
sannu fatima kuskure ne, ya wanke mata bakin, " kallon sa takeyi cikin tsana da kyamar sa, ahankali
ta fizge hannun ta tayi hanyar waje, sannan tace da kasan yadda natsane ka wallahi bak'aso k'allon
fuska ta ba, juyawa tayi hips dinta suka wane kad'a " arif ne ya rike k'ansa ciki da takaice, fatima
wallahi sai kinso ne ko ki naso ko ba kyaso.. Sama ya hau ya d'akko jak'arsa sallama sukayi da
alhaji, sannan ya shiga part din hajiya tana zaune tana waya katse wayar tayi da taji ya shigo, " ango
tafiyar ce? " eh hajiya jibe da huri zan dawo, " tohm akwai wasu kaya aleda adak'in fatima ka dauka
katafarwa da mumynk'a, " tohm hajiya ina shamsiyya tazo ta rakani airport, " kiranta hajiya tayi tace
bari ta shirya, " shi kuwa arif dak'in fatima ya zarce ko kallon sa batayi ba karatu takeyi, sak'on ya
dauka, " shamsiyya ta shigo ta dauki mayafin fatima cikin gadara tace ke na dau mayafin ki, " Fatima
ko kallon ta batayi ba, " arif ne yayi dariya sannan yace idiot sai girman k'an tsiya ni kuwa zanga mai
aurenki, " shamsiyya ce tace ai ya arif sai talaka irinta shi zai iya auren ta, kuma ai mai uba shi zaiyi
alfahari, " arif yaja hannun shamsiyya, " Fatima cikin kuka tace kafin a dau abun mutum ake
tambayar sa ba bayan an d'auka ba, " shamsiyya cikin masifa tace ubanki ne yasiya miki, ko kuwa
uwarki? " fatima tace a a alhajin kine ya siyamun, " arif ya jata suka tafi, "wane sabon kuka tafashi
dashi ahaka Har bacci ya dauke ta... Lokacin da ta farka karfe hudu, wanka tayi ta saka kayanta ta
sauka kasa, tabarma ta shinfida sannan ta fara karatun ta, kamar daga sama taji muryar maryam,
daga k'an da zatayi taga maryam ba yadda ta saba ganin taba, " fatima ce ta janyo ta maryam lafiya
mai yafaru? " kuka ta sakar mata sannan tace fatima danAllah mai nayiwa baffa ya tsaneni? Fatima
kinfi kowa sanin banda samari amma idan a kazo gurina baffa sai yakore su, ya kai ya kawo ko girke
nagama sai anty atine tace na sace nama, ga auwal ya takura mun sona yakeyi? Komai zan taba
agidan nan sai an mun sharri yanzu ma zaneni sukayi wai na sace sabulo, walhi ne zan gudu.."
dak'ata maryam *Duniya ce tafi bagaruwa iya jima* ki godewa Allah wallahi dama ya jarrabi ke,
komai komai mai huce wa ne, kanin mahaufin ki ne kiyi hakuri Dan Allah wataran sai labari, " ke
fatima nifa dadi na dake bawa mutum hakuri, " mtsew kinga maryam rashin hakuri baya haifa komai,
koma guduwar da kike anbata an gayamiki abune mai kyau? Wallahi kiyiwa kanki fada kikama
maraicin ki, kuma kidage da addu'a duniyar ce dole sai da hakuri, " tabbas fatima zan cigaba dayi
nagode, bari na tafi Kar nayi laifi, " tohm ki gaida gida, " zaije sai munyi waya... *Urs nana diso* *33-35* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Tana i'sa gida gate din da zata bud'e taji tayi k'aro da ya arif,
wane irin k'allo yayi mata sanadiyar haka ta sun k'uyar da k'anta, Chan k'uma ta tureshi, huce war da
zatayi arif ya rik'o ta, " menene haka ya arif ka sakeni nagaji Ina bukatar hutawa, " hutu ai sai d'an
gata kije dak'ina ki gyara mun k'uma akwai kayan da mumy ta bak'i, " nagode mata, " what about
me??? " ai Ana godiya ga Masoyi ne ba mak'iye ba so ka daina shiga rayuwa ta, " arif ne yagyara
tsayuwar sa common inajinki mai kikace?? Kin tsaneni? " ohhh how many times zangaya maka? Na
tsaneka, " Arif baison lokacin da ya matse mata wuya ba, i'don sa duk yayi ja, kika Kara cewa kin
tsane ni sai na karya k'i ya hanka d'ata ta wadi, " wayyo Allah na wallahi bazan daina gaya maka na
tsaneka ba wane kuka ta saka... Shirye shiryen bikin *Arif* ake tayi, fatima ko ajikin ta, ita jarabawar
ta ce a gaban ta, yau tana skul last paper zasuyi, friends dinsu suna ta amma sai dai tayi murmushi
bata kula kowa Hakan yasa Yan class sai tsiya suke mata, gurin 2 suka gama jarabawa suna fitowa
ta huce k'asuwa siyayya tayi, a hanya ta hadu da hamid abokin ya arif tsayawa yayi, " kanwar mu
ykke? " oo ya hamid kana lpya yagida, " duk lou k'asuwa kikazo ne? " eh , " dama gidan naku zani
tawo mu tafi, " bude gidan baya tayi taga alamun mutum agaba amma bata ga fuskar sa ba, " fatima
kunata shirye shiryen biki kenan, " suna dai tayi, " fati kenan ai nina zata dak'e za'ayi, " ne walhi
kafara batamun rai mai zanyi da ya arif ne natsane shi ma, " arif ne yace kema mai zanyi dak'e dan
uwarki? " ya hamid sauke ni na karasa, " arif yace kina fita zan karya ke, " hmm Wai shi mutum baka
damu da shiba amma ya takura maka, " hamid ne yayi dariya wallahi kuyi a hankali, " suna i'sa gida
taga Dr ammar murna agurin fatima kamar ta Rungume shi, " Dr na mai yafaru naga fuskar ka haka?
" wallahi ina sonki Kuma ina kaunar ki, zan tafi ba don son rai na ba, " hawaye ne ya wanke fuskarta
cikin shash shek'a mai kak'e nufi dr, " fatima zan tafi karo course a Germany, "tohm Allah ya kiyaye
amma duk abunda kadawo ka tarar karkaga laifi na, " arif da hamid sun sak'e baki suna kallon su, "
juyawa fatima zatayi Dr ammar ya riko ta, " cikin k'uka ta rungumesa, " zan dawo fati kidaina kuka, "
na daina na daina, cikin gida ta ruga aguje, " motarsa ya koma ya fita daga gidan, " lallai Arif fatima
tayi ashe Dr takeso, " kai malam sai fa ta sone ko ta naso ko bataso, " hahaha lallai kana da aiki..
Sama ta hau kuka takeyi ma cike da tausayi, ka tafi kabarne Dr in sonka ina zan kai sonka, zan jira
ka ko da kuwa za'ayi shekaru, " Arif ne yasa dariya sannan ya zauna kusa da ita hannun ta ya rik'e, "
malam banson iskance kadaina rike ne Wannan ai, " ke dakata zanyi maganin ki zaki zama tawa zan
kuma tabaki Sai yadda nayi da k'e, " in ka i'sa na kasa nafara son ka, " zakiyi zakiyi fita yayi yabar
dak'in wanka tayi tafara sallolin ta cike da kai k'ukan ta gurin Allah .. K'owa ya k'alli fatima yasan ta
rame, duk ta canza ta koma shiru shiru, aikinta takeyi kafin ma ayi mata zancen, yau ranar jumma'a
gida ya cika da mutane ga wani ciwon ciki da ke damunta, karfe biyar zaa tafi, janan gurin kamu, "
shamsiyya ce ta wanka wa fatima mari k'owa na gurin sai da ya jiyo, " me nayi miki zaki mari ne? "
ke yar iska tun dazu ina jiran ki bak'i dura abinci ba... ikon Allah yanzu Akan abinci kika mari ne? "
eh akansa Kuma kika kara magana kije saukar wane banza wacce bata iya komai ba, " ke shamsiyya
dakata ke bansan irinki Ba babu abunda kika iya sai tsanar mutane, babu abunda kika iya tunda nake
agidan Nan bantaba ganin kinyi girke ba, ke bakisan kowanne namiji burin sa macen data iya girke
wacce ta kida ilimi yar kwalliya mai hankali, hmm babu abunda kikasa agaba sai cin mutuncin
mutane, " wani wawan mari hajiya ta sakar mata yar iska mai bin maza ke maga mai aurar ki, "
fatima murmushi tayi tace *Duniya ce* kuyi mun duk abunda kukeso tayi tafiyar ta, " nan fa kowa
yafara maganar shamsiyya, " Arif yana can ya kasa zama burin sa gobe tayi ya kasance tare da
matarsa, wane mugun feeling ki damun sa, Amira ya kira awaya sai kuka tak'eyi masa nan hankalin
sa yakara tashi, " Amira please aina zamu hadu, " dariya ta saka kai da gani na sai an daura, " please
ki taimaka min " sorry dear ta kashi wayar, " sallah ya tashi yayi.... *Urs nana diso* *35-38* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Tun k'arfe biyar moto ce suka cik'a a k'ofar gida kowa Sai
shirya shirye yakeyi, shamsiyya ta saka wane material purple anyi mata wasu matsatsun d'in ki, sai
iyaye takeyi hajiya ce ta shigo dak'in ta, " kai shamsiyya irin wannan kyau haka, " hajiya ai dole na
dau wanka kinsan aboka nan ya Arif sun hadu, " gaskiya Kam ne munyi gaba sai kin tawo, " jabir ta
kirawo awaya cikin yace mata yazo, sakk'owa tayi daga Sama taga su mumy duk sunzo, " mumy tace
ina yar uwartaki, " mumy sauri nakeyi bansan inda ta shiga, Sauri tayi tafita a gate ta hadu da
rufaida, " yayi yar iska kinyi kyau sosai batsalar ba hips ba gaba, " dallah yimun shiru bakin ciki
kikemun, ta shige mota, " Allah sawake Miki, cikin gida ta shiga duk an tafi babu kowa dak'in fatima
ta shiga ganin ta tayi akwance, ke Fatima mayi haka mutane kowa yana tambayar ki, mai isa bake
shirya ba? " ke rufaida kyaleni wayannan mutane ai basu da kirki naji nayi musu me? " lallai fatima
dole suce bakin ciki kike musu, malama kitashi ki shirya danAllah sai mutafi tare GA uncle chan a
mota yana jira na, " fatima cikin Sauri ta shiga wanka, tana fitowa turare ta fesa sannan ta dakko
wane less din ta, " rufaida ce tace woow wannan lesin ya hadu Anya bazaki fi Amaryar kyau ba, "
fatima tace wallahi kika kara damuna zan fasa Kaya ta saka, " wayyo Rufaida kiba nakeyi, haha
hajiyar hips da.." dallah yimun shiru zokiyi mun kwalliya cikin lokaci kankani fatima tayi kyau sosai
head ta dora orange sai sarka da takalmi, " wane mayafi ta d'akk'o zata yafa, " haba fatima danAllah
karki yafa please, " yaza'ayi na fita haka god'e god'e.." malama kibawa makiya kunya, " hmm muje
to, wata hadaddiyar mota suka shiga, " ai bangani kiba nazata amaryarce, " kai uncle inayini? " Lou,
Amma kinyi kyau, " nagode uncle... Arif Da Amira sunyi kyau shigar blue and white su k'ayi, amarya
sai iyaye take tayi masa, a mota sun kusa karasawa tace " Arif baka bani kudin leki ba, " kallon ta
yayi jiya ba nabaki kudin leki ba? " na rabawa kawaye na, " hamid ne yace to ga 20k kiyi lek'in, " ko
godiya batayi ba ta ansa suna isa kofar janan event aka bude musu gate, " masu hotona sai faman yi
sukeyi, " Kowa ya kalle Arif sai yakara saboda k'yan da yayi, " Amira sai shishige masa Takeyi, kowa
sai hotona akeyi musu suna shiga hall suka zauna a kujera, masu kida sai yi sukeyi, " su shamsiyya
kuwa sun dadi a filin rawa gani take tafi kowa kyau, hajiya kuwa murna ta isheta 'yarta tayi kyau,
sunaye aka fara ambata wanda zasu zauna a dinning.... Kowa sai kiran sunan ta akeyi da saurayin ta,
ankira sunan fatima shiru cikin mintuna fatima suka fito daga mota, gaba ta danyi, " uncle yayi saurin
jawo rufaida tace naam wallahi ina son fatima tana da wanda takeso, " to zan gwada sa'a ta " tohm,
" sai da zata shiga Hall taga basu karaso ba, baya tayi uncle katawo mutafi, " tohm kanwata, ajeri
suka shiga, kowa kallonta, karasawa tayi gurin momy ta gaida ta, " ai Har raina ya bace, " gaba daya
hankalin Arif Yana kanta, " hakan yasa Amira tace waccan wacece yace tawace, " cikin gyatse nan
fuska tace oh itace wacce ka tsane ta ashe, " yayi dariya, " masu kida suka fara yawon fatima yar
masu kyau 'yar asalin kyau uwa ilimi ga wajen zamanki, sai ku tawo tare da mijinki, " uncle ne ya
rike hannunta suka tafi gurin zamansu sai leke yake mata, " taji dadin hakan da yayi mata sai kallon
sa takeyi, rada mata yayi a kunne nayi kuskure but ayimun afuwa, " kashe masa ido tayi bakomai, "
cikin mintuna kuma fuskarta ta canja, Bakowa take tuna waba daya huce Dr ammar, " momy ce ta
katse Mata tunanin ta..... Fatima kitawo muje kiyi rawa, bikin d'ana guda, " ne ne momy ki kyaleni
bazan iya ta shiba, " oh fatima nah sokike aji kanmu? " uncle ne yace tashi mana kitafi, " to tace
suna shiga filin, " shamsiyya da hajiyar ta kamar su mutu dan bakin ciki, bama e kayan jikin fatima
yadda take daukar hankalin mutane, " l'eke taketa yiwa amarya, Masu kida Sai washe ta sukeyi, " Arif
ne yajata gefe kamar zai Bata kudi, " Wai maye haka ya arif, " idiot ina mayafin ki ahaka kikazo kowa
sai kallon ki yakeyi, " tsake tayi tashiga filin tafara rawa, " Arif hankalin sa yakara tashi.." fatima ce
tafito domin tagaji da rawa, " Arif yayiwa ameera karya ya biyo fatima hannun ta yaja ya jefa ta a
mota, wane irin gudu yakeyi Har Sai da ya'isa gida dakin ta yakaita wasu mari ya sakar mata, kuka
tafara yi, " iskancin nake Har yakai kidinga shigar nan kalle ki? Wallahi kika kara fita haka saina
ballaki idiot Mara kamun kai wawiya, " wayyoo Dr ammar Wallahi ina sonka, " Arif cikin fushi yace za
kuma kirabu dashi ba, " Mota ya koma baa tashi daga dinner ba sai 10, " fatima tunda tayi wanka
tafada gado sai bacci..... Yau lahadi aka daura auren *Arif bello*da *juwaira (amira)* Akan sadaki
dubu dari, " Kowa murna yakeyi aka zarce gidan amarya akasha hotona, " su shamsiyya bakin ciki ya
i'sheta kullum gaba fatima takeyi amma ita tana baya, " affan sun shigo tare da ango Sai hotona
sukeyi " shamsiyya ina fatima, " tana daki, aguje ya shiga kanwata kina ina? " akujera ya sameta da
wata gown Jan hannunta kawai yayi ya affan bari nadau mayafi, " cikin zumudi ya kaita cikin Yan
hoto, " jiyowar da Arif yayi yaganta take ya daka mata tsawa, " affan yace mayi haka Arif, " tabar
gurin nan, " fatima cikin bakin ciki tabar tsakar gida kuka takeyi mai tsanane ahaka ya muddassir ya
kirawo ta mayafi tasaka ta sakko, " gaisawa sukayi suka sha hira da Dan uwanta........ Karfe bakwai
aka kai amarya gida yayi kyau haka akayi siyan baki aka barta ita kadai, " Amira murna agurin ta
ba'a cewa komai gida 3 part ga motoce, wanka tayi sannan ta saka kayan bacci ta kwanta, " Arif ne
yashigo yace tatashi suyi sallah, sukayi yayi addu'a suka kwanta, " han da nan hankalin Arif ya tashi
shafata yakeyi ko ta'ina kayanta yafar........ *Urs nana diso*

DUNIYA CEWhere stories live. Discover now