“Ke corper shun, in babu busa ba daga hannu ne?”
Fatima ta dan yi dariya, “Haba A’is sau nawa ina neman wayar ki amma ba na samu?”
A’isha ‘yar uwarta ce da suka hada uba daya, wacce kan su kusan daya, kuma tare suka tashi. Su ne na takwas da na tara a cikin jerin ‘ya’yan mahaifin su goma sha biyar da ke raye a duniya. Duk fadin duniya, babu wacce ta fahimci Fatima kamar A’isha.
“Ku ji min sharri.”
“Babu sharri ko daya. Ko jiya da dare ma na kira ki. Saura kiris na kira na mai sunan Baba, amma dai sai na kyale kawai tun da kin mana tsada.”
“To wai ki kira wayar sa bisa wane dalili?” Ta na iya jin sautin bacin rai a muryar A’isha.
Fatima ta dan yi dariya, “Oh ni! Har yanzu dai ba ki huce ba ke nan.”
“Mtsww. Ke don Allah mance da wannan. Ya ya labarin Gomben ne?”
“Kamar yadda kika sani ne tuntuni, na ba ki labarin an ba ni koyar da ajin ‘yan satifiket. Koyarwar bai kasance da matsala kamar yadda na yi zaton zai yi ba tun kafin na fara….”
Ranar farko ta yi taraddadi a lokacin da yara suka zuba mata idanu, suna sauraron kowacce kalmar da za ta fitar daga bakin ta. Ta dan yi shiru na dakika biyu ne kacal ta fahimci cewar muddin ba ita ce ta yi maganar ba, to lallai sai dai a yi ta kallon-kallon juna kawai, ba za a wuce gaba ba.
Don haka, ta fara da gabatar da kan ta, sunan ta, da kuma darasin da za ta koyar da su. Daga nan ne kuma komai ya zo ma ta cikin sauki. Sai ga ta bayan kamar minti talatin a cikin ajin, ta shiga kwalala kamar wata kwararriya.
“…Sannan yanayin garin akwai zafi. Amma fa akwai tsafta da kyau.” Ta karasa. Ta san sarai A’isha ta danna ma ta harara ta waya a lokacin.
“Ke dalla wa ke ta yanayin gari? Ya ya labarin hadaddun samarin Fulani? Na san ku na haduwa da kyawawa, irin handsome hunks din nan.”
Fatima ta yi murmushi, labarin gizo baya wuce na koki. “Me ya faru? Za ki canja Isan ne?”
Fatima ta san A’isha ta juya idanun ta ne a daya bangaren, “Duk yadda nake son yin hakan, ba zai yiwu ba. Don wannan matsolon ya manne min kamar cingam.”
Fatima ta dan gwale idanu sannan cikin dariya, ta ce, “A’uzu billah! Allah Ya shirye ki. Mijin ki ne fa A’is.”
Sanin kowa ne A’isha ta sha mitar a kan rashin dacewar su da juna. A tun haduwar su da juna ya ke mutuwar son ta, ya kuma makale har sai da ya aure ta kowa ya huta.
A bana shekaru uku ke nan da auren su kuma diyar su guda, Rahama, amma ba a taba jin kan na su ba. Jama’a da dama su na mamakin hakan. Domin kuwa ita ce macen da a ke tunanin ba za ta iya taba zaman aure ba.
A’isha Isa mace ce mai saurin fushi ga kuma zuciyar tsiya sai ka ce wata kuturu. Tun kafin zuwan Fatima Gombe ta dan samu sabani da mijin na ta.
Ba wani abu ba ne, kawai tambayar sa kudi ta yi ya kuma yi alkawarin ba ta. Amma ko da lokacin bayarwar ya yi kuma ta ke bukata, sai ya hana ta, ya dauka ya ba wa kanwar sa a bisa umarnin mahaifiyar sa, wacce suke kira da Yayya.
Kwatankwacin yadda Isa ke son A’isha, hakan Yayya ta tsane ta, ko ma fiye. Ganin kishiya ta ke ma ta, don haka komai ya yi wa matar ta sa, sai ta saka ya ma ta ko kuma ‘ya’yan ta mata da ke dakunan mazajen su.
A ganin Fatima, Yayya ba ta tausayin dan na ta ko kadan. Domin ko da a ce bangaren sa babu abinci, kasancewar su gida daya suke, to kuwa ba zata taba tallafa ma sa ba ko da da kudin sayen maggi ba ne.
